Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 28 ga watan Mayun 2026
Iran da Amurka sun amince da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta
Asalin hoton, Getty Images
Jami’an Amurka sun ce Amurka da Iran sun amince da shirin yarjejeniyar da za ta tsawaita tsagaita wutar da suka cimma da kwanaki 60.
Ana dai jiran amincewar shugaban Amurka Donald Trump, wanda majiyoyi suka ce ya ce yana son a ba shi lokaci domin nazartar yarjejeniyar da za ta sassauta matakin hana jiragen ruwa wucewa ta mashigar Hormuz.
Wannan na zuwa ne a yayin da aka ci gaba da faɗa tsakanin Amurka da Iran, wanda ke barazana ga yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma wadda a yanzu take tangal-tangal.
Tehran ba ta ce uffan ba kan rahotannin baya bayan nan.
Ba za mu sassauta wa ƴansiyasa masu son kawo rikici ba - Aliyu
Asalin hoton, Sokoto State Government
Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya buƙaci ƴan siyasa a jihar cewa kada su yi amfani da siyasar a matsayin makamin kawo ruɗani a jihar.
Najeriya na tunkarar babban zaɓen ƙasar na 2027, inda za a yi zaɓen shugaban ƙasa da gwamnoni da sanatoci da ƴan majalisar dokokin tarayya da na jihohi.
A wata ziyara da gwamnan ya kai fadar sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad na bikin sallar Idi, ya ce "wajibi ne a ririta zaman lafiyar da jihar ke samu a halin yanzu".
Sokoto na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
"Za mu hukunta duk wanda muka samu yana lalata kayan hukuma," in ji gwamnan a cikin saƙon nasa.
Netanyahu ya ba da umarnin sake ƙwace kashi 70% na yankin Gaza
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya bai wa sojojin ƙasar umurni su faɗaɗa mamayarsu a Zirin Gaza, wani abu da zai saɓa ƴarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Da yake jawabi a wani matsugunin Isra'ila da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, Mista Netanyahu ya ce dakarun IDF za su ƙwace ikon kaso saba'in na Gaza, saɓanin kashi hamsin da ke ƙarkashin ikon ta a lokacin da aka cimma tsagaita wuta a Oktoban bara.
Bidiyon da aka fitar ya nuna mutanen da ke wurin na ihun 'Kashi ɗari', sai dai Firaiministan ya ba su amsar cewa 'a yanzu za a fara da kashi 70 ne'.
Tun bayan da aka aiki da yarjejeniya da Amurka ta jagoranta, Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 900, inda ta ke zargin Hamas da saɓa sharuɗɗanta na ajiye makamansu.
Rasha ta gargaɗi Amurka da Iran kan sake ɓarkewar yaƙi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Vladimir Putin
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova ta yi kira ga Amurka da Iran su guje wa sake komawa fagen daga, a maimakon haka su ci gaba da bin hanyoyin neman sulhu ta lalata.
Zakharova ta ƙara da cewa a shirye Rasha take ta taimaka wajen karɓar makamashin yureniyum (uranium) ɗin da Iran ta inganta, sai dai ta ce Rashar ba za ta yi yunƙurin 'tilasta hakan ba."
Kuma ta bayyana cewa har yanzu Amurka ba ta riga ta amince da tayin ba, duk da cewa Rashar ta miƙa tayin ne a makonni da dama da suka gabata.
Atiku ya kai wa Amaechi ziyara bayan lashe zaɓen fitar da ɗan takarar ADC
Asalin hoton, X/Atiku Abubakar
Bayanan hoto, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi a ranar Alhamis
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar wanda ya lashe zaɓen fitar da ɗan takar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a ranar Laraba, ya kai ziyara ga abokin karawarsa tsohon ministan sufuri na ƙasar Rotimi Amaechi.
A lokacin sanar da sakamakon zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a ranar Laraba, shugaban jam'iyyar na ƙasa David Mark ya ce Atiku ne ya lashe zaɓen, inda ya samu ƙuri'a 1,846,370, inda ya kayar da mai biye masa Rotimi Amaechi da kuma wanda ya zo na uku Muhammed Hayatu-Deen.
Bayan sanar da sakamakon an yi ta raɗe-raɗin abin da zai biyo baya ganin cewa tun kafin a sanar da sakamakon ne sauran ƴan takarar suka nuna rashin gamsuwa da yadda ake tattara sakamakon.
