Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta miƙa tayin Guimaraes, Inter ta haƙura da Romero
Arsenal ta amince za ta biya Newcastle £77m domin sayen ɗanwasan tsakiyar Brazil mai shekara 28, Bruno Guimaraes. (L'Equipe - in French)
Inter Milan ta shirya biyan £30m kan ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 25, Curtis Jones, amma Liverpool ta dage sai an kai £35m. (Mail)
Inter Milan ta janye daga zawarcin ɗanwasan Tottenham Cristian Romero, kuma wakilan ɗanwasan bayan Argentinan sun ce a yanzu ya karkata ga komawa Sifaniya, inda Real Madrid da Barcelona da kuma Atletico Madrid ke bibiyar ɗanwasan mai shekara 28. (Teamtalk)
AC Milan ta tuntuɓi Arsenal a pkan shirin sayen ɗanwasan gefen Ingila mai shekara 19, Ethan Nwaneri. (Corriere dello Sport - in Italian)
Real Madrid ba ta da niyyar ƙarawa Vinicius Jr kuɗi kuma a shirye take ta sayar da ɗanwasan gaban Brazil ɗin mai shekara 25 idan ya ƙi sabinta kwangilar shi. (ESPN)
Newcastle United na shirin sayen mai tsaron ragar Czech Republic nai shekara 24, Lukas Hornicek, daga Braga. (Talksport)
Hull City ta dage kan ɗamwasan Neom, Amadou Kone yayin da Leeds da West Ham are ke sha'awar ɗanwasan tsakiyar na Ivory coast mai shekara 21. (Teamtalk)
West Ham arena zawarcin ɗanwasan Birtaniya mai shekara 25, Morgan Whittaker, daga abokiyar ghamayyar ta Middlesbrough. (Talksport)
Middlesbrough ta kusa kammala cinikin ɗanwasan gefen Amurka mai shekara 25, Max Arfsten Columbus Crew a kan £5.6m. (Goal)
Wolves ta ƙi amincewa da tayin da Real Sociedad ta gabatar kan ɗanwasan bayan Czech Republic mai shekara 27, Ladislav Krejci, 27. (Fabrizio Romano)