Akwai rashin tabbas game da makomar Henderson a Ajax, Liverpool na zawarcin Amoura

Henderson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jordan Henderson
An wallafa

Akwai rashin tabas game da makomar dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson mai shekara 33 a Ajax bayan da Kungiyar ta kasar Netherlands ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasanni ta biyu a jere. (Athletic - subscription required)

Rahotanin da ke cewa dan wasan tsakiya na Newcastle Bruno Guimaraes dan shekara 26 zai koma taka leda a Paris Saint-Germain a wannan bazara ba dai- dai bane kuma bangaren kungiyar ta Faransa ba su nuna alamun su na son su dauki dan kasar Brazil ba. (Mail)

Kocin Netherlands Arne Slot na shirin tarewa a gidan Jurgen Klopp da ke Formby idan ya maye gurbin ba Jamushen a matsayin kocin Liverpool. (Mirror)

Watakila Liverpool ta kara inganta tawagarta ta hanyar daukar dan wasan gaba na kasar Algeria Mohammed Amoura mai shekara 24 daga Union Saint-Giloise. (TEAMtalk)

Bayern Munich ta fara tattaunawa da tsohon kocinta Hansi Flick game da komawarsa kungiyar a matsayin kociyanta domin maye gurbinThomas Tuchel. (Sky Germany)

Dan wasan mai kai hari na Faransa Kylian Mbappe, 25, zai kasance dan wasan da aka fi biya a Real Madrid idan ya rattaba hannu kan kwantaraginsa da kungiyar bayan ficewarsa daga Paris Saint-Germain. (RMCsport)

Tafiyar Mbappe za ta sa PSG ta samu raran kudi na yuro miliyan 220 duk da cewa dan wasan mai kai hari ya barte ne a kyauta. (Sky Sports)

Ana samun ci gaba a sabuwar tattaunawar da ake yi tsakanin Barcelona da dan wasan tsakiyarta dan kasar Sfaniya Marc Casado dan shekara 20 tun watan Afrilun daya gabata . (Fabrizio Romano)

Barca na fuskantar adawa daga Arsenal da Juventus wajan cimma matsaya da dan wasan tsakiya na Real Sociedad da Sfaniya Martin Zubimendi mai shekara 25. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Dan wasa mai tsaron bayan Scotland Kieran Tierney mai shekara 26, ya ce ga dukan alamu wasansa a Arsenal ya zo karshe bayan ya shafe wannan kaka ya na tamaula a Real Sociedad a matsayin dan wasan da aka bada shi aro. (Athletic - subscription required)