Van Dijk na iya barin Liverpool, Fulham na son Summervill

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na son siyar da Virgil van Dijk cikin ƴan wasa da za ta siyar a wannan kaka, bayan yanke hukucin kan sabunta masa kwantaraginsa a shekarar da ta gabata, wanda hakan bai yi wa wasu daga cikin ƴanƙungiyar ke yin dana sani kan haka. (Teamtalk)
Fulham ta bi sahun ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan West Ham Crysencio Summerville, yayin da Chelsea da Manchester United su ma sukanuna sha'awarsu na ɗaukarsa. (Guardian)
Wakilin ɗan wasan Chelsea da Ingila Trevoh Chalobahya gana da takwarorinsa na Inter Milan kan yiwuwar komawar ɗan wasan Italiya, yayin da Como itama ke harin ɗan wasan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Barcelona bata da niyar siyen ɗan wasan Ingila da Bayern Munich Harry Kane. (Sport - in Spanish)
Ɗan wasan Manchester City, Mattay Warhurst na ci gaba da jan hankalin ƙungiyoyi daban daban, ciki har da Stockport County, da Northampton Town, da Swindon Town.(Mail)
Ana ci gaba da mahawara tsakanin Arsenal da Aston Villa kan ɗaukar ɗan wasan Ingila Morgan Rogers, inda dukkan ƙungiyoyin suka ɗan bambanta da juna wajen taya ɗan wasan. (Football Insider)
Leeds sun shiga gaban Juventus a zawarcin mai tsaron ragar Parma Zion Suzuki, kan fam Miliyan 25 kwatankwacin euro miliyan 30. (Sport Italia via Football Italia)
Ɗan wasan Real Madrid da Faransa Aurelien Tchouameni da ɗan wasan Bournemouth Alex Scott na cikin ƴan wasan da Manchester United da ta baiwa mahimammanci a cefa nen ƴan wasan da za ta yi. (Sky Sports)
Mai tsaron ragar Everton Mark Travers, na cikin waɗan Coventry City ke hari. (Mail)
Alamu sun nuna cewar ɗan wasan Egypt Mohamamd Salah na iya komawa Saundiya, idan ya bar Liverpool.(Mirror)
Coventry City na cikin ƙungiyoyin da ke son dauko dan wasan Juventus da Belgium Lois Openda. (Gazzetta dello Sport - in Italian)













