'An raunata sojojin Amurka 365 da kisan 13 tun bayan fara yaƙin Iran'
Amurka ta umarci babban hafsan sojin ƙasanta ya yi murabus
Jami'ar UDUS ta shirya taron nazarin waƙoƙin Ɗan Anace
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza
Amurka ta kama wasu 'yan uwan Qasem Soleimani
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce jami'anta sun kama wata 'yar uwar shugaban sojojin Iran Qassem Soleimani tare da 'yarta wanda aka kashe shekaru shida da suka gabata a wani hari da Donald Trump ya bayar da umarni.
Ma'aikatar Tsaron ta ce an kwace takardunsu na zama 'yan Amurka, saboda Hamideh Soleimani na ci gaba da bayyana goyon bayanta ga gwamnatin Iran.
An soke wa da dama daga cikin ƴan uwan manyan jami'an Iran izinin zama a ƙasa Amurka.
Cikin wata sanarwa, jami'an sun ce ba za su bari Amurka ta zama gida ga 'yan ƙasashen wajen da suke nuna goyon baya ga maƙiya Amurka ba.
"An kai wa wasu masana'antu Iran hari"
Kafar yaɗa labaran Iran ta ce Amurka da Isra'ila sun kai wa wasu masana'antunta hare-hare.
An harba makami mai linzami kusa da cibiyar nukiliya ta Bushehr da ke Kudancin Iran lamarin da yi sanadin mutuwar wani mai gadi.
Duk da haka kamfanin Rosatom na ƙasar Rasha mai kula da cibiyar makaman nukiliyar ya fara kwashe sama da ma'aikata kusan 200.
Rahotanni sun ce an jiyo fashewa ta sama a birnin Ƙudus.
Mutane 5 sun jikkata a birnin Tel Aviv sakamakon hare-haren da Iran ta kai birnin a yau Asabar.
Hotunan yadda hari ya lalata jami'ar Tehran
Hotuna daga Iran sun nuna ɓarnar da rahotanni suka ce wasu hare-haren sama da aka kai Shahid Beheshti Jami'ar Tehran a ranar Juma'a suka janyo.
Tun da sanyin safiyar ranar yau ne, ministan kimiyyar IranHossein Simaee Sarraf ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, EPA
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Ƙaramar ministar ƙwadagon Najeriya ta yi murabus
Asalin hoton, Nkeiruka Onyejeocha X
Bayanan hoto, .
Ƙaramar Ministar kwadagon Najeriya Nkeiruka Onyejeocha ta yi murabus daga muƙaminta.
Ta sanar da murabus ɗin nata ne a shafinta na X, inda ta miƙa godiyarta ga shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya bata dama ta yi aiki da gwamnatinsa.
Ta bayyana ajiye muƙamin nata a matsayin matakin rufe wani gagarumin babi na rayuwarta a matsayinta na ma'aikaciyar gwamnati, kuma ta bayyana burinta na ci gaba aiki tuƙuru wajen ciyar da Najeriya gaba.
Shugaba Tinubu ne ya shaida wa duka masu riƙe da muƙaman siyasa cewa idan suna da burin tsayawa takara a 2027 to su ajiye muƙamansu nan da 31 ga watan Maris 2026, yadda komai zai tafi daidai babu cuta babu cutarwa.
Mun bai wa Iran kwana biyu ta amince da yarjejeniya ko ta sha 'ruwan wuta' - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya bai wa Iran wa'adin kwana biyu ta amince da ''yarjejeniya'' ta kuma buɗe mashigar Hormuz ko ''mu yi mata ruwan wuta''.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce: ''Ku tuna lokacin da na bai wa Iran kwana 10 ta amince da yarjejeniya ko ta buɗe mashigar Hormuz. Yanzu lokaci na ci gaba da ƙurewa''.
"Yanzu saura sa'a 48 kafin su sha ruwan wuta...''
A ranar 27 ga watan Maris ne dai Shugaba Trump ya bayyana cewa ya dakatar da duk wani hari kan cibiyoyin makamashin Iran na tsawon kwana 10.
Ƴanmajalisar Kamaru sun amince da ɓullo da muƙamin mataimakin shugaban ƙasa
Asalin hoton, Getty Images
Ƴan majalisar dokokin Kamaru sun sake amincewa ƙudirin ɓullo da maƙamin mataimakin shugaban ƙasar, wanda aka rushe fiye da shekara 50 a ƙasar.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin halin rashin tabbas kan wanda zai gaji Shugaba Paul Biya.
