Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 22 ga watan Yunin 2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • Sadis Buba

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf da Haruna Kakangi

  1. Sojojin Myanmar sun kashe fararen hula 700 cikin wata shida, in ji MDD

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Myanmar ne ke da alhakin kashe fararen hula fiye da 700 a cikin wata shidan da ke kewaye da lokacin zaben shekarar da ta gabata, in ji MDD.

    Wani sabon rahoto da aka haɗa daga watan Agusta zuwa Janairu ya ce sahihan majiyoyi sun tabbatar da kashe aƙalla mutum 702 da suka haɗa da mata 224 da ƙananan yara 153.

    Ya shafi watanni shida ne daga lokacin da sojoji - waɗanda suka yi juyin mulki shekara biyar da suka wuce - suka sanar da gudanar zabuka, tsarin da ake yi wa kallon na jeka na yi ka ne saboda an cire manyan jam'iyyun adawa.

    Rahoton ya yi gargaɗin "raguwar tallafin ƙasa da ƙasa na kara wahalhalun da miliyoyin mutane ke fuskanta".

    Sojojin Myanmar sun ƙaddamar da juyin mulkin ne a shekarar 2021, wanda ya haifar da yaƙin basasa inda aka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

    Manyan yankunan ƙasar na ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon ƙungiyoyin ƴan adawa masu ɗauke da makamai.

  2. Ya kamata gwamnatin Najeriya ta rage farashin man fetur - Sheikh Qaribullah

    Sheikh Qaribullah Nasir Kabara

    Asalin hoton, Sheikh Qaribullah Nasir Kabara/FB

    Shugaban ɗarikar Ƙadiriyya na Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta duba yiwuwar rage farashin man fetur domin sauƙaƙa wa al'umma matsin rayuwar da suke fuskanta.

    Shehin Malamin ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa, Sheikh Abdulgaffar Nasiru Kabara, wanda ya wakilce shi a taron Qadiriyya Media Connect da aka gudanar a birnin Kano.

    Ya ce akwai buƙatar gwamnati da masu ruwa da tsaki su yi la'akari da sauƙin da aka samu a kasuwar mai ta duniya bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka.

    "Akwai buƙatar hukumomi su yi la'akari da sauƙin da aka samu a kasuwar mai ta duniya bayan ci gaban da aka samu na yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka, wanda ya taimaka wajen rage fargabar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma saukar farashin mai a kasuwannin duniya," in ji shi.

    Taron Qadiriyya Media Connect wani taro ne da matasa mabiya ɗarikar Ƙadiriyya ke shirya wa a duk shekara, inda mabiya ɗarikar daga sassa daban-daban na Najeriya ke haɗuwa domin tattauna batutuwan ilimi, sada zumunci da sauran al'amuran rayuwa.

  3. Mutum 13 sun mutu a fashewar gas a Qatar

    AFPTV video footage frame of an explosion at Qatar's Ras Laffan industrial zone

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 13 ne suka mutu yayin da 66 suka jikkata sakamakon fashewar gas a babbar cibiyar sarrafa iskar gas ta Qatar.

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta ce wani fashwar ta ya faru ne a yankin Ras Laffan a daren Lahadi.

    Ministan makamashi na Qatar, Saad Sherida Al-Kaabi, ya ce fashewar ba za ta shafi fitar da iskar gas da ƙasar ke yi zuwa ƙasashen duniya ba.

    Ya ƙara da cewa, "wannan haɗari ne kawai, ba sakaci ba ne ko zagon ƙasa daga wani ɓangare."

    Tashar jiragen ruwa ta Ras Laffan ita ce tashar ruwa ta wucin gadi mafi girma a duniya, kuma tana ɗauke da cibiyar fitar da iskar gas mai ruwa mafi girma a duniya.

    A farkon wannan shekara, yankin ya fuskanci hare-haren Iran.

    Ministan makamashin ya ce gwamnati na ci gaba da binciken musabbabin fashewar da ta faru a cibiyar samar da iskar gas ta Barzan, inda ya ce babu wata barazana ga muhalli sakamakon lamarin.

    Sai dai ya ce a halin yanzu yana da wuya a tantance lokacin da za a ci gaba da gudanar da ayyuka a cibiyar.

  4. Matsalar tsaro ce ke gurgunta tattalin arzikin Najeriya - Kalu

    Kalu

    Asalin hoton, Sokoto govt

    Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya ce matsalolin tsaro da ake fama da su a sassan Najeriya na hana ƙasar cimma burinta na gina tattalin arziki mai ƙarfi wanda zai inganta rayuwar al'umma.

