Arsenal da Man City da Man U na son Ndiaye, PSG za ta cefanar da Barcola

Iliman Ndiaye

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iliman Ndiaye
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Paris St-Germain za ta sayar da dan wasan Faransa Bradley Barcola, inda Arsenal da Liverpool na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan mai shekara 23. (L'Equipe, in French - subscription required), external

Brighton ta yi watsi da tayin fam miliyan 20 da Coventry City ta yi mata kan mai tsaron ragar Ingila Carl Rushworth mai shekara 24. (Sky Sports), external

Bayern Munich a shirye ta ke ta sha gaban Barcelona wajan daukar dan wasan Manchester United Marcus Rashford ,mai shekara 28. (Fichajes - in Spanish, external)

Arsenal ta bi sahun Manchester City da Manchester United wajan zawarcin dan wasan Everton da Senegal, Iliman Ndiaye mai shekara 26 (Mail - subscription required), external

Nottingham Forest ta yi wa dan wasan Arsenal Fabio Viera mai shekara 26 tayin fam miliyan 25 wanda aka bada shi aro ga Hamburg a kakar da ta gabata . (Football Insider, external), external

Haka kuma watakila Forest ta dauko dan wasan Inter Milan Davide Frattesi mai shekara 26 wanda ya ke son ya bar San Siro. (Football Italia, external), external

Atletico Madrid za ta maida hankali kan dan wasan Paris St-Germain Lee Kang-in, mai shekara 25, domin maye gurbin Antoine Griezmann da ya bar kungiyar. (Fichajes - in Spanish, external), external

Barcelona na sha'awar dan wasan Australia Lucas Herrington, mai shekara 18 wanda a halin yanzu yana taka leda a kungiyar Colorado Rapids ta Major League Soccer. (Goal, external), external

Watakila tsohon dan wasan Barcelona Robert Lewandowski, mai shekara 37, da tsohon dan wasan Bayern Munich Leon Goretzka, mai shekara 31, su koma kungiyar Chicago Fire ta MLS . (Yahoo Sports, external), external

Roberto Mancini zai sake rike mukamin kocin Italiya karo na biyu bayan ya bar kungyar Al -Sadd ta kasar Qatar. (Fabrizio Romano, external), external