A lokacin zaman majalisar na yau, mambobin majalisar 200 ne suka amince da ƙudirin, yayin da 18 suka nuna adawa da matakin, sai kuma huɗu da ba su kaɗa ƙuri'a ba.
Idan ƙudirin ya zama doka bayan sa hannun shugaban ƙasa, za a nada mataimakin shugaban ƙasar.
Bidiyon yadda sojojin Iran ke harbin jiragen yaƙin Amurka
Sashen tantance labarai na BBC ta tabbatar da sahihancin wani bidiyo da ke nuna yadda wasu sojojin Iran uku ke harbin wasu jiragen yaƙin Amurka masu saukar ungulu.
Mun fahimci an ɗauki bidiyon ne a lardin Kohgiluyeh da Boyer-Ahmad.
Hotunan jiragen ya yi daidai da jiragen da ke aikin neman matuƙin jirgin yaƙin Amurka da ya ɓace bayan Iran ta harbo jirgin da yake ciki a lardin Khuzestan mai maƙwabtaka.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Jami'ar UDUS ta shirya taron nazarin waƙoƙin Ɗan Anace
Cibiyar Nazarin Harshen Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ta shirya wani babban taro na kwana uku kan nazarin waƙoƙin maza da tarihin shahararren mawakin nan, Muhammadu Bawa Ɗan Anace 'Yartsakuwa.
Taron ya samu halartar masana kusan 100 a Najeriya da ma jamhuriyar Nijar, waɗanda suka gabatar da muƙaloli daban-daban a kan ɓangarorin da suka shafi harshe da al'ada da kuma adabi.
A samu halartar sarakunan ciki har da mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III da gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu da makada ciki har da wasu daga iyalan Ɗan Anaci da suka rage da kuma mutum biyu da ya yi wa waƙa wato Umaru Gindumi da Bagobiri Dantcimau da sauran mahalarta da manazarta.
An haifi Muhammadu Bawa Ɗan Anace Gandi a shekarar 1901 inda ya rasu a 1986 yana da shekara 85, a duniya.
Ya yi shuhura a waƙoƙinsa da suka fi mayar da hankali kan noma da dambe da kuma kokowa, waɗanda aka fi sani da "waƙoƙin maza".
Bawa Ɗan'ance ya fara waƙa ne tun yana yaro matashi, saboda tasowarsa a wurin kawunsa Anace.
Ya yi wa manyan ƴanwasan dambe irin su Dan Dunawa da Shago da Ado Dankore da sauran su waƙa.
Da farko dai Ɗan'ance ya fara ne da kiɗin dambe, sannan daga baya ya watsar ya koma kiɗan noma.
A kiɗin noma ne ya yi fice duk da cewa daga baya ya koma kiɗan dambe, inda ya haɗu da su Muhammadu Shago da Ɗandunawa da sauran 'yan dambe da ya yi wa waƙa.
Wasu daga waƙoƙinsa sun haɗa da waƙar Shago da ta Ado Ɗan Kore da Audu Kai Kaɗai Gayya, da Maigidan Gona da ta Garba na Godi da waƙar Basabce da sauran su.
Bayanan hoto, Daga dama Ɗan dambe Alh. Yahaya Ibrahim Bargaja da aka fi sani da Bagobiri Ɗantcimau ne tare da abokin karawarsa (hagu) wato Ɗan dambe Umaru Gundumi
Hotunan ɓarnar harin Iran a Ramat Gan da ke Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ambato sashen kula da motocin ɗaukar marasa lafiya na hukumar bayar da agajin gaggawar Isra'ila na cewa yana aiki a wurare shida da ke tsakiyar Isra'ila bayan hare-haren Iran na yau Asabar.
Hare-haren na makamai masu linzami sun lalata gine-gine a birnin Ramat Gan, da ke gabashin Tel Aviv, babban birnin Isra'ila, kamar yadda hotunan suka nuna.
Babu labarin rasa rai a hare-haren.
Tun da farko, Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta ce ta gano wasu makamai masu linzami da Iran ta harba sun tunkari ƙasar, inda suka buƙaci mutane su shiga wuraren fakewa.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ce ta kai hare-hare kan 'muhimman cibiyoyin fararen hula' a Tehran
Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta ce ta kammala "jerin hare-hare kan cibiyoyin gwamnatin ta'addanci'' a Tehran a ranar Juma'a.
Sojojin sun ce sun kai hari cibiyoyin tsaro ''inda ake ajiye makamai masu linzami'' da kuma wasu cibiyoyin soji ''da ke kare binciken gwamnati''.
IDF ta ci gaba da cewa "waɗannan hare-hare na daga cikin yunƙurin da muke yi na ƙara warzaga shirin gwamnatin ta'addanci''.