    Ya ce sai an ba fannin tsaro muhimmancin da ya kamata idan ana son samun ingantaccen tattalin arziki a Najeriya.

    "Kasar nan tana buƙatar bunƙasa tattalin arziki domin a samu kuɗi, wadata da kyakkyawar rayuwa ga ƴan Najeriya. Wannan shi ne abin da ƙasar ke buƙata," kamar yadda Kalu ya faɗa a wajen taron ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar Sokoto.

    Tsohon gwamnan ya buƙaci a ɗauki tsauraran matakai domin magance matsalolin tsaro, ida ya ce hakan zai taimaka wajen samar da ci gaba sosai a fannin tattalin arziki.

  5. Za mu ci gaba da zama a Lebanon har sai abin da hali ya yi - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce har yanzu bai sauya matsayarsa kan ci gaba da kasancewar sojojin ƙasarsa a kudancin Lebanon ba,

    Ya mai jaddada cewa za su ci gaba da zama a yankin "har sai abin da hali ya yi.".

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Netanyahu ya ce umarnin da ya bai wa ministan tsaron ƙasar ma bai canza ba.

    Ya ce, "Sojojinmu da ke kudancin Lebanon suna da cikakkiyar damar ɗaukar matakin kawar da duk wata barazana kai tsaye da za ta iya tunkarar mazauna arewacin Isra'ila."

    Firaministan ya ƙara da cewa sojojin Isra'ila ba su da wani shamaki a yankin, kuma za su ci gaba da kasancewa a yankin har sai lokacin da gwamnati ta ga ya dace su janye.

    Kalaman nasa na zuwa ne yayin da batun tsagaita wuta a Lebanon ya zama ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da suka mamaye tattaunawar da aka yi tsakanin Iran da Amurka a Switzerland.

  6. Vance ya ce Iran za ta bar masu binciken nukiliya su koma cikin ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ce Iran ta amince da barin masu binciken nukiliyar su koma cikin ƙasar - wata muhimmiyar buƙatar ƙasashen duniya - a inda za a fara tattaunawa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA .

    Vance ya ce an samu muhimmin ci gaba bayan zagayen farko na tattaunawa tsakanin Amurka da Iran domin cimma matsaya ta ƙarshe don kawo ƙarshen yaƙin.

    Ya ce tawagogin sun tattauna batun sake buɗe mashigar ruwan Hormuz.

    Yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da aka rattabawa hannu a makon da ya gabata ta haɗa da ƙudurin sake buɗe mashigar da kuma kawo ƙarshen faɗan da ake yi a dukkan fagagen daga - ciki har da Lebanon.

    A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar a ranar Litinin, masu shiga tsakani na Qatar da Pakistan sun ce bayan zagayen farko na tattaunawar, Amurka da Iran sun amince da "taswirar hanyar cimma yarjejeniyar ƙarshe cikin kwanaki 60".

  7. An amince da tsagaita wuta a Labanon, bayan hare-haren Isra'ila sun girgiza yarjejeniyar Amurka da Iran

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah sun amince da tsagaita wuta a Lebanon bayan wani harin da aka kai cikin dare wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 47, a cewar ma'aikatar lafiya.

    Isra'ila ta ce hare-haren na mayar da martani kan ayyukan ƙungiyar Hezbolah, ciki har da wani harin da aka kai cikin dare wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Isra'ila huɗu.

    Tsagaita wutar ta fara aiki ne da ƙarfe 16:00 agogon ƙasar amma ƴan wakilan mu da ke ƙasa sun ce anci a gaba da kai hare-hare.

    Wannan dai wani gwaji ne na yarjejeniyar da Amurka da Iran suka ƙulla a farkon wannan makon, wadda ta buƙaci a dakatar ayyukan soji a dukkan fagen daga da suka haɗa da Lebanon.

    Rundunar IDF dai ta sha alwashin "ci gaba da kawar da duk wata barazana nan take" da kuma "mai da martani kan duk wani abu da Hezbollah ta aikata".

    A halin da ake ciki, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani saɓa alƙawari da Isra'ila ta yi "za a rataya wa Amurka alhakinsa".

  8. Shugabannin duniya na tsokaci kan murabus ɗin Starmer

    UK

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashe daban-daban na ci gaba da tsokaci kan murabus ɗin Firaministan Birtaniya, Keir Starmer.

    Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya gode wa Starmer bisa goyon bayan da ya bai wa ƙasarsa, yana mai cewa tsohon firaministan mutum ne mai "ƙoƙarin yin abin da ya dace da kuma abin da zai taimaka".

    Firaministan Kanada, Mark Carney, ya ce "duniya ta fi samun tsaro kuma ƙawayen ƙasashe sun fi haɗin kai saboda ƙoƙarin da Starmer ya yi".

    Shi ma shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya gode masa kan rawar da ya taka wajen ƙarfafa dangantakar Faransa da Birtaniya, da kuma jajircewarsa a cikin ƙawancen ƙasashen da ke goyon bayan Ukraine. Macron ya kuma yaba da ƙoƙarinsa na farfaɗo da dangantaka tsakanin Birtaniya da Tarayyar Turai.

    Firaministan Ireland, Micheál Martin, ya ce Starmer ya yi aiki tare da gwamnatinsa wajen "buɗe wani sabon babi na dangantaka tsakanin Ireland da Birtaniya, domin amfanin al'ummomin ƙasashen biyu."

  9. Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bankaɗo tarin man fetur da aka ɓoye a Rivers

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin ruwan Najeriya sun bayyana cewa dakarun Operation DELTA SENTINEL sun gano wata ɓoyayyar ma’adanar man fetur da ake tacewa ba bisa ƙa’ida ba, tare da kama wata mota da ake zargin tana safarar haramtaccen mai a jihar Rivers.

    A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, jami’an sojin jirgin ruwan yakin NNS SOROH sun kai samame ne bayan samun sahihan bayanan sirri zuwa yankin Okolomade a ƙaramar hukumar Abua-Odual, inda aka ce ana safarar man fetur da aka tace ba bisa ka’ida ba ta cikin dazukan Orashi.

    Yayin gudanar da aikin, jami’an sun kama wata mota wacce ake zargin tana ɗauke da man diesel (AGO) da aka tace ba bisa doka ba.

    Daga bisani, an ƙwato man da yawansa ya kai kimanin lita 63,290 tare da motar da ake zargin ana amfani da ita wajen safarar man.

    Rundunar sojin ruwan ta ce hakan ya daƙile wata muhimmiyar hanyar safarar haramtaccen mai, tare da jaddada ƙudirinta na ci gaba da yaƙar masu yi tattalin arzikin ƙasa ta'annati.

  10. "DPO ne ya cire wa matata hijabi, ya tura ta kan titi": Mijin da aka kashe matarsa a Marabar Jos

    ....

    Asalin hoton, Family

    "Tun ana saura kwana biyu ta rasu nake jin gabana yana faɗuwa amma ina tsoron na faɗa mata saboda kada ta tayar da hankalinta," in ji Aliyu Muhammad, wanda a ranar Lahadi ya iske gawar matarsa Ummulkhairi ƙone kan titi, bayan mutane sun zarge ta da satar yara.

    Aliyu ya tattauna da BBC ne kwana ɗaya bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, kan yadda mutane suka kashe tare da ƙona wata mata a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

    Mutumin - wanda ke aikin kanikanci - ya shaida wa BBC, cewa sun yi sallama da matarsa da safe: "lokacin da zan fita, ta ce min suna da wa'azi a makarantar Malama Mardiyya," - wata makarantar Islamiyya da ke garin, yayin da shi kuma ya kama hanya zuwa wurin aiki.

    Sai dai wannan ita ce rabuwa ta ƙarshe tsakanin mata da mijin, waɗanda suka kwashe shekara 14 a tare, inda suka haifi ƴaƴa huɗu - biyu maza, biyu mata.

    Ya bayyana cewa kimanin ƙarfe 11 na safe aka kira shi kan cewa matarsa tana gidan mai unguwa, bayan an kama ta da zargin kasancewa mai satar yara.

    Duk da cewa Aliyu ya tura abokinsa zuwa gidan mai unguwa, amma tuni mutane suka cika ƙofar gidan suna neman a ba su ita domin su hukunta ta, bayan zargin ta da satar yara.

  11. An rantsar da Andy Burnham a Majalisar Dokokin Birtaniya

    Andy Burnham

    Asalin hoton, House of Commons

    An rantsar da Andy Burnham a matsayin sabon ɗan Majalisar Dokokin Birtaniya mai wakiltar mazaɓar Makerfield, inda ya samu kyakkyawar tarba daga 'yan jam'iyyar Labour a zauren majalisar.

