Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 23/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Salva Kiir ya rusa gwamnatinsa

    Shugaban ƙasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya rusa gwamnati tare da naɗa gwamnatin riƙon ƙwarya, matakin da ya ce zai share fagen gudanar da zaɓen ƙasar na farko a tarihi wanda ake sa ran yi a watan Disamba.

    Masu sukar matakin dai sun yi gargadin cewa hakan zai bai wa shugaban cikakken iko ba tare da wata takura ba.

    A bangare guda kuma, Mista Kiir ya cire dukkan mataimakan shugaban ƙasa da aka naɗa ƙarƙashin yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasar ƙasar.

    Haka kuma an sallami ministoci, da shugabannin ƙananan hukumomi da kuma jami'an majalisun dokoki na ƙasa da na jihohi.

    'Yan adawa a kasar dai sun yi Allah-wadai da wadannan sauye-sauyen, waɗanda suka soke muhimman tanade-tanaden yarjejeniyar zaman lafiyar, ciki har da haɗa rundunonin sojojin da suka yi gaba da juna da kuma kammala rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.

  2. Manyan wakilan Amurka sun gana da jami'an gwamnatin Iran

    Manyan wakilan shugaba Donald Trump sun gudanar da tattaunawar keke da keke ta farko a cikin watanni tare da manyan jami'an gwamnatin Iran.

    Shugaba Trump ya ce ganawar ta sa'o'i uku, wadda aka yi a gefen taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a birnin New York, ta kasance mai matukar amfani.

    Kafofin yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun ce babban dalilin tattaunawar shi ne isar da sharuddan Tehran na sake buɗe Mashigar Hormuz.

    Rahotanni sun ce daga cikin sharuddan akwai janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba da kuma sakin kadarorin Iran da aka yi.

    Tun da farko, Mista Trump ya shaida wa taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniyar cewa, Iran ta daɗe tana zama barazana, amma ya bayyana cewa yana da yaƙinin za a cimma yarjejeniya bayan zaɓen rabin zangon na Amurka da za a gudanar a watan Nuwamba mai zuwa.

  3. Firaiministan Birtaniya ya gargaɗi duniya kan haɗarin AI

    Firaministan Birtaniya, Andy Burnham, ya yi amfani da jawabinsa a babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya wajen gargadin duniya a kan haɗarin da ke tattare da rashin ƙa'ida a wajen amfani da kirkirarriyar basira ta AI, da kuma yaɗa labaran ƙarya da Rasha ke yi.

    Mista Burnham, ya ce yana son jagorantar ƙoƙarin da ake a duniya na samar da dokoki da ƙa'idojin ƙasa da ƙasa da za su tsara yadda ake amfani da AI.

    Firaministan ya zargi Rasha da gudanar da abin da ya kira yaƙin yaɗa labaran ƙarya da kuma ɓoyayyen tasiri a Birtaniya.

    Wakilin BBC ya ce Sa'o'i kaɗan bayan ganawarsa ta farko ido-da-ido da Shugaba Donald Trump, Firaministan ya gabatar da jawabinsa na farko a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, in da ya ce ya umarci manyan jami'an tsaro da su fara aiki kan kafa sabuwar Cibiyar Ƙasa ta Kare Bayanai, da za ta mayar da hankali wajen ganowa, da tantancewa da kuma dakile abin da ya bayyana a matsayin hare-haren yaɗa labaran karya da ƙasashen waje ke yi.

  4. Manyan ƙasashe na buƙatar rage bashin da suke ci - IMF

    Shugabar Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ta yi gargadin cewa manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arziƙi na bukatar rage bashin da suke ci tare da saukaka nauyin bashin da ke kansu, bayan da farashin biyan kuɗin ruwa kan basussukan gwamnati ya yi tashin gwauron zabi a makonnin baya-bayan nan.

    Da take zantawa da BBC, Kristalina Georgieva, ta yi kira da a ɗauki matakan gaggawa, duk da cewa za su iya yin tsauri, domin daƙile yawaitar bashin gwamnati.

    Ta ce duk da cewa gwamnatoci ba za su iya shawo kan wasu abubuwan da ke faruwa a waje ba, kamar yaƙin Iran, suna da ikon tsara manufofin cikin gida da za su taimaka wajen shawo kan matsalolin tattalin arziƙi.

    Game da yadda za a inganta haɓakar tattalin arziƙi, Misis Georgieva, ta ce babban zaɓin da ya rage shi ne aiwatar da sauye-sauye da za su tallafa wa kamfanoni masu zaman kansu, saboda a cewarta gwamnatoci ba su da isassun kuɗaɗen da za su ɗauki nauyin hakan.

  5. Assalamu alaikum

    Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Litinin. Muna barka da wannan rana ta Laraba da Bahaushe ke yi wa taken 'tabawa ranar samu'.

    A yau ma kamar kodayaushe za mu ɗora daga inda muka tsaya domin ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram da YouTube domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo har ma da tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.