Mun goyi bayan matakin INEC kan ADC - Jama'iyyar APC
Asalin hoton, APC
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce ta goyi bayan matakin da hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta ɗauka kan jam'iyyar hamayya ta ADC.
INEC ta soke shugabanci ADC tare da janye sunayen shugabannin jam'iyyar, tsagin David Mark daga shafinta saboda wani hukuncin kotu.
Cikin wata hira da BBC daraktan yaɗa labaran sakatariyar APC, Mallam Bala Ibrahim ya ce hukumar zaɓe, kamar alƙali ne, ba ta goyon bayan kowane ɓangare a harkar zaɓe, aikinta shi ne ta yi adalci ga kowa.
Dangane da zargin da ADC ke yi wa APC na amfani da hukumar zaɓe domin muzguna mata kuwa, Mallam Bala Ibrahim ya ce sam ba haka ba ne.
''Rikicinsu ne na cikin gida, magana tana kotu, kuma yayin da magana ke gaban kotu kamata ya yi a bar kotu ta kammala aikinta'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa matakin da INEC ta ɗauka yana kan doron shari'a, saboda biyayya ne ga hukuncin kotu.
''Mu mun yarda da matsayin da hukumar zaɓe ta ɗauka na janye goyon bayan shugabancin kowane ɓangare na David Mark da na Bala Nafi'u'', in ji shi.
Harin Iran ya raunata ma'aikacin lafiyar Isra'ila ɗaya
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra'ila, (MDA) ta ce ɗaya daga cikin ma'aikatanta ya samu rauni bayan da sojojin Isra'ila suka ce sun ƙoƙarin kakkaɓo makaman linzami da Iran da harba cikin ƙasar.
Mutumin mai shekara 45 ya samu ƙananan raunukan saboda fashewar gilashi a birnin Bnei Brak da ke tsakiyar ƙasar.
Hukumar ta ce an kai mutumin asibiti.
Ƴan sama-jannati da suka tafi duniyar wata na ci gaba da luluƙawa
Asalin hoton, NASA
Ƴan sama-jannatin nan huɗu da ke cikin wani kumbo mai suna Artemis II na ci gaba da luluƙawa zuwa duniyar wata, inda yanzu suka wuce rabin tafiyarsu.
Ana sa ran kumbon zai isa kusa da wata, ya zagaya shi, sannan ya dawo doron ƙasa cikin mako guda.
Hukumar kula da sararin samaniyar Amurka, NASA ta fitar da wasu hotuna masu ƙayatarwa da aka ɗauka daga cikin kumbon, ciki har da cikakken hoton doron ƙasa da ke nuna zurfin ruwan tekuna masu shuɗi da kuma gajimare masu yawo.
Asalin hoton, NASA
Tun da farko, jagoran tafiyar, Reid Wiseman, ya bayyana irin kyawawan abubuwan da suke gani na duniyarmu daga sararin samaniya.
Tarko INEC ke son ɗana mana kuma ba za mu kamu ba - ADC
Asalin hoton, ADC
Jam'iyyar ADC ta haɗakar ƴan adawar Najeriya ta zargi hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗana mata tarko ta hanyar yunƙurin dakatar da ita daga gudanar tarukanta domin zaɓen shugabanninta.
ADC - tsagin David Mark - ta jaddada aniyar ci gaba da tsare-tsarenta na gudanar da zaɓukan shugabanninta na jihohi da babban taron jam'iyyar na ƙasa, saɓanin gargaɗiin da hukumar zaɓen ƙasar ta yi, yayin da batun rikicin shugabanci ke ci gaba da munana a jam'iyyar
A baya-bayan nan ne dai INEC ta gargaɗi jam'iyyar da kada ta gudanar da tarukan jam'iyyar da za su zaɓi shugabanninta don gudan Matsala.
Cikin wata hira da gidan talbijin na Arise a ranar Juma'a shugaban hukumar Farfesa Joash Amupitan ya ce kotu ta riga ta dakatar da jam'iyyar daga gudanar da komai har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam'iyyar.
Sai dai Kakakin jam'iyyar, Faisal Kabir ya shaida wa BBC cewa, matakin wata ƙullalliya ce domin kafa wa jam'iyyar tarko a hana ta yin tarukan ta yadda daga baya za a ce ba ta da shugabanci, don haka ba za ta shiga zaɓen 2027 ba.
''Tarko aka naɗa mana da wannan, ai su manyan tarukan jam'iyyu, wajibi ne a doka, kuma suna da lokacin yin su, idan wannan lokacin ya ƙure shikenan'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa abin da dokokin Najeriya suka ce shi ne ka sanar da INEC taron jam'iyyarka kwana 21 kafin ranar taron, mu kuma mun riga mun sanar da ita.