    Burnham ya shiga zauren Majalisar Wakilai ta Birtaniya ana masa tafi da murna daga ƴan jam'iyyar ta Labour kafin ya yi rantsuwar kama aiki.

    Ya yi rantsuwar ne tare da sabbin 'yan majalisar biyu, Lara Bird ta jam'iyyar SNP da Douglas Lumsden na jam'iyyar Conservative, waɗanda su ma suka samu nasara a zaɓukansu.

    Yayin da yake ratsawa cikin zauren majalisar, Burnham ya riƙa sunkuyar da kai tare da yin murmushi ga 'yan majalisar da suka tarbe shi.

    House of Commons

    Asalin hoton, House of Commons

    Sabon ɗan majalisar mai wakiltar Makerfield yana cikin 'yan majalisa uku da aka rantsar, tare da Douglas Lumsden wanda ya lashe zaɓen cike gurbi a Aberdeen South da kuma Lara Bird wadda ta riƙe kujerar Arbroath da Broughty Ferry a ƙarƙashin jam'iyyar SNP.

  12. Sojojin Najeriya sun daƙile harin ƴanbindiga, sun ceto mutane a Sokoto da Katsina

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun samu manyan nasarori a ayyukan da suka gudanar a jihohin Sokoto, Katsina da Kaduna, inda suka kashe ‘yanbindiga tare da ceto waɗanda aka sace da kuma ƙwato dabbobi da makamai daga hannun masu laifi.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce a jihar Sokoto, dakarun sun daƙile yunƙurin wani hari da ‘yanbindiga suka yi a garin Tureta, bayan samun sahihan bayanan sirri, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa.

    Bayan haka, jiragen yaƙin sojoji sun bi sawun maharan har zuwa ƙauyen Sulubawa Gidan Kare, inda aka kai farmaki tare da kuɓutar da mutanen da aka sace da kuma ƙwato shanu, duk da cewa dakarun sun fuskanci kwanton ɓauna daga ‘yan ta’addan.

    A jihar Katsina kuwa, dakarun sun kai farmaki na bazata a wani sansanin ‘yan ta’adda da ke ƙaramar hukumar Matazu da safiyar 22 ga watan Yuni, 2026, inda suka kashe guda biyu daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka.

    Hakazalika a jihar Kaduna, dakarun sun hallaka ‘yan bindiga biyu a wani farmaki yayin yunƙurin satar shanu, tare da ƙwato makamai da dabbobin da aka sace.

  13. Yawancin ƴan Isra'ila na ganin cewa Iran ce ta yi nasara a yaƙin da aka fafata

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mafi yawan ƴan Isra’ila na ganin cewa Iran ce ta yi nasara a yaƙin da aka fafata, duk da ikirarin da firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu, ke yi na cewa Isra’ila ce ta yi galaba.

    Wannan ya fito ne daga sakamakon wani bincike da jami’ar Hebrew ta Jerusalem ta gudanar, wanda ya nuna bambancin ra’ayi tsakanin shugabanci da jama’a.

    Rahoton binciken ya nuna cewa kusan kashi 92 cikin dari na wadanda aka tambaya sun ɗauki Iran a matsayin wadda ta yi nasara, yayin da da dama suka nuna rashin gamsuwa da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da Amurka.

    Haka kuma, sun bayyana damuwa cewa hare-haren da aka kai na iya raunana tsaron Isra’ila a nan gaba.

    Duk da wannan ra’ayi, Netanyahu ya dage cewa hare-haren da Isra’ila ta kai, tare da goyon bayan Amurka, sun hana Iran samun makamin nukiliya tare da rage karfinta na soja.

    Ya ce kuma an lalata kadarori masu yawa a Iran tare da kashe wasu manyan kwamandojin soja da yake zargin suna shirin kai hari ga Isra’ila.

  14. Ƙasashen da aka fitar da su daga Gasar Kofin Duniya

    Turkiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Zuwa yanzu an fara fitar da tawagar wasanni ƙasashe daga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da ke gudana a Amurka da Mexico da Kanada.

    Ƙasashe 48 ne ke fafatawa a gasar, inda kowa ke neman tikitin zuwa zagayen gaba na kifa ɗaya ƙwala ta hanyar samun maki a wasannin rukuni.

  15. An samu ci gaba kan yadda za a warware rikicin Lebanon - Araghchi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce an samu gagarumin ci gaba wajen kawo ƙarshen rikicin Lebanon, wanda yake daga cikin manyan manufofin Iran a tattaunawar da ta yi da Amurka a Switzerland.

