Ana tuhumar wata fitacciyar ƴar TikTok da kashe saurayinta a Dubai
Wata fitacciyar ƴar TikTok mai shekara 23 daga Gravesend da ke Kent a Birtaniya, Brooke George, na fuskantar tuhuma kan zargin kashe saurayinta a Dubai.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam a Haɗaɗɗiyar Daular Laraba mai suna Detained in Dubai, ta ce tana iya fuskantar hukuncin kisa ta hanyar harbi idan aka same ta da laifi.
Ƙungiyar ta ce George na fuskantar tuhuma ne kan zargin daɓa wa wani mutum wuƙa har lahira, wanda suka fara soyayya bayan sun haɗu ta yanar gizo.
"George ta ce ta ɗauki wuƙar ne domin kare kanta a yayin da saurayin nata ya ke ƙoƙarin illata ta," in ji ƙungiyar.
Ƙungiyar ta buƙaci a bayar da belinta tare da duba lamarin.
An kama George, wadda tsohuwar ma'aikaciyar kamfanin John Lewis ce, a safiyar ranar 22 ga Yuni, kuma daga baya aka gurfanar da ita bisa zargin kisan kai.
Idan aka same ta da laifi, tana iya fuskantar hukuncin kisa ƙarƙashin dokokin UAE.
Yayin da ake tsare da ita a ofishin ƴansanda na Bur Dubai, George ta yi zargin cewa an tilasta mata cire kayanta gaba ɗaya a gaban jami'an ƴansanda maza ba tare da wata jami'ar mace a wurin ba, abin da ta bayyana a matsayin abin kunya da kuma tayar da hankali, kamar yadda ƙungiyar Detained in Dubai ta bayyana.