Yadda ake damfarar mutane da sunan FRSC ana cire musu kuɗi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta gargaɗi al'umma, musamman masu ababen hawa, da su yi hattara da wasu saƙonnin wayar salula na ƙarya da ake turawa, waɗanda ke iƙirarin cewa sun fito ne daga hukumar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa wasu masu damfara na aika saƙonni ga jama'a suna sanar da su cewa sun aikata laifin tuƙi, don haka sai a buƙaci su danna wani link domin ganin cikakkun bayanai.

Hukumar ta ce waɗannan saƙonni na ƙarya ne kuma ba su da wata alaƙa da FRSC.

Hukumar ta ƙara bayyana cewa masu zamban sun ƙirƙiri wani shafin yanar gizo na bogi domin ya yi kama da na FRSC, da nufin yaudarar mutane da satar muhimman bayanansu.

Ɗaya daga cikin shafukan da ake yaɗawa shi ne frscgov.top/ng, wanda hukumar ta tabbatar ba nata ba ne, inda ta nanata cewa sahihin shafinta shi ne www.frsc.gov.ng.

Yadda suke "damfara"

A wani saƙo da BBC ta gani na wata mata, wadda ta ce an tura mata saƙo, kamar yadda ta wallafa a shafin X a ƙarƙashin sanarwar hukumar kiyaye haɗura, ta bayyana yadda ta kaya tsakaninta da ƴan damfarar, inda ta ce ita dai ta yi rashin nasara domin ta faɗa ƙomarsu.

Ta ce a cikin makon ne jami'an hukumar suka tare ta a hanya, sannan suka ɗauki wasu bayan motarta.

A cewarta, wannan ya sa da ta ga saƙon, sai ta yi tunanin su ɗin ne suka tura mata saƙo domin biyan tarar laifin da take tunanin ta yi.

Sai dai ta ce a saƙon, an rubuta cewa ne za ta biya tarar naira 2,500 ne, wanda hakan ya sa da shiga, ta saka bayanan bankinta, aka tura mata lambobin OTP, ta tura musu domin cire kuɗin.

Amma maimakin a cire naira 2,500 da aka rubuta, kawai ta ga saƙon an cire kuɗi har naira 300,00.

Ita ma wata wadda ta ci karo da saƙon, amma ta tsallake rijiya ta baya, ta ce lamarin ya faru a daidai lokacin da take ƙoƙarin samun lasisin tuƙi.

"Dama ina ƙoƙarin samun sabon lasisin tuƙi. Ko da na gani, sai hankalina ya koma can. Amma sai na lura adireshin intanet babu .gov.ng ko kuma .com kamar yadda hukumomin gwamnati ke ɗauka. Wannan ya sa na shiga shakku, na ƙi shiga," in ji ta.

Bayan waɗannan mutanen guda biyu, BBC ta ga mutane da dama suna wallafa saƙon da aka tura musu a ƙarƙashin saƙon gargaɗi da hukumar ta wallafa a shafinta na X, suna bayyana an tura musu saƙon.

Abin da ya kamata

FRSC ta yi bayanin cewa masu zamban na amfani da dabarar gaggawa domin razanar da mutane, suna sanar da su cewa sun aikata wani laifin tuƙi tare da buƙatar su shiga wani link na yanar gizo domin duba bayanai.

A cewar hukumar, manufar wannan yaudara ita ce tattara bayanan sirri, bayanan banki, lambobin katin kudi da sauran bayanai masu muhimmanci daga hannun jama'a.

Saboda haka, hukumar ta gargaɗi mutane da kada su danna irin waɗannan bayanan saƙonnin ko kuma su bayar da bayanansu na sirri ga waɗanda ba su sani ba, sannan ta kuma shawarci duk wanda ya samu irin wannan saƙo da ya ajiye shaidar saƙon sannan ya kai rahoto ga hukumomin da suka dace.

FRSC ta buƙaci direbobi su riƙa tabbatar da duk wani zargin laifin hanya ta hanyoyin hukuma, ba ta hanyar saƙonnin ba, sannan ta tunatar da jama'a cewa tana da layin waya da ba a buƙatar katin waya domin kira wato lambar waya 122, da kuma shafinta na hukuma domin tabbatar da bayanai.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa amfani da sunanta da tambarinta da martabarta wajen damfarar jama'a yana aikata babban laifi, inda ta ce za ta haɗa kai da hukumomin tsaro da na yaƙi da laifukan intanet domin ganowa tare da hukunta waɗanda ke da hannu a wannan maƙarƙashiya.

A nasa ɓangaren, shugaban hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ya buƙaci a ƙara wayar da kan jama'a game da wannan sabon salo na damfara. Ya kuma yi kira ga direbobi da sauran ƴan Najeriya da su kasance masu lura a duk lokacin da suke amfani da intanet.