Amurka ta umarci babban hafsan sojin ƙasanta ya yi murabus
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin wajen Amurka, Pete Hegseth ya umarci babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar, Janar Randy George ya sauka daga muƙaminsa, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS ƙawar hulɗar BBC a Amurka ta ruwaito.
Kakakin ma'aikatar tsaron ƙasar ta Pentagon, Sean Parnell ya bayyana cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sada zumunta cewa Janar George ''zai sauka daga matsayinsa na babban hafsan sojin ƙasan Amurka na 41 ba tare da ɓata lokaci ba''.
Kawo yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa ake ce ya sauka daga muƙamin nasa.
Matakin na na zuwa ne bayan da Shugaba Trump ya bayyana a wani jawabin da ya yi wa ƙasar cewa ana sa ran yaƙin Amurka da Isra'ila da kuma Iran a gefe guda ya kusa zuwa ƙarshe ''nan ba da jimawa ba''.
A ƙa'ida babban hafsan sojin ƙasan Amurka kan yi wa'adin shekara huɗu.
Tsohon shugaban Amurka, Joe Biden ne ya naɗa George muƙamin a 2023.
Janar George ya fara ya fara aiki da rundunar sojin Amurka ne bayan kammala karatu a makarantar horon manyan hafsoshin sojin ƙasar da ke West Point.
Ya halarci yaƙin yankin Gulf na farko a matsayin kwamandan dakarun ƙasa, sannan a baya-bayan nan ya halarci yaƙe-yaƙen Afghanistan da Iraƙi.
Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce za a maye gurbinsa da mataimakinsa Janar Christopher LaNeve a matsayin riƙo.
'An raunata sojojin Amurka 365 da kisan 13 tun bayan fara yaƙin Iran'
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce sojojin ƙasar 365 ne suka samu raunuka tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra'ila da kuma Iran a gefe guda.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce sojojin sun fito ne daga rundunoni daban-daban da suka haɗa da:
Sojojin kasa - 247
Sojojin ruwa - 63
Sojojin sama - 36
Dakarun ƙundunbala - 19
Ma'aikatar ta kuma waɗanda suka mutu sakamakon yaƙin su 13 ne.
Makaman rokar Iran sun faɗa tsakiyar Isra'ila
Asalin hoton, Getty Images
Wasu makaman roka da Iran ta harba sun faɗa wasu yankuna masu cikowar jama'a a sassan tsakiyar Isra'ila da safiyar yau Asabar.
Ma’aikatan agajin gaggawa sun garzaya zuwa wuraren da abin ya shafa a biranen Petah Tikva da Ramat Gan.
Iran na ci gaba da kai hare-hare kan ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya, inda ma’aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta buƙaci jama'a su nemi mafaka bayan na'urar gargadi ta yi kuwa a faɗin ƙasar.
Tun da farko, wani wurin sarrafa iskar gas ya kama da wuta a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sakamakon tarkacen abubuwan da suka faɗo.
Can ma a Kuwait, hare-haren da aka kai sun lalata tashoshin samar da lantarki da tace ruwan sha da kuma matatar mai.
Amurka na neman mutum na biyu cikin matuƙan jirginta da Iran ta harbo
Asalin hoton, ..
Dakarun Amurka na can na ci gaba da neman mutum na biyu, cikin matukan jirgin yakin kasar na da Iran ta harbo jiya Juma'a.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ƙi yin ƙarin bayani kan ƙoƙarin ceton, amma ya ce hakan ba zai shafi tattaunawar da ake yi da Iran ba.
A nasu ɓangaren, hukumomi a Tehran sun buƙaci mazauna yankin da su taimaka wajen gano matuƙin jirgin, har ma suka yi alƙawarin bayar da lada mai tsoka ga duk wanda ya kai rahoton inda yake.
A wani zama na sirri da ƴan majalisar dokokin Amurka, ma'aikatar tsaron ƙasar Pentagon ta ce an harbo jirgin yaƙin ƙirar F-15 ne a yankin kudu maso yammacin Iran, kuma an ceto ɗaya daga cikin matuƙansa, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman ɗayan.
A wani ƙarin koma-bayan ga Amurka, Iran ta ce ta kakkaɓo mata jirgin yaƙi na biyu duk dai a wannan rana.
Kafofin watsa labaran ƙasar sun ce Iran ɗin ta kakkaɓo jirgin ƙirar A-10, a kusa da mashigin Hormuz.
Assalamu alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ta wayi gari.
Ku biyu mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.