Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 24/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa na haifar da sakamako mai kyau - Shettima

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce ƙasar ta tsallake wani muhimmin mataki a sauye-sauyen tattalin arzikinta, kuma yanzu tana kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.

    Bayanin na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar.

    Shettima ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako na zahiri, inda ya bayar da misali da ƙaruwar ajiyar kuɗin ƙasashen waje zuwa sama da dala biliyan 55, da ingantuwar kasuwar musayar kuɗaɗen waje, da kuma ƙaruwar tattalin arzikin ƙasar da kashi 4.45 cikin 100 a rubu’i na biyu na bana.

    Mataimakin Shugaban Najeriyar ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin wata ganawa da ’yan Najeriya mazauna Amurka a New York, a wai ɓangare na babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

    Ya shaida wa mahalarta taron cewa duk da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, gwamnatin Tinubu na aiki domin sake fasalin tattalin arzikin ƙasar, musamman a fannonin ilimi da lafiya da kimiyya da fasaha da kuma noma, tare da samar da yanayin da zai jawo masu zuba jari.

    Sanarwar ta ruwaito Shettima na cewa “Ku kwantar da hankalinku cewa duk da munanan labaran da kuke ji da gani a kafafen sada zumunta, ƙofar Najeriya a buɗe take domin kasuwanci. Mun tsallake wani muhimmin mataki, kuma muna kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.”

    Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da su taka rawar gani wajen ci gaban ƙasar, yana mai bayyana ilimi da ƙwarewa da basirar da suke da ita a matsayin muhimman kadarori ga yunƙurin Najeriya na sauya fasalin tattalin arzikinta.

  2. Isra'ila ta ce ta kashe wani jami'in Hamas

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun kashe Mohammed Abu Alwan, shugaban sashen kuɗi na Hamas, a wani hari da suka kai Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza ranar Laraba.

    Sanarwar rundunar sojin Isra'ila, IDF, ta ce Abu Alwan “ya taka rawa wajen tsara kasafin kuɗin dukkan rassan Hamas.”

    Rundunar Isra'ila ta kuma ce a ƙarƙashin jagorancinsa, an tura sama da shekel biliyan ɗaya, kwatankwacin kusan dala miliyan 330, domin ɗaukar nauyin ayyukan Hamas.

    A cewar IDF, Mohammed Abu Alwan ya kasance “muhimmin jigo ne a ci gaban Hamas da ikonta.”

  3. 'Hare-haren Pakistan sun kashe farar hula huɗu a Afghanistan'

    Afghanistan ta ce hare-haren sama da Pakistan ta kai wurare da dama a ƙasar sun kashe fararhula huɗu, tare da alƙawarin mayar da martanin da ya dace.

    Zargin na zuwa ne bayan da Pakistan ta ce ta kai hare-hare kan wasu wurare a Afghanistan da ake amfani da su wajen ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa da ke ƙetara iyakar ƙasashen biyu.

    Jami'an Pakistan sun ce sun kakkaɓo jirage marasa matuƙan, amma hukumomin Taliban sun musanta cewa su ne suka harba su.

    Mazauna Kandahar, inda babban jagoran Taliban yake, sun ce an kai hari a tsakiyar birnin.

    Taliban ta ce an kuma kai hare-hare a lardunan Paktia da Khost.

    Pakistan na zargin Taliban da bai wa mayaƙan da ke kai munanan hare-hare a arewacin Pakistan mafaka, zargin da Taliban ɗin ke musantawa.

  4. Ya kamata China da Amurka su zama abokan hulɗa ba na hamayya ba - Xi

    Xi Jinping: Ya kamata China da Amurka su zama abokan hulɗa maimakon abokan hamayya

    Shugaban China Xi Jinping ya yi kira ga ƙasarsa da Amurka su zama abokan hulɗa maimakon abokan hamayya, a kalaman da kafafen yaɗa labaran gwamnatin Chinan suka wallafa sa'o'i bayan isarsa Washington domin wata muhimmiyar ziyarar aiki.

