Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tarihin yadda aka assasa rundunar sojin Najeriya da Hausawa 18 a Legas
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Tarihin rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ya samo asali tun a shekarar 1863, lokacin da Laftanal Glover na rundunar sojin ruwa ta Birtaniya (Royal Navy) ya nemi taimakon ƴan ƙasar.
A lokacin ne baturen ya ɗauki wasu ƴan arewacin Najeriya mazauna Legas su 18, inda ya kafa musu rundunar da ya sanya wa suna "Glover Hausas."
Kamar bayanai daga shafin intanet na ma'aikatar tsaron Najeriya suka nun Glover, wanda a lokacin shi ne Gwamnan Legas, ya yi amfani da wannan ƙaramar runduna wajen kutsawa yankunan karkara a yankin da kuma kare hanyoyin kasuwancin Birtaniya.
Daga rundunar mutum 18, yanzu sojojin ƙasan Najeriya na cikin gwarazan sojojin da ake ji da su a duniya, musamman a ƙasashen Afirka inda suke taimakawa a lokuta da dama wajen kwantar da tarzoma a wasu ƙasashen.
Rundunar Hausawa zuwa rundunar Legas
A shekarar 1865, rundunar "Glover Hausas" ta zama cikakkiyar rundunar gwamnati, aka kuma sauya sunanta zuwa "Hausa Constabulary." wato rundunar sojin wucin-gadi ta Hausawa.
Da farko rundunar tana gudanar da ayyukan soja da na ƴansanda a ƙarƙashin jagorancin turawa mulkin mallaka ta Legas. Daga baya kuma aka sake sauya sunanta zuwa "Lagos Constabulary."
A shekarar 1901 ce aka haɗe ta a cikin rundunar sojin Afirka ta yamma wato West Africa Frontier Force (WAFF), inda aka sake sauya mata zuwa bataliyar Legas wato "Lagos Battalion."
Daga Birtaniya ta kuma haɗa da:
- Dakarun wucin-gadi na Royal Niger Company (RNC) Constabulary da aka kafa a Arewacin Najeriya a shekarar 1886.
- Oil Rivers Irregular Force, wadda aka kafa a shekarar 1891.
A shekarar 1889, Lord Frederick Lugard ya assasa rundunar da daga baya aka sani da West Africa Frontier Force (WAFF) a Jebba da ke Arewacin Najeriya.
Sabuwar rundunar ta ƙara ƙarfi ne bayan ta haɗa dakarun Royal Niger Company (RNC) Constabulary da ke Arewacin Najeriya.
A ƙarshen shekarar 1901, WAFF ta haɗa dukkan rundunonin tsaro da na soja da Birtaniya ke da su a yankunan mulkin mallakarta na Yammacin Afirka ƙarƙashin jagorancinta. Wannan ne ya tabbatar da sunanta na West Africa Frontier Force (WAFF).
Kafuwar WAFF ta haifar da haɗa dukkan rundunonin soja zuwa runduna guda a kowace ƙasa da Birtaniya ke mulka.
A Najeriya, wannan haɗewar ya haifar da ƙirƙirar:
- Rundunar arewacin Najeriya wato Northern Nigerian Regiment
- Runduar kudancin Najeriya wato Southern Nigerian Regiment
Daga baya an yi amfani da waɗannan rundunoni wajen yaƙe-yaƙen da Lord Lugard ya jagoranta tsakanin 1901 zuwa 1903 domin haɗa yankunan Najeriya ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniya.
Kafa rundunar Najeriya
Bayan haɗewar arewacin Najeriya da kudancin a shekarar 1914, an kuma haɗa rundunonin Northern Regiment da Southern Regiment, wanda ya haifar da kafuwar rundunar Nigerian Regiment ta ƙasa baki ɗaya.
Sabon tsarin ya kasance kamar haka:
A rundunar arewa akwai:
- Bataliya ta 1
- Bataliya ta 2
Rundunar kudu akwai:
- Bataliya ta 3
- Bataliya ta 4
Babbar rundunar da ke jagorantar yaƙi a yanzu wato Infantry ta samo asali ne daga rundunar Mounted Infantry ta Arewacin Najeriya, wato dakaru mahaya doki bayan yaƙin duniya na biyu.
Haka kuma tun a lokacin akwai rundunar kula da manyan makamai wato Artilerry, wadda a lokacin ake kira da Field Artillery.