    Ya bayyana cewa matakan da aka ɗauka a tattaunawar sun nuna yiwuwar samun ci gaba mai dorewa wajen dakatar da rikicin.

    Ya ƙara da cewa gwajin farko na wannan nasara shi ne yadda sabuwar hanyar haɗin gwiwar “de-confliction cell” za ta fara aiki tsakanin Iran, Amurka da Lebanon domin tabbatar da tsagaita wuta da kauce wa sake barkewar rikici.

    A halin da ake ciki, masu shiga tsakani daga ƙasashen Pakistan da Qatar sun tabbatar da cewa an kammala zagaye na farko na tattaunawar da ake yi a Switzerland tsakanin Amurka da Iran, inda suka ce an samu ci gaba mai ƙarfafawa.

    Sun kuma bayyana cewa an tsara wata hanya da za ta kai ga cimma yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60 masu zuwa.

    Sai dai duk da kammala wannan mataki na farko, an ce za a ci gaba da tattaunawar a cikin makon nan domin zurfafa tattaunawa kan batutuwan da suka rage.

    A lokaci guda, Shugaban Lebanon, Joseph Aoun, ya fara tattaunawa da jami’an Amurka da Qatar kan yadda za a tabbatar ɗa dorewar tsagaita wuta da zaman lafiya a yankin.

  16. An ƙirƙiri tsarin sa ido don tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon - Iran

    Mai magana da yawun tawagar Iran da ke cikin tattaunawar Amurka da ƙasar, Esmail Baqaei, ya bayyana cewa an tsara wani tsari na musamman domin sa ido kan tabbatar da tsagaita wuta a Lebanon.

    Ya ce wannan tsari yana daga cikin muhimman abubuwan da aka cimma a tattaunawar da ake yi a Switzerland.

    Baqaei ya ce an samar da tsarin ne tare da haɗin gwiwar ƙasashen Qatar da Pakistan da ke shiga tsakani, domin tabbatar da cewa an kawo ƙarshen yaƙin a Lebanon.

    Ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da an ci gaba da kiyaye zaman lafiya a yankin.

    Ya ƙara da cewa bisa tanadin sashe na farko na yarjejeniyar, wajibi ne a dakatar da yaƙi da duk wani aikin soja a dukkan wurare, ciki har da Lebanon.

    A cewarsa, kafa wannan tsarin na nuni da cewa ana son tabbatar da tsagaita wutar ya ɗore ba tare da tangarɗa ba.

    Haka kuma, Baqaei ya ce an samu ci gaba mai kyau dangane da alƙawarin Amurka na sakin wasu kadarorin Iran da aka ƙwace a baya, wanda yake daga cikin manyan batutuwan tattaunawar.

  17. Keir Starmer yayi murabus daga muƙamin firaministan Birtaniya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya sanar da cewa zai sauka daga muƙaminsa na jagoran ƙasar da kuma shugaban jam’iyyar Labour, bayan ya fuskanci matsin lamba daga cikin jam’iyyarsa.

    Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar, inda ya ce ya riga ya sanar da Sarkin ƙasar, Charles game da matakin da ya ɗauka.

    Starmer ya ce kafin ya karɓi jagoranci, jam’iyyar Labour tana cikin wani hali na rauni a fannonin siyasa da tattalin arziki. Duk da wannan, ya jaddada cewa ya yi aiki tukuru wajen sauya alkiblar jam’iyyar, inda ya magance wasu manyan matsaloli da suka addabe ta, ciki har da zarge-zargen wariyar addini, tare da dawo da martaba a fannoni kamar tsaro da tattalin arziki.

    Ya kuma bayyana cewa a yanzu jam’iyyarsa tana tambayar ko shi ne mafi dacewa da zai jagorance ta zuwa babban zaɓe mai zuwa

    Starmer ya kuma ce zai ci gaba da riƙe mukamin firaminista na ɗan lokaci har sai an zaɓi sabon shugaban jam’iyyar kafin dawowar majalisar dokoki daga hutun bazara.

    Ya kuma yi alkawarin tabbatar da mika mulki cikin natsuwa, tare da mika cikakken goyon baya ga wanda zai gaje shi, yayin da ya gode wa abokan aikinsa da ma’aikatan gwamnati kan gudunmawar da suka bayar.

