Hanyoyin da doka ta haramta wa ɗan takara bi don samun kuɗin kamfe

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Dokokin Najeriya sun tanadi ƙa'idoji kan yadda ɗan takara zai tara kuɗin yaƙin neman zaɓensa, adadin da zai iya karɓa daga masu ba da gudummawa, da kuma iyakar kuɗin da zai kashe wajen kamfen ɗin.
Waɗannan tanade-tanade an yi su ne domin tabbatar da adalci tsakanin ƴan takara, hana amfani da kudi wajen sauya ra'ayin masu kaɗa ƙuri'a, da kuma rage tasirin amfani da dukiyar gwamnati wajen siyasa.
Sai dai kusan duk lokacin da babban zaɓen ƙasar ya ƙarato, ana yawan samun zarge-zargen kan sayen ƙuri'a, amfani da kayan gwamnati wajen kamfen, da kuma zargin kashe kuɗaɗe fiye da abin da doka ta amince da shi.
Hukumar zaɓe ta ƙasar (INEC) tana da sashen da ke sanya ido kan yadda jam'iyyu da ƴan takara ke kashe kuɗi. Hukumar takan buƙaci jam'iyyu su gabatar da bayanan kuɗaɗen da suka shigo da kuma yadda aka kashe su bayan an kammala zaɓe.
To amma shin ana bin waɗannan dokokin? Waɗanne hanyoyi aka amince ɗan takara ya bi wajen samun kuɗin kamfe, kuma waɗanne hanyoyi ne aka haramta? Sannan mene ne hukuncin wanda ya karya waɗannan tanade-tanade?
Me doka ta ce kan kuɗin da ɗantakara zai kashe a kamfe?
Ɗaya daga cikin muhimman tanade-tanaden dokar zaɓen Najeriya shi ne kayyade adadin kuɗin da kowane ɗan takara zai iya kashewa wajen yaƙin neman zaɓe.
Masana harkokin zaɓe na cewa an tanadi wannan iyaka ne domin hana siyasa zama ta masu kuɗi kaɗai, da kuma rage tasirin masu hannu da shuni ko wasu ƙungiyoyi da ka iya amfani da kuɗinsu wajen rinjayar sakamakon zaɓe.
A sabuwar dokar zaɓe ta 2026, sashe na 92 ya ƙara adadin kuɗin kamfe da ƴan takara za su iya kashewa, inda aka bayyana cewa an yi hakan ne saboda hauhawar farashin kaya da tsadar gudanar da kamfe idan aka kwatanta da shekarun baya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cewar shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, a lokacin da aka amince da dokar, Sanata Opeyemi Bamidele, dokar ta nunka adadin kuɗin ga ɗan takarar shugaban ƙasa zai iya kashewa daga naira biliyan biyar zuwa naira biliyan goma. Haka kuma an ƙara kuɗin ga sauran masu neman muƙaman siyasa.
Bisa tanadin Sashe na 92 na dokar:
Ɗan takarar shugaban ƙasa: ba zai kashe fiye da naira biliyan 10 ba.
Ɗan takarar gwamna: ba zai kashe fiye da naira biliyan 3 ba.
Ɗan takarar Sanata: ba zai kashe fiye da naira miliyan 500 ba.
Ɗan takarar Majalisar Wakilai: ba zai kashe fiye da naira miliyan 250 ba.
Ɗan takarar Majalisar Jiha: ba zai kashe fiye da naira miliyan 100 ba.
Sai dai masana shari'a sun bayyana cewa akwai bambanci tsakanin kuɗin da ɗan takara zai kashe da kuma kuɗin da yake da shi.
Barista Aminu AbdulRasheed, lauya a Najeriya, ya ce doka ba ta ce dole ne ɗan takara ya kashe wannan adadi ba idan ba shi da su, illa dai ta sanya iyakar da ba zai wuce ba.
"Misali, idan ɗan takarar shugaban ƙasa ya kashe naira biliyan huɗu kacal a kamfensa, bai karya doka ba. Amma idan ya kashe fiye da naira biliyan goma, zai iya fuskantar hukuncin da dokar ta tanada idan aka tabbatar da hakan," in ji shi.
Barista ya ce dokar ta ce da zarar an kammala zaɓe ƴan takara za su bayar da bayanin ƙididdigar abin da suka kashe.
Hanyoyin da aka amince dantakara ya karɓi gudummuwar kamfe
Dokar Najeriya ta tanadi hanyoyin da ake ganin sun dace dan takara ya karɓi gudummuwa domin yaƙin neman zaɓe
Masana shari'a sun ce manufar hakan ita ce bai wa ƴan takara damar samun tallafin gudanar da kamfen ba tare da buɗe ƙofa ga masu kuɗi ko wasu masu ruwa da tsaki da za su iya neman biyan bukata bayan an ci zaɓe ba.