Sai dai a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da yammacin yau Alhamis, Atiku ya ce: "A wannan rana na kai wa ɗan'uwana kuma abokin tafiya, tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ziyara a gidansa da ke Abuja.
"Mun yi tattaunawar gaskiya-da-gaskiya kan mawuyacin halin da ƙasarmu ke ciki, ƙaruwar matsin tattalin arziƙi, rashin tsaro da kuma buƙatar da ake da ita ta gaggawa wajen ganin an ceto ƙasar daga gocewa daga kan hanya da kuma faɗawa cikin mugun hali," a cewar Atiku wanda ya wallafa saƙon tare da hotunansa tare da Amaechi suna raha.
Ana kallon ziyarar a matsayin wani mataki na neman sulhu da Amaechi a siyasance bayan abin da ake ganin zai iya zama babbar matsala ga tafiyar manyan ƴan siyasar na hamayya waɗanda suka shiga jam'iyyar ADC da nufin ƙalubalantar shugaban Najeriya mai ci, Bola Tinubu a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Shi ma ɗan takaran da ya zo na uku a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar ta ADC Mohammed Hayat-Deen ya yi ƙorafi kan zaɓen.
Masana da dama sun yi fargabar cewa za a iya samun ɓaraka bayan zaɓen fitar da gwani na jam'iyyu, kasancewar waɗanda suka gaza yin nasara a wasu lokutan kan fice zuwa wasu jam'iyyu na daban.
Amurka na barazanar ƙaƙaba ƙarin takunkumi kan Ira
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump
Amurka na ƙoƙarin ƙara matsa wa Iran lamba ta fannin tattalin arziƙi domin tilasta wa Iran ɗin ta buɗe mashigar Hourmuz.
Sakataren kuɗi na Amurka Scott Bessent ya ce Amurka za ta haramta wa jiragen sama mallakin kamfanonin Iran sauka a wasu filayen jiragen sama domin ƙara mai.
Wannan sanarwa na zuwa ne kwana ɗaya bayan ma'aikatar kuɗi ta Amurkar ta fitar da bayanai kan wasu matakai da take shirin ɗauka kan wata sabuwar ma'aikata da ke karɓar haraji kan jiragen ruwan da ke ratsawa ta Mashigar Hormuz.
Isra'ila ta kai farmaki birnin Beirut
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Isra'ila ta kai hari a Beirut, babban birnin Lebanon, karo na biyu tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a watan da ya gabata.
Dakarun IDF sun ce harin an tsara shi ne amma ba su bayar da cikakken bayani ba.
Kafofin yaɗa labarai a Isra'ila sun ambato wasu majiyoyi da ba a faɗi sunansu ba suna cewa wanda aka nufa da harin shi ne shugaban wata ƙungiyar masu riƙe da makamai a Iran.
Isra'ila ta sassautawa Beirut bisa buƙatar Shugaban Amurka Donald Trump sannan harin na zuwa ne bayan hare-hare babu ƙaƙautawa da Isra'ila ta kai gine-ginen Hezbollah a Kudancin Lebanon, a cewar IDF.
Isra'ila da Hezbollah mai samun goyon bayan Iran - sun zargi juna da ci gaba da saɓa yarjejeniyar.
An ga baƙin hayaƙi na ratsowa ta gine-gine a Dahieh, da ta zama cibiyar Hezbollah a babban birnin bayan da hare-haren baya-bayan nan na Isra'ila.
An kuma jiyo mazauna yankin suna kiran maƙwabta da ƴanuwa yayin da masu aikin ceto ke kai ɗauki.
Australiya na tuhumar wata mata kan shiga IS
Asalin hoton, Supplied: Australian Federal Police
An tuhumi wata mata mai alaƙa da ƙungiyar IS wadda a shekarar da ta gabata ta koma Australiya daga Syria da laifin zama mamba a ƙungiyar ta'addancin.
Matar mai shekara 34 ta isa Australiya a Satumba tare da wata mata, in ji ƴansanda kuma an tsara za ta bayyana gaban kotu a Melbourne yau.