  18. An kammala zagayen farko na tattaunawar Iran da Amurka a Switzerland

    ....

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    An kammala zagayen farko na tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka a Switzerland, inda tawagar Iran ta fice daga wurin bayan zaman farko.

    Masu shiga tsakani wato Qatar da Pakistan sun bayyana cewa za a ci gaba da tattaunawar a cikin makon nan.

    A cikin sanarwar haɗin gwiwa, ƙasashen biyu sun ce ɓangarorin sun cimma matsaya kan wata hanya da za a bi domin kai ga yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60 masu zuwa.

    Haka kuma sun bayyana cewa an amince da kafa wata hanya ta dakatar da yaƙi a Lebanon, domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

    Bugu da ƙari, masu shiga tsakani sun ce Iran da Amurka sun amince da ƙirƙirar wata hanyar sadarwa kai tsaye domin kauce wa rikice-rikice da rashin fahimta a mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci ga jigilar kayayyaki da makamashi a duniya.

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa an samu “gagarumin ci gaba” a tattaunawar, inda ya ce an ɗage takunkumin fitar da man fetur da na petrochemical da aka sanya wa ƙasar.

    Ya ƙara da cewa an saki wasu daga cikin kadarorin Iran da aka ƙwace yana mai jaddada cewa hakan na daga cikin manyan nasarorin tattaunawar.

  19. Nijar ta bayyana sharuɗɗanta na buɗe iyaka da Benin

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin sojin Nijar ta bayyana cewa buɗe iyakarta da Benin zai dogara ne kan wasu muhimman sharuɗɗa da suka haɗa da sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsaro da za ta hana kowace ƙasa amfani da ƙasarta wajen kai hari da tabbatar da cikakken bayani kan duk wani sojin ƙetare da ke yankin iyaka da kuma kafa tsarin musayar bayanan sirri tsakanin ƙasashen biyu.

    Ta ce ba za ta sauka daga waɗannan sharuɗɗan ba yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakan

    Wannan ya biyo bayan wata ganawa da aka gudanar a Cotonou tsakanin jami’an ƙasashen biyu, inda aka tattauna hanyoyin dawo da dangantaka ta yau da kullum.

    Jami’an Nijar sun ce tattaunawar ta kasance mai ma’ana, kuma ta samar da wata kafa da za ta kai ga inganta alaƙar diflomasiyya.

    Amma sun jaddada cewa batun tsaro da na soji su ne suka fi mayar da hankali a kai, la’akari da rashin yarda da juna da ke tsakanin Niamey da Cotonou.

    Dangantakar ƙasashen biyu ta taɓarɓare ne tun bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar a watan Yulin 2023, inda Nijar ta zargi Benin da marawa wasu ƙasashen waje baya wajen kawo cikas.

    Nijar ta kuma danganta wasu hare-haren tsaro da suka faru, ciki har da kai hari filin jirgin Niamey, da taimakon waje, zargin da Benin ta musanta.

    Duk da haka, ƙasashen biyu sun fara sabuwar tattaunawa domin farfaɗo da kasuwanci da inganta tsaro.

  20. An ɗage mana takunkumin man fetur tare da sakin wasu kadarorinmu - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da ƙasarsa ke yi da Amurka a Switzerland.

    Ya ce an ɗage takunkumin da aka sanyamu kan fitar da man fetur da kayan petrochemical, sannan an dakatar da toshe ruwa da aka yi wa Iran.

    Araghchi ya kuma ce an saki wasu daga cikin kadarorin Iran da aka ƙwace a kasashen waje, tare da fara aiwatar da wani babban shiri na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

    Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya jaddada cewa matakan na daga cikin nasarorin tattaunawar.

    Ministan ya gode wa ƙasashen Pakistan da Qatar bisa rawar da suka taka wajen shiga tsakani, yana mai cewa hakan ya haifar da babbar nasara wajen ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Lebanon.

    Ya ce daga cikin matakan da aka tsara akwai kafa wata hanya ta tabbatar da dakatar da faɗa a Lebanon a matsayin gwajin farko na yarjejeniyar.

    A ƙarkashin yarjejeniyar tsakanin Iran da Amurka, batutuwan da suka haɗa da dakatar da yaƙi a dukkan fannoni da sassauta takunkumi kan fitar da mai, da kuma sakin kadarorin da aka ƙwace na daga cikin manyan abubuwan da ake tattaunawa a kai, yayin da ake ci gaba da tattaunawa domin cimma yarjejeniya ta ƙarshe.