Barista AbdulRasheed, ya shaida wa BBC cewa dokar ta amince ɗan takara ya karɓi gudummawar kuɗi daga magoya bayansa, mambobin jam'iyyarsa da kuma wasu ƙungiyoyi ko mutane da suka yanke shawarar tallafa masa bisa ƙa'ida.
"An amince magoya baya, mambobin jam'iyya da wasu ƙungiyoyi su bayar da gudummawa, haka kuma ɗan takara na iya kafa gidauniya ko kwamitin tara kuɗin kamfen domin gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓensa," in ji Barista.
"An yi hakan ne saboda ba a son ɗan takara ya zama kamar ya zuba jari a siyasa, ko kuma wasu mutane su riƙa juya shi bayan ya ci zaɓe saboda gudummawar da suka bayar.
Ya ƙara da cewa haka kuma ana son a hana masu kuɗi juya sakamakon zaɓe.
Nawa aka amince ɗantakara ya karɓa a matsayin gudummuwa?
Daya daga cikin tambayoyin da ake yawan yi shi ne ko dokar Najeriya ta sanya iyaka kan adadin kuɗin da ɗan takara zai iya karɓa a matsayin gudummawar kamfen?
Barista Aminu AbdulRasheed ya ce dokar ba ta ƙayyade adadin kuɗin da ɗan takara zai iya tarawa daga masu ba da gudummawa ba, "domin ba zai yiwu a sanya iyaka kan yawan mutanen da za su iya ba da gudummawa ba".
Sai dai ya bayyana cewa abin da doka ta fi mayar da hankali a kai shi ne adadin kuɗin da ɗan takara zai kashe wajen gudanar da yaƙin neman zaɓensa, ba wai adadin da zai tara ba.
Ya ce hakan na nufin ko da ɗan takara ya samu gudummawar da ta haura iyakar kuɗin da doka ta amince a kashe, bai halatta ya yi amfani da dukkan kuɗin wajen kamfe ba.
Hanyoyin da aka haramta wa ɗantakara ya samu kuɗin kamfe
Duk da cewa dokar Najeriya ta amince ƴan takara su tara kuɗaɗen kamfen daga halastattun hanyoyi, ta kuma haramta wasu hanyoyin tara kuɗi.
Barista Aminu AbdulRasheed ya ce duk wata gudummawa da ta samo asali daga haramtacciyar hanya ko ake zargin tana da alaƙa da cin hanci, almundahana ko wasu laifukan kuɗi, ba ta halatta ɗan takara ya karɓa ba.
"Idan kuɗin da za a ba ɗan takara sun fito ne daga wata haramtacciyar hanya, ko kuma ana zargin sun shafi cin hanci, badakala ko wasu laifukan kuɗi, bai kamata ɗan takara ya karɓe su ba," in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa dokar zaɓe ta haramta wa jam'iyyun siyasa da ƴan takara karɓar gudummawar kamfen daga ƙasashen waje ko wasu ƙungiyoyi na ƙetare.
Ya ƙara da cewa ba a yarda a yi amfani da kuɗaɗen gwamnati ko dukiyar al'umma wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe.
"Ba a yarda a yi amfani da wata hukuma ta gwamnati, ko kuɗaɗen gwamnati, ko wani abu mallakin al'umma domin hidimar siyasa ko yaƙin neman zaɓe ba," in ji Barista AbdulRasheed.
Wane hukunci za a yanke wa wanda ya saɓa dokar?
Dokar Zaɓen Najeriya ta tanadi hukunci ga duk wani ɗan takara ko jam'iyyar siyasa da suka karya ƙa'idojin da suka shafi kuɗaɗen kamfen.
Barista AbdulRasheed ya ce sashe na 89(1) na dokar zaɓe ya fayyace cewa duk wanda aka samu da laifin karya tanade-tanaden da suka shafi kuɗaɗen kamfe, da gangan ko cikin sani, zai fuskanci hukunci.
"Sashe na 89 sakin layi na ɗaya ya tanadi cewa duk wanda ya saɓa wa waɗannan ƙa'idoji da sani ko da gangan, kotu na iya hukunta shi da biyan tara da ta kai kashi ɗaya cikin ɗari na kuɗin da ya kashe," in ji shi.
Ya ce ban da tarar kuɗi, dokar ta kuma bai wa kotu damar yanke hukuncin ɗaurin kurkuku.
"Haka kuma, wanda aka samu da laifi na iya fuskantar ɗaurin kurkuku na aƙalla wata shida, amma hukuncin ba zai wuce watanni 12 ba."











