Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da gaske ne INEC ba ta nuna son kai a aikinta?
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce hukumar zaɓen ƙasar, INEC ba ta nuna son kai ko goyon bayan wata jam'iyya a ayyukanta.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu jam'iyyun adawa da ƴan siyasa ke ci gaba da nuna damuwa kan yadda hukumar ke ɗaukar wasu matakai da suke zargin goyon baya ne ga APC.
A baya-bayan nan INEC na fuskantar zarge-zargen nuna son kai a ayyukanta, musamman wasu matakai da take ɗauka, waɗanda a wasu lokuta suke janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar.
A wasu lokutan ma an sha jin wasu ƙungiyoyin siyasa da addini na kira ga shugaban hukumar ya sauka daga muƙaminsa, sakamakon zarge-zargen da suke yi masa.
To sai dai Shugaba Tinubu ya ce INEC na gudanar da ayyukanta bisa doron doka.
" INEC ba ta nuna son kai, ba ta taɓa tsoratar da kowa ba, idan ƴan adawa na ƙorafin, watakila suna zargin kansu ne da kuma rashin shirin da suka yi'', in ji shi.
''Akwai masu neman ƙwace mulki daga hannuna, hakan ba laifi ba ne a siyasa. INEC ba ta ɗaukar ɓangare, kuma ba ta zalunci kowa ba. Idan ƴan adawa na ganin ba haka ba ne to daga su ne. Za mu ci gaba da siyasa, ni kuma zan yake su har ƙarshe'', in ji Shugaba Tinubu.
Su wane ne ke zargin INEC da son kai?
Jama'iyyun adawar ƙasar da ɗaiɗaikun ƴansiyasa da wasu ƙungiyoyin addini a Najeriya sun sha zargin INEC da nuna son kai a ayyukanta.
Mutum na baya-bayan nan da ya nuna irin wannan zargi shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, wanda ya buƙaci matasan ƙasar su tashi tsaye don kare dimokraɗiyya da kuma tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe a 2027.
Yayin wata hira da ta ja hankalin ƴanƙasar, Mista Obi, ya ce babu tabbacin shugaban INEC, Joash Amupitan zai gudanar da sahihin zaɓe, don haka dole ne ƴan ƙasar su tsaya tsayin daka don kwatarwa kansu ƴanci.
Peter Obi ya bayar da misalai kan irin abubuwan da suka faru a ƙasar musamman irin abubuwan da jam'iyyun hamayya ke fuskata dama irin matakan da shugaban INEC ɗin ke ɗauka wanda ya ce suna da ban tsoro.
A nasa ɓangare shi ma Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta ADC sun zargi hukumar ta INEC da nuna son kai da yunƙurin murƙushe jam'iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Ɗantakarar shugaban ƙasar na ADC ya yi waɗannan zarge-zarge ne dangane da yadda ake tafiyar da rikicin shugabanci a jam'iyyarsa ta ADC da kuma wasu matakai na hukumar ke ɗauka da suka shafi shirye-shiryen zaɓukan 2027.
Ita ma Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci a ƙasar ta sha yin zarge-zargen nuna bambancin addini daga shugaban hukumar zaɓen.
Shugaban Majalisar Dr Bashir Aliyu Umar ya ce majalisar na zargin shugaban INEC da nuna wa al'ummar musulmai bambanci a zaɓukan ƙasar da ke tafe.
"Mun kaɗa ƙuri'ar yanke ƙauna ga Shugaban INEC. Gwamnatin Tarayya ya kamata ta maye gurbinsa da wani Kiristan da zai iya haƙurin zama da abokan zamansa Musulmai da sauran mabiya addinai".
Da gaske INEC na nuna son kai?
Farfesa Abubakar Umar Kari mai sharhi kan al'amuran siyasar Najeriya ya ce bisa doron doka kamata ya yi hukumar INEC ta zama ƴar ba ruwanmu.
''Kamar yadda sunanta ya nuna ita mai zaman kanta ne, don haka bai kamata ta riƙa ɗaukar wasu matakai da ke janyo mata zargi ba'', in ji shi.
Farfesa Kari ya ce wasu daga cikin matakan da INEC ɗin ke ɗauka ne ke sa jam'iyyun hamayyar su riƙa zarginta da nuna son rai.
Masanin siyasar ya ce wasu matakan da INEC ke ɗauka da ke janyo cece-ku-ce ne ke haifar da waɗannan zarge-zargen.