Sanarwar ta zo ne bayan da wasu tawagar mata da yara suka isa Australiya cikin watan nan bayan shafe shekaru a sansanin al-Roj da ke arewa maso gabashin Syria inda ake tsare da iyalan mayaƙan IS tun 2019.
Uku daga cikin matan da suka dawo a watannan suna fuskantar tuhume-tuhume da dama ciki har da laifukan cin zarafin bil adama.
Laifukan da ake tuhumar matar da aikatawa an tanadar musu hukunci kusan shekara 10 a gidan yari, kamar yadda mataimakiyar kwamishinan ƴansanda Hilda Sirec ta shaida wa manema labarai.
Ta ce matar, wadda kafafen yaɗa labarai suka bayyana sunanta da Rayann El Houli, ta je Syria a 2013 ko 2014 kuma Ƙurdawa suka tsare ta a 2019 inda aka ajiye ta a sansanin al-Hawl da ke Syria.
Halin da ake ciki a Kenya bayan gobarar da ta kashe ɗalibai 16
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani ɓangare na gobarar inda wata ƴarsanda ke wucewa ta gaban ƙwararrun masu bincike da ke tsaye a ƙofar shiga ginin makarantar Utumishi.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wata uwa ke nan da aka rirriƙeta yayin da take cikin kaɗuwa bisa halin da ake ciki na gobara da ta halaka ɗalibai wasu 79 kuma suna asibiti.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ƴan'uwan ɗalibai da suka taru a harabar makarantar da ke arewa da Nairobi, babban birnin Kenya.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wani mahaifi ke nan yake neman a bashi damar shiga harabar makarantar.
Amurka ta zargi Iran da saɓa ƙa'idojin yarjejeniya
Asalin hoton, Getty Images
Babbar Cibiyar tafiyar da harkokin soji ta Amurka ta zargi Iran da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar harba miyagun makamai a Kuwait.
Tehran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin Amurka a Kuwait a matsayin martani ga harin makamai masu linzami da Amurka ta kai mata.
Kuwait ta samu harbo jirgin.
Hare-haren baya-bayan nan na barazana ga yarjejeniyar da ke ƙasa amma ana ci gaba da tattaunawa don samar da yarjejeniya mai ɗorewa.
Jagoran addinin Iran Ayatollah Mojtaba Khamenei ya ce Amurka da Isra'ila na neman tarwatsa ƙasarsa. Ya faɗi haka ne cikin saƙon da aka karanto a gidan talabijin na ƙasar.
Khamenei bai bayyana cikin jama'a ba tun bayan da aka naɗa shi kan muƙamin.
NLC ta caccaki gwamnati kan taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziki
Asalin hoton, Nigeria Labour Congress HQ/FB
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta soki yadda ake samun taɓarɓarewar matsalar tsaro da tattalin arziki a ƙasar.
A saƙon barka da sallah da Shugaban NLC, Joe Ajaero, ƙungiyar ta ce ma'aikatan Najeriya da talakawa na cikin ƙunci ƙarƙashin manufofin
A cewar shi, miliyoyin mutane na jurewa yanayin tsadar rayuwa da ke ƙara jefa mutane cikin talauci inda kuma ya yi kira ga ƴansiyasa da su yi nazari kan tasirin matakansu na tattalin arziki.
Mambobin NLC sun yi kira da a ɗauki matakai domin magance matsalar tsaro da ke ta'azzara a ƙasar.
Ajaero ya kuma ce ya kamata gwamnatoci su mayar da hankali wajen kare rayukan al'umma da kuma samar musu da abubuwan buƙata kamar abinci da kiwon lafiya da ilimi da kuma ayyukan yi.
EU ta ci tarar Temu dala miliyan 232
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Ƙungiyar Tarayyar Turai sun ci tarar kamfanin kasuwancin intanet na Temu dala miliyan 232.
Jami'ai sun ce kamfanin ya gaza yin abin da ya kamata wajen hana sayar da haramtattun kayayyaki da kaya masu illa ga kwastamominsa da ke EU ciki har da cajar waya da kuma kayan wasan yara.
Matakin na zuwa ne bayan wani bincike na shekara biyu da aka yi kan ƙorafe-ƙorafen da hukumomin kare haƙƙin masu sayen kaya daga ƙasashen Turai 17 suka yi game da ayyukan kamfanin na Temu.
