Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka binne tsohon jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei
Kafafen yaɗa labaran gwamnati a Iran sun ce an binne jagoran addini na ƙasar da aka kashe, Ayatollah Ali Khamenei, a hubbaren Imam Reza da ke Mashhad, wuri mafi tsarki a Iran, bayan taron jana'iza da ya jawo dubban mutane.
An gudanar da jana'izar a Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran bayan mako guda na jerin gwanon jana'iza da tarukan alhini da kuma zaman makoki, a daidai lokacin da rikici ya sake ɓarkewa tsakanin Iran da Amurka bayan wani lokaci na tsagaita wuta a yaƙin da ya shafe wata huɗu ana yi.
An kashe Khamenei ne a hare-haren farko da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a ranar 28 ga Fabarairu.
Daga baya Amurka da Iran sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a watan da ya gabata.
A ranar Alhamis an yi tafiya da gawar Khamenei cikin mota a hankali ta titunan Mashhad da suka cika da jama'a, zuwa haramin Imam Reza mai gubba da hasumiyoyi na zinariya, yayin da manyan malamai sanye da farin rawani ke tafiya a gefensa.
Masu makoki sanye da baƙaƙen kaya sun bi bayan gawar, suna daga tutocin Iran da hotunan marigayin da kuma allunan da ke ɗauke da taken juyin juya hali.
Jana'izar ta kasance a ƙarshen mako guda na bukukuwan makoki a Iran da Iraki, inda shugabannin addinin Iran din suka yi kira ga jama'a su halarta da yawa domin nuna ƙarfi da kuma kishin akidar tsarin mulkinsu.
A lokacin jana'izar ba a ga dan marigayin ba Mojtaba Khamenei wanda wani taron malamai ya ayyana shi a matsayin sabon Jagora Mafi Girma a farkon watan Maris, mako guda bayan mutuwar mahaifinsa.
Tun bayan fara yaƙin ba a sake ganinsa a bainar jama'a ba. Duk da cewa ya fitar da rubutattun saƙonni, ba a wallafa hotonsa ko bidiyonsa ko kuma wani sautin muryarsa ba.
Rahotanni sun ce ya ji munanan raunuka a harin da ya kashe mahaifinsa, inda aka ce fuskarsa ta baci kuma gaɓoɓinsa sun ji mummunan rauni.
Majiyoyi masu kusanci da gwamnati a Tehran sun ce yana ci gaba da jinya kuma har yanzu bai samu cikakkiyar lafiya ba da zai iya fitowa bainar jama'a.
Haka kuma jami'an tsaro na ƙoƙarin rage bayyanarsa saboda fargabar yiwuwar sabbin hare-hare.
Yayin da jama'a suka taru a Mashhad suna jiran jana'izar Khamenei, an ji wasu suna rera taken neman ɗaukar fansa kan Shugaban Amurka Donald Trump saboda kashe Khamenei.
Masu makoki sun rika furta kalamai na neman ramuwar gayya, yayin da wasu ke ɗauke da alluna masu saƙonnin siyasa.
Harabar hubbaren ta cika da masu makoki yayin da rana ke faɗuwa, inda aka rika jin taken siyasa da kuma waƙoƙin makoki da ake watsawa ta manyan lasifika.
Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya ɗauki akwatin gawar Khamenei daga motar jana'iza domin kai shi zuwa wajen binne shi, saboda dimbin jama'ar da suka mamaye yankin.
Ɗansa na fari, Mostafa Khamenei, ne ya jagoranci sallar jana'izar, kafin wasu maza masu makoki su ɗauki akwatin gawar da aka kawata da launukan tutar Iran zuwa cikin hubbaren.
Hotunan bidiyo sun nuna mutane da dama suna riƙe da kyandir, suna miƙa hannayensu zuwa ga akwatin gawar tare da zubar da hawaye.
Imam Reza na daga cikin manyan mutanen da mabiya Shi'a ke girmamawa, kuma hubbarensa da ke Mashhad, garin da Khamenei ya fito, na daga cikin manyan wuraren aikin hajjin Shi'a.
Kafin a kai gawarsa Mashhad, an yi jerin gwanon jana'izar a Tehran da birnin Qom na Iran, da kuma biranen Najaf da Karbala na Iraki.
A kowane ɗayan waɗannan wurare, dubban mutane sun fita domin halartar jana'izar, tare da waƙoƙin makoki na Shi'a da taken juyin juya hali.