Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hukumomin gwamnati 5 da suka fi tasiri a tsarin zaɓen Najeriya
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Tsarin zaɓe shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyya a kowace ƙasa mai bin tsarin mulkin, da ake yi wa taken na jama'a, kuma don jama'a.
A Najeriya, gudanar da ingantaccen zaɓe ba aiki ne da ya rataya a wuyan hukuma guda ɗaya ba, domin akwai hukumomi da dama da ke haɗa ƙarfi da ƙarfe don tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana da adalci.
Waɗannan hukumomi suna taka muhimmiyar rawa tun daga shirye-shiryen zaɓe, da tsaro, da sa ido kan bin doka, har zuwa warware rikice-rikicen da ka iya tasowa bayan zaɓen.
Ga hukumomi biyar da suka fi tasiri a tsarin zaɓen Najeriya:
1. Hukumar INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ita ce ke jagorantar dukkan harkokin zaɓe a Najeriya.
An kafa ta ne domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci ba tare da katsalandan daga gwamnati ko wata jam'iyya ba.
Daga cikin manyan ayyukan INEC akwai rijistar masu zaɓe, da rajistar jam'iyyun siyasa, da tantance ƴan takara, da samar da kayan zaɓe da horas da ma'aikatan zaɓe.
Haka kuma ita ce ke tattarawa da bayyana sakamakon zaɓe daga matakin rumfa har zuwa matakin ƙasa.
A cikin shekarun da suka gabata, INEC ta rungumi amfani da fasahar zamani kamar BVAS, wato (Bimodal Voter Accreditation System) da kuma tsarin aika sakamakon zaɓe ta Internet.
Waɗannan matakai sun taimaka wajen rage maguɗi da ƙarfafa amincewar jama'a ga tsarin zaɓen da sakamakonsa.
2. Rundunar Ƴansanda
Rundunar Ƴan Sandan Najeriya ita ce babbar hukuma mai kula da tsaro a lokacin zaɓe.
Duk da kasancewar sauran hukumomin tsaro suna bayar da gudunmawa, ƴan sanda ne ke jagorantar ayyukan tabbatar da zaman lafiya a cibiyoyin zaɓe.
Kafin zaɓe, rundunar kan gudanar da tantance wuraren da ka iya fuskantar matsalolin tsaro domin ɗaukar matakan kariya.
A ranar zaɓe kuwa, jami'anta kan kasance a rumfunan zaɓe domin kare masu kaɗa ƙuri'a, da jami'an INEC da kuma kayan aikin zaɓe.
Bugu da ƙari, rundunar tana da alhakin kamawa da binciken mutanen da ake zargi da aikata laifukan zaɓe kamar sayen ƙuri'a, da tada zaune tsaye, da satar akwatunan zaɓe da kuma amfani da ƙarfin tuwo wajen hana jama'a yin zaɓe.
3. Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS)
Hukumar DSS tana taka muhimmiyar rawa wajen tattara bayanan sirri da gano barazanar da ka iya kawo cikas ga nasarar zaɓe.
Duk wata alama ta tashin hankali, da ta'addanci ko shirye-shiryen tayar da rikici kan kasance ƙarƙashin sa idon wannan hukuma.
A lokutan zaɓe kuwa, DSS kan yi aiki tare da INEC da sauran hukumomin tsaro domin gano wuraren da ake zargin za a iya samun matsaloli.
Bayanan da hukumomi ke tattarawa suna taimakawa wajen hana aukuwar abubuwan da za su iya jefa rayuka cikin haɗari ko kuma kawo cikas da sahihancin zaɓe.
Masana harkokin siyasa suna ganin cewa nasarar gudanar da zaɓe cikin lumana a wurare da dama na da alaƙa da aikin leƙen asiri da tattara bayanan sirri da DSS ke yi kafin ranar zaɓe.
4. Hukumar EFCC
EFCC ta zama muhimmiyar hukuma a zaɓen Najeriya saboda yaƙin da take yi da cin hanci da rashawa a harkokin siyasa.
Daya daga cikin matsalolin da suka daɗe suna addabar zaɓe a Najeriya shi ne sayen ƙuri'a da rabon kuɗi ga masu zaɓe.
Domin magance wannan matsala, EFCC kan tura jami'anta zuwa wuraren zaɓe domin sa ido kan mu'amalolin kuɗi masu alaƙa da zaɓe.
Haka kuma hukumar kan binciki zargin amfani da kuɗaɗen haram wajen yaƙin neman zaɓe ko tasiri kan sakamakon zaɓe.
Ayyukan EFCC sun taimaka wajen jawo hankalin ƴan siyasa da magoya bayansu cewa duk wanda aka kama da laifukan rashawa na zaɓe na iya fuskantar hukunci.
5. Kotunan ƙorafe-ƙorafen zaɓe
Babu dimokuraɗiyya mai ƙarfi idan babu hanyar neman adalci bayan zaɓe.
Wannan ne ya sa kotunan sauraron ƙorafin zaɓe suka kasance wani muhimmin ɓangare na tsarin zaɓen Najeriya.
Waɗannan kotuna suna sauraron ƙorafe-ƙorafen da 'yan takara, da jam'iyyun siyasa ko masu ruwa da tsaki ke gabatarwa idan suna zargin cewa an samu kura-kurai ko take doka yayin zaɓe.
A wasu lokuta, kotuna kan tabbatar da sakamakon zaɓe, yayin da a wasu lokuta kuma kan soke zaɓe ko umartar a sake gudanar da shi idan an tabbatar da cewa an karya doka.
Wannan iko na kotuna yana taimakawa wajen tabbatar da cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka.
Ƙarin wasu hukumomi da ke taka rawa
Baya ga waɗanda muka lasafto a sama, akwai kuma wasu hukumomin gwamnati da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar zaɓe a Najeriya.
A baya bayan nan rundunar sojin Najeriya na shiga a dama da ita a hidimar zaɓe, musamman a yankunan da ake fargabar rikici ko matsalar tsaro yayin zaɓe.
Haka kuma, Babban Bankin Najeriya (CBN) kan kasance wurin da ake adanawa da kuma kiyaye wasu muhimman kayan zaɓe kafin a rarraba su zuwa sassa daban-daban na ƙasar.
A gefe guda kuma, Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima ta (NYSC) na samar da dubban mambobinta a matsayin ma'aikatan wucin gadi da ke gudanar da ayyuka daban-daban a rumfunan zaɓe.
Haka nan, akwai wasu ƙungiyoyi da hukumomi da ba sa cikin hukumomin gudanar da zaɓe kai tsaye amma suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar zaɓe.
Misali, ƙungiyoyin sufuri irin su National Union of Road Transport Workers (NURTW) da sauran masu harkar sufuri sukan taimaka wajen jigilar kayan zaɓe da ma'aikatan INEC daga wani wuri zuwa wani, musamman a yankunan karkara da ke da wahalar isa.
Haka kuma, Kamfanin Sadarwa na Najeriya (NCC) tare da kamfanonin sadarwa suna taka rawa wajen tabbatar da sadarwa mai inganci, tsakanin jami'an zaɓe da cibiyoyin tattara sakamako.