BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Za mu fice daga yarjejeniyar tsagaita wuta idan Isra'ila ba ta daina kai hari Lebanon ba - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 8 ga watan Afrilun 2026.
KAI TSAYE, Barca ta sha mamaki a hannu Atletico, PSG ta nuna wa Liverpool fin ƙarfi
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Talata 7, zuwa Asabar 11 ga watan Afrilun 2026.
Manyan ƴansiyasar Amurka da suka buƙaci a tsige Trump saboda yaƙin Iran
Kiraye-kirayen tsige Trump ta hanyar amfani da sashe na 25 ya samu karɓuwa a tsakanin ƴan jam'iyyar Democrat waɗanda suka yi tir da kalaman na shugaban Amurka da cewa "ba su da kan gado" kuma "laifukan yaki" ne.
Me ya kamata ku sani kan babban taron jam'iyyun siyasa na Ƙasa
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya zayyana tanade-tanade masu yawa domin gudanar da tsarin shugabanci tun daga tafarkin ƙasa zuwa sama.
Shin nasara Trump ya samu ko faɗuwa bayan amincewa da tsagaita wuta a yaƙin Iran?
Akwai matuƙar mamaki mutum kamar Trump ya amince da waɗannan sharuɗɗan da Iran ta gabatar, amma alamu ne da ke nuna cewa za a iya cimma matsaya ta har abada a tattaunawar makonni biyun.
Sharuɗɗa 10 da ke cikin yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Amurka da Iran
Kafar yaɗa labaran Iran ta ce: "Trump ya sanar da tsagaita wuta ta tsawon mako biyu, inda ya amince da sharuɗɗan da Iran ta gindaya na dakatar da yaƙin saboda gudun zubewar ƙimarsa bayan barazanar da ya yi".
Atiku, Obi da Kwankwaso sun jagoranci zanga-zangar adawa da matakin INEC
Zanga-zangar ta fara ne daga Maitama Roundabout a Abuja, inda ta ƙare a hedikwatar INEC.
Ba za mu bari a ƙwace mana ADC ba - Nafi'u Gombe
Nafiu Bala Gombe ya ce har yanzu shi ne halattaccen shugaban jam'iyyar ta ADC, inda ya ce raina shekarunsa da aka yi, ya sa shi tashi tsaye wajen ganin ya ƙwatar wa kansa haƙki.
Ƙasashen Afirka 5 da Dangote zai riƙa sayar wa man fetur
A baya-bayan nan Matatar - wadda ta fi kowacce girma a Afirka - ta sayar wa wasu ƙasaahen Afirka biyar jiragen mai 12 da nauyinsu ya kai tan 456,000.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 9 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 8 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 8 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 8 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
Fernandez na son tafiya Madrid, Man Utd ta rasa damar samun Anderson
Danwasan tsakiya na Chelsea da Argentina Enzo Fernandez, na shirin miƙa buƙatarsa ta neman tafiya Real Madrid a bazara, yayin da ake ganin Man United ta rasa damar samun Elliot Anderson, na Ingila saboda ya fi son tafiya Man City daga Nottingham Forest.
Liverpool na harin Camavinga, Barca da Juventus na son Silva
Liverpool na harin dan wasan tsakiyar Real Madrid, Juventus na son daukar ɗan wasan Manchester United, yayin da ɗn wasan Manchester City ke ci gaba da samun ƙungiyoyin da ke zawarcin sa a Turai.
Lewandowski da wasu fitattun ƴan wasan da ba za su je Gasar Kofin Duniya ba
Gasar Kofin Duniyar ta kunshi ƙasashe 48, sai dai akwai fitattun ƴan wasa da suka kasa tsallakewa zuwa gasar.
United za ta siyar da Ugarte, Vinicius na son komawa Ingila
Manchester United na duba yi wuwar siyar ɗan wasan tsakiyar Uruguay, ya yin da ɗan wasan gaban Real Madirid ya nuna sha'awarsa na komawa ɗaya daga cikin ƙungiyaoyin da ke buga gasar Premier, yayin da Liverpool ke yunƙurin daukar dan wasan Al'ahli Marcus Leonardo.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Hanyoyin ruwa guda 8 masu muhimmanci a duniya
Waɗannan hanyoyin ruwan suna taka muhimmiyar rawa wajen haɗa tekuna da dama, kuma suna rage tazarar tafiya da kuma kashe kuɗi.
Me ya janyo musayar yawu tsakanin Kwankwaso da Nafi'u Bala?
Faɗi-in-faɗa ta kaure tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Nafi'u Bala wanda ake rigimar shugabancin jam'iyyar ADC da shi.
Mutum 2,360 aka kashe a Najeriya a wata ukun farkon 2026 - Rahoto
Cikin rahoton wata-wata da kamfanin ke fitarwa ya ce duk da matakan da jami'an tsaron ƙasar ke ɗauka har yanzu matsalar ba ta sauya ba.
Ko farin jinin Buhari zai yi tasiri a siyasar ɗansa?
Tun bayan saukar mahaifinsa daga mulki, ƴansiyasa da dama ke alaƙanta Yusuf Buhari da shiga siyasa, to sai dai ya riƙa noƙewa tare da nuna rashin muradin hakan. Tun bayan saukar mahaifinsa daga mulki, ƴansiyasa da dama ke alaƙanta Yusuf Buhari da shiga siyasa, to sai dai ya riƙa noƙewa tare da nuna rashin muradin hakan
Ƙasashe 10 da suka fi samar da man fetur a duniya
Yayin da ake ƙara nutsawa a cikin yaƙi tsakanin Amurka da Isra'ila da kuma Iran, ƙasashe masu samar da mai a duniya na ƙara zama wasu 'yan lele a idanun marasa man.
Amurka ba ta da niyyar amfani da nukiliya kan Iran - Fadar White House
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 7 ga watan Afrilun 2026.
Yaƙin Iran: Gaba ake ci ko baya?
Duniya ta sa ido tana jiran yadda za a samu mafita game da yakin Iran: ko dai a sasanta ko kuma lamarin ya kazance ganin wa’adin da shugaba Trump ya diba
Matakan da jam'iyyun adawar Najeriya ke shirin ɗauka gabanin 2027
''Duk wata hanya da za mu bi mu tabbatar cewa mun ƙwato wa kanmu 'yanci za mu bi ta, domin irin wannan bi-ta-da-ƙullin da ake yi ba zai taimaka wa dumukuradiyya ba. Gurgunta ta yake so ya yi. Ana so a tabbatar ba mu da murya gabaɗaya.''
Yadda fasa-ƙwaurin cinnaka ya zama sana'a mai maiƙo a duniya
An samu ƙaruwar wannan haramtacciyar kasuwa a Kenya a bara, lokacin da aka gano wasu cinnaku mata kusan 5,000 da ransu a wani gida a garin Naivasha, wanda ke kusa da wani kogi da masu yawon buɗe ido ke zuwa.
Ina ne mashigar Hormuz, kuma me ya sa take da muhimmanci?
Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.
Yadda sojojin Najeriya suka kashe ƴaƴan Ado Aleiro da ƴanbindiga 65
Bayanai sun ce ƴaƴan ƙasurgumin ɗanfashin dajin uku na daga cikin ɓarayin dajin da suka addabi yankin Tsafe.
Da gaske ne sha'awar ma'aurata na dakushewa?
Reeves mai shekaru 52 a yanzu ya ce rashin sha'awa ya zamar masa ƙalubale a alaƙarsa. "Mu kan shafe watanni 3 ko 4 a wasu lokutan ba tare da jima'i ba.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.































































