Arsenal na son Kroupi, United na harin ƴan wasan Dortmund uku

Asalin hoton, Getty Image
Arsenal na son ɗaukar ɗan wasan Bournemouth Eli Junior Kroupi a watan Janairu, sai dai suna fuskantar hammayya daga Bayern Munich da Paris St-Germain da ke son ɗan wasan. (Mirror)
Ɗan wasan Juventus Kenan Yildiz, na cikin ƴan wasan da Arsenal ke son ɗauka sai dai Mikel Arteta yamayar da hankalinsa kan ƙara ƙarfafa yan wasan gaban kungiyar. (Mirror)
Manchester United na zawarcin ɗan wasan Borussia Dortmund Jobe Bellingham, da Felix Nmecha, 26, da mai tsaron bayan Swedin Daniel Svensson. (Teamtalk)
Mai tsaron ragar Brighton Bart Verbruggen, zai iya samun wata babbar dama ta komawa Real Madrid. (Football Insider)
Brighton na sa ido kan ɗan wasan Estoril Jordan Arnolin, duk da cewar ɗan wasan na jan hankalin Barcelona. (Record via Sport Witness)
Sunderland za ta baiwa zegis le Bris kuɗaɗe wajen ganin ya siyo ƴan wasa a kakar siyen ƴan wasa a watan Janairu. (The I - subscription required)
Mai horar da ƴan wasan Nottingham Forest Oliver Glasnerna da ke fuskantar matsin lamba, na samun goyan bayan yan wasan bayan ganawar da ya yi da su, a filin wasa da atisayensu. (Telegraph - subscription required)
Ƙungiyoyin da ke buga gasa Firimiya na bibiyar ɗan wasan Celta Vigo Javi Rodriguez. (Teamtalk)
Atletico Madrid na son ɗan wasan Almeria Stefan Dzodic, domin ƙara inganta ƙungiyar a kaka mai zuwa. (Marca - in Spanish)
























