BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Boko Haram na dab da zama tarihi - Zulum
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Lahadi 5/4/2026
Lewandowski da wasu fitattun ƴan wasan da ba za su je Gasar Kofin Duniya ba
Gasar Kofin Duniyar ta kunshi ƙasashe 48, sai dai akwai fitattun ƴan wasa da suka kasa tsallakewa zuwa gasar.
Abin da likitoci da masana suka gano kan 'gicciye Yesu'
An yi amfani da wata ƙusa mai tsayin santimita 12.5 wajen buga hannun Yesu a jikin katako, inda ya ce hakan zai sanya ƙusar ta lalata wasu muhimman jijiyoyi tare da haifar da tsananin raɗaɗi, in ji wani masani kan jini a Amurka.
'Daga yau ke ba ƴar'uwata ba ce' - yadda yaƙi ke raba kan ƴan'uwan juna a Iran
Mutane a Iran sun kwatanta yadda yaƙin ke kara janyo fushi tsakanin ƴan uwa har ma da raba kawunansu.
'Abin da ya sa na yanke shawarar ƙin yin aure' - Yadda wasu matan Najeriya suka 'boƙare'
A Najeriya, ƙasar da wasu ke kallon haihuwa a matsayin wani muhimmin al'amari a rayuwar mace, wasu matan sun yi hannun riga da wannan tunani, inda suka yi watsi da duk wani matsi na amincewa da hakan.
A karon farko cikin shekaru 43, shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya zai sami mataimaki
A 1972 aka soke muƙamin mataimakin shugaban ƙasa a Kamaru, inda a bisa tsarin baya shugaban majalisar dattawa ne zai zamo muƙaddashin shugaban ƙasar idan wani abu ya faru da shugaban, har zuwa lokacin da za a yi sabon zaɓe.
Mun bai wa Iran kwana biyu ta amince da yarjejeniya ko ta sha 'ruwan wuta' - Trump
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da sauran batutuwan da ke faruwa a duniya 4/4/2026
Ƙasashen da al'umma suka fi farin ciki a duniya cikin shekara 2026
Jerin wanda cibiyar nazarin lafiya ta Oxford ke fitarwa tare da haɗin gwiwar hukumar ci gaba mai ɗorewa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, na la'akari ne da yanayin ƙarfin tattalin arziki, da tallafin zamantakewa, da tsawon rayuwa, da ƴancin walwala a ƙasashe 140 na duniya.
Aiki mai haɗari: Yadda Amurka ke neman matuƙin jirgin yaƙinta a Iran
Ana ci gaba da aikin neman sauran ma'aikatan jirgin a cikin Iran kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS, mai hulɗa da BBC ta bayyana.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 6 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 5 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 5 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 5 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
Arsenal za ta yi gogayya da Liverpool wajen neman Gordon, Chelsea na son Barco
Chelsea na neman dan baya daga Strasbourg , Inter na bibiyar golan Spurs, Liverpool kuma na son kara karfin bayanta.
Man U da Man City na son Anderson, Liverpool za ta sallami 'yan wasan da suka gaza
Man U da Man City na son Anderson, Liverpool za ta sallami 'yan wasan da suka gaza, Dan wasan tsakiya na Ecuador, Moises Caicedo ya ce yana da niyyar ci gaba da zama a Chelsea.
Arsenal da Man City da PSG na neman Olmo, Salah zai koma Saudiyya
RB Leipzig ta sanya farashin Yan Diomande fam miliyan 87 , Saudiyya na ƙara matsa lamba kan Mohamed Salah, Everton na ƙara kwarin gwiwa kan Jack Grealish.
Fitattun ƙasashen da ba za su buga kofin duniya ba a 2026
Fitattun ƙasashe da ke taka rawar gani a nahiyar turai da dama da na Afirka sun kasa samun damar buga gasar kofin duniya a wannan karon.
Wakilan Tonali sun tuntuɓi Real Madrid, Liverpool da Man U na zawarcin Diomande
Everton na bibiyar halin kwantiragin John Stones, wakilan Sandro Tonali sun tuntubi Real Madrid, Barcelona na kan gaba wajen neman Bernardo Silva.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Ko Obi da Kwankwaso za su kawo wa Atiku cikas wajen samun takara?
Kawo yanzu dai Peter Obi da Rotimi Amaechi sun riga sun sanar da aniyar su ta yin takarar shugaban ƙasa, yayin da Rabi'u Kwankwaso da Atiku Abubakar ba su bayyana aniyar yin takarar ba.
Yaƙin Iran ya illata ƙasashen yankin Gulf, wane sauyi za a samu?
An daɗe ana kallon yankin Gulf a matsayin wuri mai kwanciyar hankali da kuma burin jawo hankalin masu zuba jari daga manyan kamfanoni da kuma ƙwararrun ma'aikata zuwa cikinsu.
China ta shiga tsaka-maiwuya bayan ɓullo da tsarin taƙaita haihuwa
Kwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce al'ummar China za ta ci gaba da raguwa, inda ta yi kiyasin cewa ƙasar za ta rasa sama da rabin al'ummarta a karshen ƙarni.
Yadda aka gicciye Yesu Almasihu a mahangar Kirista
Mabiya addinin Kirisita a fadin duniya kan gudanar da bukukuwan Easter duk shekara domin tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.
Za a gudanar da gagarumin taron Musulmi a Paris
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 03/04/2026
Dauloli huɗu da suka fi ƙarfi a tarihin yammacin Afirka
Tsakanin ƙarni na 8 da 16 an yi hamshaƙan dauloli a yammacin Afirka. Duk da cewa daga baya sun dusashe, amma sun bar tarihin da har yau ana alfahari da su.
Wace illa matakin INEC zai yi ga ADC?
''Tun daga lokacin da aka ga mutane suna tururuwa suna shiga wannan jam'iyya tamu ta ADC, hankalin gwamnatin Tinubu ya tashi, ta san cewa ƴan Najeriya ba za su bari ta tsallake shekarar 2027 ba...," in ji ADC.
Yadda Boko Haram ta yi wa mutane 20 yankan rago a Borno
Ƙungiyar Boko Haram dai ta kwashe shekaru tana ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Falle Ɗaya: Me take nufi kuma daga ina ta samo asali?
Idan akwai wata kalma da za ta samu karɓuwa a wurin ƴan siyasa musamman a arewacin Najeriya to ita ce kalmar Falle Ɗaya wadda a yanzu haka amonta kawai ake ji na tashi a cikin wake da waƙoƙin siyasa.
Ko Iran ta yi wa Amurka da Isra'ila ba-zata?
Lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan Iran ranar 28 ga Fabrairun 2026, tambayar ita ce tsawon wani lokaci yaƙin zai ɗauka?
'Yadda aka kama ni bayan sayen layin waya da ƴan bindiga suka taɓa amfani da shi'
A baya-bayan nan ne ƴansanda suka tsare wata matashiya mai suna Tititlayo Ibrahim, ƴar jihar Ondo kan laifin da ba ta san komai a kai ba bayan sayan layin waya da aka taɓa amfani da shi.
Shin muna tunkarar yaƙin duniya na uku ne ko ana razana mu ne kawai?
A wata hira da BBC a watan Fabrairu, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce ya yi amanna cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya riga ya fara yaƙin duniya na 3, kuma mafita ɗaya ce a matsa lamba domin tilastawa Rasha ta dakata.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