Kamfanin na Temu yana da nan da watan Agusta ya yi gamsasshen bayani ko kuma ya fuskanci hukunci.
Me sabon rahoton Amurka ya ce kan Fulani a Najeriya?
Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoton Amurka ya yi iƙirarin cewa Fulani masu gwagwarmaya da makamai na ci gaba da gagarumar mamaya a gonakin Kiristoci da kai miyagun hare-hare a kan wuraren addinan Kiristanci da na Musulmai.
Ya ce a 'yan shekarun nan, masu gwagwarmaya da makamai daga tsatson Fulani sun tafka miyagun hare-hare a kan al'ummomi da ba lallai kawai Kiristoci ba a Najeriya.
Ya ce da yawan ƙungiyoyin Fulani 'yan ta-da-ƙayar-baya na ƙaddamar da hare-hare, amma akwai wasu waɗanda lokaci-lokaci suna haɗa gwiwa da gungun 'yan fashin daji, da kuma sanannun ƙungiyoyin 'yan ta'adda don yaɗa wata fassarar addinin Musulunci ta tarzoma.
Najeriya, musamman yankin arewacinta na fama da rikice-rikice masu nasaba da ƙabilanci ko addini.
A baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana "gallaza wa Kiristoci" a Najeriya, zargin da hukumomin ƙasar suka musa.
Ƙananan yara da mata sun mutu a harin Isra'ila kan Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar agaji ta
Palestine Red Crescent da kuma wasu majiyoyi daga wani asibiti sun ce wani hari
da Isra'ila ta kai kan wani gida da ke Gaza ya yi sanadin rasa rayukan mutum
bakwai ciki har da ƙananan yara mata biyu tare da jikkata wasu 15.
Rahotannisun ce wani
jirgin yaƙin Isra'ila ne ya harba makamai masu linzami a kan gidan da ke
tsakiyar birnin.
Rundunar sojin
Isra'ila dai ta ce ta kai wa wasu manya biyu a ƙungiyar Hamas hari a arewacin
Gaza, to amma bata bayyana sunayensu ba.
A jiya Laraba
Isra'ilan ta hallaka sabon kwamandan Hamas a Gaza wato Mohammed Odeh.
Wannna rikicin dai na
zuwa ne duk da yarjejeniya tsagaita wuta da aka amince da ita a watan Oktoban
da ya gabata.
ADC za ta ceto dimokraɗiyya daga barazana - Atiku
Asalin hoton, Atiku Abubakar/FB
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce tsarin da aka bi wajen ba shi takarar yin zaɓe a jam'iyyarsa ta ADC ya nuna cewa dimokraɗiyya ba ta mutu ba.
Da yake magana bayan samun tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin ADC a Abuja, Atiku ya ce yayin da jam'iyya mai "mulkin zalunci da adawa da dimokraɗiyya" ke yi wa dimokraɗiyyar riƙon sakainar kashi, dimokraɗiyya na nan da ranta a ADC.
"Ina son miƙa godiyata bisa wanan dama da kuka ba ni, ta yi wa jam'iyyarmu ta ADC takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa. Na ji daɗi ƙwarai da gaske da wannan karramawa." in ji Atiku.
Atiku ya ƙara da cewa ADC a shirye take ta kuɓutar da dimokraɗiyyar Najeriya da ke fuskantar barazana mafi muni tun komawa tsarin mulkin dimokraɗiyya a 1999.
Ya ce mambobin jam'iyyar na da damar bayyana ra'ayinsu su kuma nemi takara a tsari na gaskiya da adalci.
Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fitar da gwanin na shugaban ƙasa a ADC da ƙuri'a 1,846,370 inda ya doke abokan takararsa da suka fafata a zaɓen - Rotimi Amaechi da kuma Muhammed Hayatu-Deen.
Sanata Omo-Agege ya fice daga APC
Asalin hoton, Senator Ovie Omo-Agege/FB
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege ya fice daga Jam'iyyar APC mai mulki.
Cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara ka harkar labarai, Sunday Areh ya fitar, Sanata Omo-Agege ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓa da ya yi da makusantansa a siyasa da kuma magoya bayansa, bugu da ƙari kuma abubuwan baya-baya da suka faru a jam'iyyar reshen jihar Delta.
