Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Amurka ke neman tilasta Iran ta yi alƙawarin daina kai hari a mashigar Hormuz
- Marubuci, Ana Faguy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Washington
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Amurka ta buƙaci Iran ta fito fili ta bayyana wa duniya cewa ta buɗe mashigar Hormuz kuma ta yi alƙawarin daina kai hari kan jiragen da ke wucewa ta mashigar, daga cikin sharuɗɗan tattaunawar Oman.
Kafafen yaɗa labarai a Amurka sun ruwaito wani jami'i da ba su ambaci sunansa ba na cewa a asirce, Tehran ta riga ta shaidawa masu bai wa shugaba Trump shawara cewa harbin da aka yi wa jiragen ruwa a Mashigar Hormuz sun faru ne bisa kuskure, duk da cewa a baya sun ɗora alhakin harin ga wasu ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Trump dukkan ɓangarorin sun amince su ci gaba da tattaunawa duk da musayar wutar da suka yi a makonnan a kan mashigar Hormuz, wani abu da fadar White House ke yi wa kallon saɓa yarjejeniyar tsagita wuta.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Aragchi ya ce ƙasar ta mutumta yarjejeniyar, kuma a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ya zargi Amurka da karya yarjejeniyar.
A watan Yuni Amurka da Iran suka sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, inda a ciki aka amince cewa Iran za ta baɗe mashigar Hormuz.
Wani babban jami'in gwamnatin Trump ya shaidawa kafar CBS ta Amurka cewa Tehran ta ce wasu ɓatagari ne ke neman kawo cikas ga tattaunawar da ke gudana ta hanyar kai hari kan jiragen dakon mai da ke wucewa ta Hormuz.
Ya ce: "Su da kansu [Iraniyawa] sun dawo kan teburin tattaunawa suna masu amsa cewa sun yi kuskure, a koma tattaunawa.''
Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar JD Vance da sakataren harkokin waje Marco Rubio da sirikin shugaba Trump ared Kushner da kuma wakilinsa a gabas ta tsakiya Steve Witkoff za su jagoranci ganawar.
Shi ma Araqchi zai halarci zaman.
Kafafen yaɗa labaran Amurka da dama sun ce a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma'a, jami'in gwamnatin Amurkan ya ce sun aikewa shugabannin Iran saƙo ta hannun masu shiga tsakani suna neman Tehran ta fitar da sanarwa kowa ya gani cewa ta buɗe mashigar kuma ta daina kai wa jirage hari.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters "Ko dai su fitar da sanarwa ko kuma tattaunawar ta tashi babu biyan buƙata,''
Fadar White House tana kuma neman Iran ta fito fili ta amsa cewa ta tafka kuskure a hare-haren da ta kai wa jiragen ruwan.
A halin da ake ciki dai wata tawaga daga Qatar ta tashi zuwa Iran a ranar Juma'a domin tattauna yadda za a kwantar da fargabar da ake ciki da kuma sauƙaƙe hanyar wucewa ta mashigar Hormuz.
Shugaba Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Truth Social a ranar Juma'a cewa: "Jamhuriyar Musulumci ta Iran ta buƙaci mu ci gaba da tattaunawa.''
"Mun amince da hakan, amma Amurka ta shaida masu cewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta ƙare!''
A ranar Asabar da safe, Trump ya yi martani ga rahotannin da ke cewa Iran na shirin kashe shi.
Ya wallafa a Truth Social, cewa rundunar sojin Amurka za ta "tarwatsa duk wani yanki na Iran'' idan har ƙasar ta kashe shi.
A makon nan jaridar Wall Street Journal da sauran kafafen yaɗa labaran Amurka sun bayar da rahoton cewa Isra'ila ta aikewa Washington bayanan sirri da ke cewa Iran ta tsara yadda za ta kashe shugaban Amurka.
An kuma riƙa yin kiran a kashe shugaba Trump a wajen janaizar Ayatollah Ali Khamenei.
Khamenei, wanda aka yi janaizar shi a makon nan, ya rasu ne a sakamakon harin da Amurka da Isra'ila suka ka Tehran a ranar 28 ga watan Faburairu, ranar farko ta yaƙin.
A ranar Asabar, jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei ya fitar da wani saƙo yana cewa dole a ɗauki ramuwa kan kisan mahaifinsa.
Daga cikin yarjejeniyar zaman lafiyan, Iran da Oman za su tattauna da kuma tsara yadda gwamnati a Tehran da kuma kamfanonin jiragen ruwa za su amince da tsarin wucewa ta mashigar Hormuz.
A lokacin yaƙin Iran ta gwada ƙarfin ikon da take da shi kan mashigar, ta kuma kafa wata runduna ta sintiri, wadda ta ce za ta sanya ido kan ayyukan da ke gudana a mashigar Mormuz.
Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya ruwaito cewa aƙarƙashin sabuwar yarjejeniyar da za a ƙulla, mashigar Hormuz za ta zamo a ƙarƙashin ikon Iran da Oman, kuma za a sanya haraji ga jiragen ruwan da ke wucewa ta mashigar.