Sojojin Amurka da suka mutu da waɗanda suka jikkata a yaƙi da Iran

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Aƙalla jami'an sojin Amurka 624 ne suka jikkata tun bayan da Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin kai hare-hare kan Iran a watan Fabrairu, bisa sabon rahoton ma'aikatar tsaro ta Pentagon da aka fitar ranar 25 ga Yuli.

Daga cikin waɗanda suka jikkata, 417 na da alaƙa da "Operation Epic Fury", wato farmaki cikin fushi yayin da wasu 207 kuma ke da alaƙa da ayyukan soji a ƙasashen waje.

Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta a watan Afrilu, sannan suka rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a watan Yuni. Sai dai hare-hare daga ɓangarorin biyu sun ci gaba da faruwa duk da hakan.

A makon da ya gabata, Pentagon ta sake duba alƙaluman waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata a yaƙin, inda ta sauya sunayen mutum huɗu da suka mutu daga jerin "Operation Epic Fury" zuwa jerin waɗanda suka mutu a ayyukan soji a ƙasashen waje na "Foreign Operations".

Adadin waɗanda suka mutu

Bisa ga bayanan da Ma'aikatar Pentagon ta taskace, adadin waɗanda suka mutu sakamakon farmakin na fushi ko kuma "Operation Epic Fury", ya kai mutum 18 zuwa ranar Talata, yayin da adadin waɗanda suka jikkata ya kai 482.

Daga baya an cire sunayen mutum huɗu daga cikin jerin waɗanda suka mutu, kuma a ranar Alhamis an rage adadin mace-macen daga 18 zuwa 14.

Yanzu sunayen waɗannan sojoji huɗu da suka mutu suna cikin sashen ayyukan soji a ƙasashen waje, wanda aka ce yana tattara bayanan asarar rayuka da aka samu har zuwa ranar 7 ga Yulin 2026. Su kaɗai ne mutanen da aka bayyana sun mutu a wannan sashe.

Sauye-sauyen da aka yi a bayanan waɗanda suka jikkata da waɗanda suka mutu ba tare da wani bayani a hukumance ba sun fuskanci suka daga masu sa ido, waɗanda ke cewa hakan na raunana gaskiya da fayyacewa wajen fitar da bayanan asarar rayuka da aka yi a yaƙin.

"Da alama gwamnatin na fuskantar matsala wajen faɗin gaskiya kan abin da ke faruwa, ba wai game da asarar rayuka kaɗai ba, har ma da yaƙin gaba ɗaya," in ji Janar Ben Hodges, wanda ya jagoranci dakarun Amurka a Turai lokacin da Trump ya fara hawa mulki.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, ɗan majalisar wakilai daga jam'iyyar Republican, Thomas Massie, wanda ya saba sukar Trump, ya bayyana raba bayanan yaƙin zuwa sassa daban-daban a matsayin wata "dabara mai wuyar fahimta."

BBC ta tuntuɓi Ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon domin samun martani kan lamarin.

A wani bayani da ya fitar a shafin X, kakakin Pentagon Sean Parnell ya bayyana sauyin alkaluman a matsayin "matsalar bayanai ta wucin gadi."

Sanarwar ta ce, "Ana ci gaba da magance waɗannan cikas na bayanai tare da haɗin gwiwar rassa daban-daban na rundunar sojin Amurka."

A wani saƙo da ya wallafa a shafin Truth Social ranar 21 ga Yuli, Trump ya ce "Yaƙin Sojin Amurka da Iran" ya yi sanadin mutuwar mutane 18.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa sashen sojojin Amurka da ke yaƙi a ƙasashen waje ya fara bayyana a shafin yanar gizon Pentagon ne a ranar Lahadi.

Sashen ya ƙunshi sunayen sojojin Amurka huɗu da suka mutu kwanan nan, sannan ya nuna cewa mutum 207 suka jikkata. Sai dai ba a bayyana ko dukkan su 207 sun samu raunukan ne a rikicin da ya shafi Iran da Iraki ba.

Sauya rukunin sunayen waɗanda suka mutu ya yi kama da yana da alaƙa da sojojin Amurka huɗu da suka mutu a watan Yuli, bayan yarjejeniyar wucin gadi da Trump ya sanya hannu a kai a watan da ya gabata ta fara rugujewa, kuma bayan shugaban ya bayyana cewa tsagaita wutar da Iran ya "ƙare."

Sojojin Amurka uku sun mutu bayan makaman roka na Iran sun kai hari wani sansanin soji a Jordan ranar 17 ga Yuli, yayin da wani soja ɗaya ya mutu a Iraki lokacin da ake gudanar da sarrafa fashewar wani jirgin sama maras matuƙi na Iran.

Tun daga tsakiyar watan Yuli, Amurka ta ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin sojin Iran, yayin da dakarun Iran ke kai hare-hare kan sansanonin Amurka a ƙasashen maƙwabta na tsawon dare 13 a jere.

Daga nan kuma, tun daga ranar Juma'a, an samu ɗan dakatawa inda babu ɓangaren da ya kai hari. Sai dai a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, hare-haren sun sake komawa.