    Mista Xi ya ce muradun ƙasashen biyu suna da alaƙa sosai, saboda haka ya kamata su ci gaba da haɗin gwiwa, su kuma yi gogayya bisa tanadin doka.

    Ana sa ran ziyarar Xi ta kwanaki uku, wadda Shugaba Donald Trump ke karɓar baƙuncinsa, za ta ƙunshi tattaunawa kan batutuwa masu sarƙaƙiya da suka haɗa da cinikayya da fasahar AI da Taiwan da kuma Iran.

    An kuma sanar da tsawaita wa'adin yarjejeniyar sassauta takaddamar cinikayya tsakanin ƙasashen biyu zuwa Janairu.

  5. Gwamnatin sojin Nijar ta cimma yarjejeniyar farfaɗo da aikin haƙar uranium

    Gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta cimma yarjejeniya da kamfanin haƙar ma’adanai na Madaouela don sake fara aikin haƙar uranium, wani sabon mataki mai muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a Yamai ranar Laraba, ana sa ran yarjejeniyar za ta ƙunshi biyan dala miliyan 10 da farko, tare da samar da ayyukan yi kusan 1,000.

    Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ne ya ruwaito yarjejeniyar.

    Wannan mataki ya yi daidai da manufofin gwamnatin mulkin sojan Nijar na ƙara wa gwamnati iko kan albarkatun ma'adinai na ƙasar, tare da sake duba yarjejeniyoyin haƙar ma'adinai da kamfanonin ƙasashen waje.

    Madaouela na daga cikin manyan wuraren da da arzikin uranium, inda aka kiyasta cewa yana ɗauke da kimanin tan 52,800 na uranium.

    Kamfani dillancin labarai na AFP ya ce ana farfaɗo da aikin ne bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar da aka yi a baya da kamfanin GoviEx na Canada.

    Wannan wani misali ne na yunƙurin mahukuntan Nijar na ƙara wa gwamnati iko da albarkatun ƙasar da kuma ƙarawa gwamnati kuɗaɗen shiga.

  6. Ministocin harkokin wajen Pakistan da Iran sun gana a New York

    Mataimakin Firaministan Pakistan kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Ishaq Dar, ya gana da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, a wani ɓangare na taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana a shafinta na X cewa ɓangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar ƙasashensu, tare da musayar ra'ayoyi kan abubuwan da ke faruwa a yankin da kuma duniya baki ɗaya.

    A cewar Pakistan, Mista Dar ya jaddada muhimmancin tattaunawa da diflomasiyya da kuma ci gaba da mu'amala domin ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

    Bangarorin biyu sun kuma amince su ci gaba da tuntuɓar juna.

    Pakistan na ɗaya daga cikin manyan masu shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka.

  7. Kifewar kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mata huɗu a Jigawa

    Wasu mata huɗu sun mutu bayan da kwale-kwale ɗauke da mutum takwas ya kife a tafki Dudduru da ke ƙaramar hukumar Dutse a jihar Jigawa.

    Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba.

    Daily Trust ta ruwaito Shugaban hukumar tsaro ta NSCDC a jihar ya tabbatar da lamarin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud ya fitar.

    A cewar sanarwar, kwale-kwalen yana ƙoƙarin kai fasinjojin takwas zuwa kasuwar Chai Chai Sabuwa daga ƙauyen Kwadige a lokacin da jirgin ya kife.

    Matan da suka mutu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito matasa ne da shekarunsu ke tsakanin 12 zuwa 13.

    Shugaban NSCDC a jihar ya ce tuni aka yi jana'izar mamatan kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

  8. Gagarumar fashewa ta afku a Kudancin Lebanon

    Wata gagarumar fashewa ta afku a birnin Khayyam da ke Kudancin Lebanon, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya bayyana.

    Lamarin ya kuma shafi wasu yankuna da ke maƙwabtaka da wajen.

    Rahotanni su ce cibiyar fashewar ta kasance a wani yanki mai tsawon kimanin mita 300.

    Kamfanin dillancin labaran ya sanar cewa ƙarfin fashewar ya kai ga garuruwan Marjayoun da Al-Qalia da ma wasu yankunan da ke kewaye da su.

    Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu ƙarin bayan ikan abin da ya haddasa fashewar.

  9. Alƙali ya soke matakin Trump na haramtawa kafofin yaɗa labarai shiga White House

    Alƙalin da ke sauraron ƙarar da wasu kafafen yaɗa labarai uku na Amurka da ke neman a mayar musu da damar shiga Fadar White House suka shigar, ya nuna shakku kan halaccin matakin gwamnatin Trump na hana su shiga.

    Kamfanonin yaɗa labaran CNN, da MS NOW da kuma Politico, sun ce haramcin ya saɓa wa 'yancin da kundin tsarin mulkin Amurka ya tanada a bangaren aikin jarida.

    Lauyan gwamnatin Trump, ya shaida wa kotun cewa an ɗauki matakin ne saboda dalilan tsaron ƙasa, amma kafafen yaɗa labaran sun musanta wannan hujjar.

    Alƙalin ya ce zai yanke hukunci nan ba da jimawa ba.

    Manyan kafafen yaɗa labarai na Amurka sun kaurace wa watsa shirye-shiryen abubuwan da ke faruwa a Fadar White House domin nuna goyon baya ga waɗannan kafafen yada labarai uku, ta hanyar janye wakilansu daga ƙungiyar 'yan jaridar da ke bibiyar harkokin fadar gwamnatin ta Amurka.

  10. Shugaba Xi ya isa Amurka don ganawa da Trump

    Shugaban ƙasar China Xi Jinping ya isa birnin Washington domin wata ziyarar ƙasa da ake sa ran za ta ƙara inganta dangantaka tsakanin manyan ƙasashen biyu mafi ƙarfi a duniya.

    Ana sa ran bambancin ra'ayin da ƙasashen biyu ke da shi a kan kirkirarriyar basira ta AI, za ta kasance cikin muhimman batutuwan da za su tattauna a kai da ma batun kasuwanci.

    Yayin da Mista Xi ya sauka a Amurka, Sakataren Baitul Malin Amurka ya sanar da cewa an tsawaita yarjejeniyar dakatar da takun-saƙar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu zuwa watan Janairu.

    Wakilin BBC ya ce an tsawaita yarjejeniyar dakatar da takun-saƙar kasuwanci tsakanin Amurka da China na wasu watanni.

    Sai dai har yanzu akwai muhimman batutuwa da dama da ƙasashen biyu ke buƙatar warwarewa kafin a iya ƙara tsawaita yarjejeniyar.

    Yarjejeniyar ta dakatar da kakaba wasu manyan harajin kwastam da Amurka ta shirya ɗorawa a kan kayayyakin China.

  11. Australiya ta soki OpenAI kan jinkirin sanar da kutse a shafin intanet na gwamnati

    Firaministan Australia Anthony Albanese, ya zargi kamfanin OpenAI da jinkirta sanar da hukumomin ƙasar cewa wani ɓangare na ƙirƙirarriyar basirarsa ya yi kutse cikin shafin intanet na harkokin lafiyar ƙasar.

    Mista Albaneze ya ce "ina so na bayyana rashin jin dadina a kan jinkirin da kamfanin ya yi wajen sanar da gwamnati abin da ya faru, wannan mataki sam ba mu ji daɗnsa ba kuma ba za mu lamunta ba a gaba.

    An ce kutsen, wanda ya faru a watan Yuni daya gabata, ya samu damar shiga wasu bayanan da ba a bayyana wa jama’a ba.

    Rahotanni sun ce wannan ne karo na farko da aka samu kutse daga kirkirarriyar basira ta AI.

    A martanin da ya mayar, kamfanin OpenAI ya ce bai gano aukuwar kutsen ba sai a watan Agusta, kuma ya buƙaci a bashi lokaci domin gudanar da bincike a kai.

  12. Buɗewa

    Masu bibiyar wannan shafi, barkan mu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Nabeela Mukhtar Uba.

    Ku kasance da mu, inda za mu kawo muku labarai masu ƙayatarwa game da Najeriya da ma ƙasashe maƙwabta, da kuma sauran sassan duniya.