Hanyar da za ku bi idan kuna son daina shan taba sigari

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Michelle Roberts
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Tifaftiraha caafimaadka dhijitaalka ah
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 2
Wani sabon bincike ya nuna cewa masu shan sigari da ke son dainawa suna da damar yin hakan idan suna amfani da wata na'urar shan sigari ta laturoni da aka fi sani da vape, a turance.
Wannan bincike ne da wata ƙungiyar ƙwararru ta duniya ta gudanar, inda ta gano cewa sigarin laturoni (e-cigarettes) ita ce hanya mafi tasiri a shirye-shiryen tallafa wa mutanen da ke son daina shan sigari.
Binciken ya kuma goyi bayan ra'ayin cewa sigari ta gargajiya ta fi sigarin laturoni illa ga lafiya.
Ƙungiyar Cochrane ta yi nazarin manyan bincike guda 80 da suka haɗa kusan mutane 30,000, inda ta gano cewa vape mai nicotine ya fi hanyoyin gargajiya na daina shan sigari tasiri da kuma shirye-shiryen dainawa shan sigarin.
Binciken ya nuna cewa amfani da vape mai nicotine ya ƙara yiwuwar samun nasarar daina shan sigari da kusan kashi 60 cikin ɗari.
Wannan na nufin adadin mutanen da suka samu nasarar dainawa ya tashi daga kusan mutum shida cikin 100 zuwa kusan mutum 10 cikin 100.
Bugu da ƙari, binciken ya nuna cewa vape mai nicotine na iya kasancewa ya fi tasiri fiye da cytisine, wani sabon maganin ƙwaya da ake amfani da shi wajen taimaka wa mutane su daina shan sigari, wanda Hukumar Kula da Lafiya ta Birtaniya (NHS) ta fara samarwa ga jama'a a faɗin ƙasar.
Sai dai masu binciken sun ce ana buƙatar ƙarin nazari domin tabbatar da wannan.
Haɗarin shan taba sigari

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana sun ce amfani da sigarin lantarki (vaping), duk da cewa ba shi da cikakkiyar kariya daga haɗari, ya fi shan sigari na gargajiya saukin illa.
A Birtaniya, bisa ƙididdiga, adadin mutanen da shekarunsu suka kai 16 zuwa sama da ke amfani da sigarin laturoni (vaping ko e-cigarettes) yanzu ya zarce na masu shan sigari na gargajiya.
Kimanin mutum miliyan 5.3, wato kashi 10 cikin 100 na manya, sun ce suna shan sigari, yayin da kusan mutum miliyan 5.4 ke amfani da sigarin lantarki a kullum ko kuma lokaci-lokaci.
Binciken bai haɗa da sigarin lantarki marasa tsari ko marasa izini ba, waɗanda kan iya ƙunsar haramtattun ƙwayoyi kamar Spice ko THC.
Ƙungiyar agaji ta Action on Smoking and Health ta ce kusan mutum biyu cikin kowane mutum uku da suka daɗe suna shan sigari za su mutu sakamakon wata cuta da ke da alaƙa da taba sigari.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), shan sigari shi ne babban sanadin cututtuka da mutuwa da za a iya kaucewa, inda yake kashe fiye da mutum miliyan bakwai a kowace shekara.
Daina shan sigari na rage haɗarin kamuwa da munanan cututtuka kamar cututtukan zuciya, kansar huhu da kuma bugun jini (stroke).
Kusan dukkanin ayyukan NHS na yankuna da ke taimaka wa mutane daina shan sigari suna ba da sigarin laturoni (vapes) ko wasu nau'o'in tallafi domin taimaka musu daina shan sigari.