Zuwan Sarauniya Elizabeth Najeriya
Tsakanin 28 ga Janairu zuwa 15 ga Fabrairun 1956 ne Sarauniya Elizabeth ta II ta kai ziyara Najeriya.
Saboda wannan ziyara, an sauya sunan rundunar sojin Najeriya wato Nigerian Regiment zuwa rundunar sarauniy wato Queen's Own Nigerian Regiment (QONR), waɗanda ake kira sojojin sarauniya.
A wannan shekarar ne kuma aka fara tsarin da ya ba kowace rundunar soja ta ƙasashen Yammacin Afirka 'yancin gudanar da harkokinta ba tare da dogaro da sauran rundunonin WAFF ba.
Saboda haka, rundunar Queen's Own Nigerian Regiment (QONR) ta koma rundunar Nigerian Military Force (NMF).
Miƙa undunar ga Najeriya
A ranar 1 ga Yunin 1958, majalisar ƙoli ta rundunar sojin Birtaniya da ke Landan ta miƙa ikon gudanar da rundunar Nigerian Military Force (NMF) ga gwamnatin Najeriya.
Wannan shi ne karo na farko da Najeriya ta fara samun cikakken iko kan rundunarta ta soja, ko da yake ƙasar ba ta samu ƴancin kai ba tukuna.
Lokacin da Najeriya ta samu ƴancin kai a shekarar 1960, an sauya sunan rundunar zuwa: Royal Nigerian Army (RNA)
Daga baya, lokacin da Najeriya ta zama Jamhuriya a shekarar 1963, an cire kalmar Royal, aka mayar da sunanta zuwa rundunar sojin ƙasan Najeriya wato Nigerian Army.
A wannan lokaci ne kuma rundunar ta yi manyan sauye-sauye, ciki har da:
- Sauya kayan sutturar soja daga na Royal West African Frontier Force (RWAFF) zuwa kore.
- Sauya tsarin muƙaman soja.
- Sauya alamomin runduna da kayan aikin soja domin nuna cikakken 'yancin kai da kasancewar rundunar mallakin Najeriya
Faɗaɗa zuwa sojin ruwa da na sama
Asalin Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya (Nigerian Navy) ya fara ne daga Marine Department da gwamnatin mulkin mallakar Birtaniya ta kafa a shekarar 1887. Wannan sashe yana gudanar da ayyukan soja da na farar hula, kuma daga cikinsa ne aka samar da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa (NPA) da hukumar kula da hanyoyin ruwa (NIWA), da rundunar sojin ruwa ta Najeriya.
A ranar 1 ga Yuni, 1956, aka kafa Naval Defence Force (NDF), wadda ta fara aiki da jiragen ruwa guda 11 da aka gada daga Marine Department. A 1 ga Mayun 1958, an sauya sunanta zuwa Royal Nigerian Navy (RNN).
Bayan Najeriya ta zama jamhuriya a shekarar 1963, an cire kalmar Royal, sannan Dokar Majalisa ta Lamba 21 ta 1964 ta kafa Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya a hukumance.
A ɗaya ɓangaren kuma, burin kafa rundunar sojin sama ta Najeriya (Nigerian Air Force – NAF) ya samo asali ne a shekarar 1961 bayan Najeriya ta shiga ayyukan tabbatar da zaman lafiya a Congo da Tanganyika.
A lokacin, jiragen saman ƙasashen waje ne ke jigilar sojojin Najeriya, abin da ya nuna muhimmancin samun rundunar sojin sama ta ƙasa.
A shekarar 1962, gwamnatin tarayya ta amince da kafa rundunar, sannan aka fara ɗaukar jami'an da za a horar a watan Yuni. A watan Afrilu 1964, aka kafa rundunar a hukumance ta hanyar dokar majalisa. Manufofinta sun haɗa da kare sararin samaniyar Najeriya, jigilar sojoji cikin sauri, tallafa wa rundunar ƙasa da ta ruwa, da kuma ɗaukaka martabar Najeriya a duniya.
Lokacin Yaƙin Basasar Najeriya (1967–1970), Rundunar Sojin Sama ta shiga yaƙi duk da kasancewarta sabuwa. Ta yi amfani da jiragen yaƙi irin su MiG-15 da MiG-17, waɗanda suka taimaka wajen ƙarfafa ayyukan soja. Bayan yaƙin, an sake tsara rundunar tare da sayen sabbin jiragen sama da inganta horo tsakanin 1981 da 1990.