Me jam'iyyun hamayya ke cewa?
Jam'iyyun hamayyar ƙasar sun ce kalaman yabon da Shugaba Tinubu ya yi wa INEC, alamu da ke nuna cewa hukumar na nuna bambancin.
Ibrahim Abdullahi babban babban sakatare a ofishin shugaban jam'iyyar PDP, ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki ya ce kalaman nasa ba su dace da gaskiya ba.
''Duk wanda ke bibiyar al'amuran siyasar ƙasar nan ya san irin matakan da INEC ke ɗauka suna nuna goyon bayan APC'', in ji shi.
Babban jami'in na PDP ya kuma ai ba ma hurumin shugaban ƙasar ba ne ya ce INEC ba ta nuna son kai.
''Ta yaya shugaban ƙasa zai koma yana kare hukumar INEC, ya bari ƴanƙasa da ƙungiyoyin fararen hula da jam'iyyun siyasa su faɗi haka, idan hakan ne amma ba shi shugaban ƙasa ba'', in ji shi.
Ibrahim Abdullahi ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da yin katsalandar a wasu hukumomin gwamnati masu zaman kansu.
Jami'in na PDP ya kuma bayar da misali da yadda INEC ke ɗaukar wasu matakai da ke nuna rashin goyon baya ga jam'iyyun hamayya.
''A kwanakin baya wata kotun tarayya ta yanke hukuncin soke rajistar wasu jam'iyyu biyar, nan da nan INEC ta ƙuduri aniyar zartar da hukuncin duk kuwa da cewa jam'iyyun sun ɗaukaka ƙara, har sai jiya da kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin kotun tarayyar'', in ji shi.
Ibrahim Abdullahi ya ƙara da cewa abin da ya kamata a lokacin shi ne INEC ta jira tun da jam'iyyun sun ɗaukaka ƙara, sai kotun ɗaukakar ƙarar ta yanke hukuncin, ba wai ta ce za ta aiwatar da hukuncin ba.
''A baya ma bayanai sun nuna cewa shi shugaban hukumar tsohon ɗan jam'iyyar APC ne, kuma bai taɓa fitowa ya musanta hakan ba'', in ji shi.
Ita kuwa jam'iyyar ADC cewa ta yi kalaman na Tinubu na ƙara tabbatar da zargin da suke yi wa INEC ɗin ne.
Faisal Kabir ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ya ce duk wanda yake Najeriya yana sane da halin da ƙasar ke ciki game da matakan da INEC ke ɗauka.
''A baya-bayan nan INEC ta fito da wani taƙaitaccen lokaci na tura sunayen ƴantakara''.
''Sannan a cikin ƙurarren lokaci INEC ta faɗa cewa duk jam'iyyar da ke son shiga zaɓen 2027, sai ta yi wa mambobinta rajista, kuma sai an saka lambar NIN a cikin rajistar'', in ji shi.
Faisal ya yi zargin cewa wannan mataki jam'iyyar APC ta jima da saninsa, amma jam'iyyun hamayya sai a ƙurarren lokaci aka sanar da su.
''Ai ita INEC ta koma kamar wata hukuma ce ƙarƙashin gwamnatin APC'', kamar yadda ya yi zargi.
Sai dai a lokuta da dama hukumar ta INEC ta sha musanta zarge-zargen da jam'iyyun hamayyar ke yi mata.
Me kalaman Tinubun ke nufi?
Farfesa Kari ya ce dama abin da ya kamata shugaban ƙasar ya yi kenan tun da jimawa.
''Dama an jima ana zarginsa da gwamnatinsa da maƙure hukumar zaɓen, don haka ya kamata ya fito ya nesanta kansa daga waɗannan zarge-zarge'', in ji shi.
Ya ce ko ba komai hakan zai nuna cewa zarge-zargen da ake yi masa na katsalandan a hukumar ba gaskiya ba ne.
Masanin siyasar ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa INEC suna da tushe, kuma dama an saba yi wa hukumar zarge-zargen tun da jimawa, wanda kuma ya ce an yi mata zarge-zargen ne kan yadda take gudanar da ayyukanta.
Ya ce babban abin da ke zarge-zargen shi ne hanyar da ake bi wajen zaɓen shugabannin hukumar.
''Ana ganin wanda shugaban ƙasar ke naɗawa ɗan jam'iyyarsa ne ko mai yin biyayya a gare shi'', in ji shi.