Tsohon ɗanmajalisar ya ce ya fi dacewa ya nemi cika burinsa na siyasa da muradan da yake da shi ga al'ummar mazaɓarsa a wata jam'iyyar inda ya ƙara da cewa ba zai ci gaba da kasancewa a jam'iyyar da ba zai iya samar da ci gaba ga mutanensa ba.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito Omo-Agege yana gode wa APC bisa damar da ta ba shi na riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar dattawa a majalisa ta tara inda kuma ya ce yana yi wa jam'iyyar fatan alheri.
Isra'ila na ƙara zafafa hare-hare a Lebanon
Asalin hoton, AFP
Ƙarin wasu hare haren
da Isra'ila ta kai sun faɗa ciki da kuma kewayen birnin Tyre da ke kudancin
Lebanon inda suka faɗa kan wani gini da ya kama da wuta daga bisani.
Rundunar sojin
Isra'ila ta ce tana harin gine-ginen 'yan Hezbollah ne bayan ta umarci mazauna
wurin da su tashi daga wajen.
Wakilin BBC ya ce
hare-haren sun zo ƙasa da sa'oi biyu da Isra'ila ta bai wa mazauna wajen umarnin
su tattara nasu ya nasu su bar wuraren inda aka bar su da yanke hukunci mai
sarƙaƙiyar gaske.
Rundunar ta ce wani
hari da jirgi marar matuƙi da Hezbollah ta kai ya kashe wani soja a arewacin
Isra'ila.
Ƙungiyar agaji ta Red
Cross, ta ce kashe 'yan Lebanon da kuma lalata wurare da ake na nufin
rayuwa ta yi tsanani ga fararen hula.
Gobara ta yi ajalin ɗalibai 16 a Kenya
Asalin hoton, Robert Maina
Ɗalibai 16 sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a makarantar kwana da ke Gilgil a Kenya, kamar yadda wani ɗansanda ya shaida wa manema labarai.
Wasu ɗalibai 74 kuma suna samun kulawa a asibiti bayan raunin da suka ji.
Gobarar da ta faru a makarantar ƴanmata ta Utumishi ta soma ne da sanyin safiyar yau Alhamis lokacin da ɗaliban suke barci, in ji ƙungiyar agaji ta Red Cross a Kenya da kuma ƴansanda.
Ƴansanda sun ce ana aikin ceto sai dai zuwa yanzu hukumomi ba su gano musabbabin gobarar ba.
Ƙungiyar Red Cross a Kenya ta ce masu bayar da agajin gaggawa na wajen domin ba da tasu gudunmawar.
A yayin da yake magana da iyayen ɗalibai da sauran mutanen da suka taru a wajen makarantar, babban jami'in ƴansanda Masoud Mwinyi ya ce lamarin abin tashin hankali ne.
Dama a kan samu tashin gobara a makarantun kwana a Kenya inda a shekarun baya-bayan nan lamari ya janyo mutuwar mutane.
Amurka da Iran sun yi wa juna luguden wuta
Asalin hoton, US Navy via Getty Images
Amurka da Iran sun kai wa juna hare-hare a Gabas ta Tsakiya, abin ya nemi ya jirkita ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi domin kawo ƙarshen yaƙin da ƙasashen biyu ke yi.
Sojojin Amurka sun ce sun ƙaddamar da abin da suka kira kare kai daga hare-haren da aka kai wa jami'ansu da jirage maras matuƙa inda suka
harbo hudu daga cikinsu.
A matsayin martani, dakarun juyin juya halin Iran sun ce
sun kai hari kan wani sansanin sojin Amurka da ke yankin.
Ba su bayyana ko ina ne ba, to amma an jiyo ƙarar jiniyar
ankarar da mutane za a kawo hari ta sama a Kuwait.
Kafar yaɗa labaran Iran ta ce tun da farko wasu jiragen
ruwa sun yi ƙoƙarin wucewa ta Mashigar Hormuz ba tare da neman izini ba daga
Tehran abin da ya janyo dakarunsu harba makaman gargaɗi.
Barka da Zuwa
Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na marhaba da ɗumbin masu bibiyar mu a wannan ranar Alhamis.
Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma wainar da ake toyawa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.
Nabeela Mukhtar Uba ce za ta kasance tare da ku a don haka sai ku ci gaba da kasancewa da mu.
Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo har ma ku tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.