Manyan ƙungiyoyin Firimiya na son Scott, Arsenal za ta siyar da Trossard

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal, da Manchester United, da Manchester City, da Chelsea na harin ɗan wasan Bournemouth Alex Scott. (Talksport)
Arsenal ta amince ya siyar da ɗan wasanBelgium Leandro Trossard, sai dai, Besiktas ta sanya masa farashin euro 20 kwatankwacin fam miliyan 17. (Athletic - subscription required)
Ɗan wasan Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, na cikin ƴan wasan da Real Madrid ke son siye, domin kara inganta tsakiyar ƙungiyar. (Fichajes - in Spanish)
Manchester City ta sanar da masu zawarcin ɗan wasan ta Ruben Dias, ciki har da Real Madrid, ba zata siyar da ɗan wasa ba a wannan kaka. (Teamtalk)
Como na shirye shiryen taya ɗan wasan Chelsea da Ingila Trevoh Chalobah kan fam miliyan 30. (Sky Sports)
Roma a shirye ta ce wajebn hanzarta ciniki ɗan wasan Marseille Mason Greenwood kan euro miliyan 45, dai dai da fam miliyan 38.5. (Corriere dello Sport - in Italian)
Paris St-Germain na da masaniyar iya samun tayi mai cike da tarihi kan ɗan wasan AjantinaJulian Alvarez daga Atletico Madrid. (Fichajes - in Spanish)
Atletico Madrid na shirye-shirye sabunta taya ɗan wasan Sporting Morten Hjulmand, bayan da suka ƙi amincewa da tayin ɗan wasan kan euro miliyan 35 kwatankwacin fam miliyan 30. (A Bola - in Portuguese)
West Ham, na son ɗan wasan Everton da Ingilawight McNeil, don komawa ƙungiyar a wannan kaka. (Sky Sports)
Tsohon ɗan wasan Netherlands Daley Blind, na dab sake komawa Ajax, bayan ya bar Girona da ke Sipaniya. (Algemeen Dagblad - in Dutch)











