Arsenal da Tottenham da Newcastle na sanya ido kan Tresoldi, Liverpool na son Jeltsch

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea da Manchester City da Arsenal da Tottenham da Newcastle duk suna sanya ido kan ɗan wasan matasan Jamus na ƙungiyar Club Brugge, Nicolo Tresoldi. (Teamtalk)
Sai dai Club Brugge ta ce ba za ta sayar da ɗan wasan mai shekara 22 a watan Janairu ba. (Het Nieuwsblad)
Liverpool da Barcelona da Real Madrid na daga cikin manyan ƙungiyoyin Turai da ke nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan baya na tsakiya ɗan ƙasar Jamus mai shekara 20, Finn Jeltsch, wanda ke buga wa Stuttgart wasa. (Sport)
Chelsea ta mayar da hankali kan ɗaukar Alex Scott daga Bournemouth, bayan da yunƙurin ɗaukar sa ya ci tura a lokacin bazara; ɗan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 23 yana kuma cikin jerin ƴan wasan da Liverpool ke son ɗauka. (Florian Plettenberg)
Manchester United ta yi shirin korar Michael Carrick a wannan makon, amma ta kasa cimma matsaya kan wanda zai maye gurbinsa.(The I)
Manchester United za ta biya Newcastle diyya ta kimanin fam miliyan 3 idan ta yanke shawarar naɗa Eddie Howe a matsayin wanda zai maye gurbin Carrick.(Guardian)
Brighton ba ta da wata fargaba game da yiwuar rasa ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Paraguay mai shekara 23, Diego Gomez, duk da cewa AC Milan da Atletico Madrid na nuna sha'awar ɗaukar sa. (Football Insider)
Pierre Sage na fuskantar matsin lamba mai tsanani, kuma ana iya korarsa daga aiki idan Crystal Palace ta yi rashin nasara a hannun Tottenham a ranar Asabar. (Guardian)
Liverpool za ta yi ƙoƙarin sayen ɗan wasan gefe na Valencia, David Otorbi, a watan Janairu, idan har ƙungiyar ta La Liga ta yanke shawarar amfani da damar da take da ita na ƙara kuɗin soke kwangilar ɗan wasan na Spain mai shekara 19 daga fam miliyan 30 zuwa fam miliyan 50. (Football Insider)
Juventus ta sanya ɗan wasan gaba na Monaco, Folarin Balogun—wanda ɗan ƙasar Amurka ne mai shekara 25—a matsayin babban burinta a watan Janairu; wanda a baya aka yi ƙoƙarin kai shi Everton a ranar ƙarshe ta kasuwar musayar ƴan wasa amma yarjejeniyar ta ci tura. (Tuttosport)

























