Abin da muka sani game da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon

    • Marubuci, Yang Tian
    • Marubuci, Helen Sullivan
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Lebanon da Isra'ila sun amince da tsagaita wuta na kwanaki 10 da zai fara aiki da karfe 5:00 agogon ƙasar.

Sai dai bai yi wani ƙarin bayani game da ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran a Labanon ba, wadda Isra'ila ke ta musayar wuta da ita cikin makonni shida da suka wuce.

Sai dai a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social daga bisani, ya buƙaci ƙungiyar ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar, inda ya ce, "Ina fatan Hezbollah za su yi biyayya a wannan lokaci mai muhimmanci."

Bayan sanarwar, shugaban na Amurka ya kuma gayyaci Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban Lebanon Joseph Aoun zuwa fadar White House domin ci gaba da tattaunawa.

Ga abubuwan da muka sani game da yarjejeniyar.

Abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa

Yarjejeniyar ta tsawon tsagaita wutar ta tsawon kwanaki 10 ce, amma da yiwuwar a tsawaita idan an samu fahimtar juna a tattaunawar da ake yi.

Wasu ƙarin bayanai da Hukumar Tsaron Amurka ta fitar sun bayyana cewa:

  • Isra'ila tana da hurumin ɗaukar duk matakan da suka dace domin "kare kai" a kowane lokaci idan aka kai mata hari.
  • Gwamnatin Lebanon "za ta ɗauki matakan da suka dace don taka wa Hezbollah burki, da sauran masu tada ƙayar baya masu ɗauke da makamai" a cikin ƙasarta.
  • Ƙasashen sun amince da " alhakin Lebanon da ƴancinta na tabbatar da tsaron ƙasar".
  • Isra'ila da Lebanon sun buƙaci Amurka da ta ci gaba da shiga tsakanin kasashen biyu a tattaunawar da ake yi, da nufin warware duk wasu batutuwan da suka rage.

Bayanin ya ƙara da cewa amincewa da yarjejeniyar ya biyo bayan "dattakun" da Isra'ila ta nuna da kyakkyawar manufa domin ba da damar tattaunawar samar da tsaro da zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.

Me ɓangarorin suka ce?

Shugabannin Isra'ila da Lebanon sun yi maraba da yarjejeniyar, inda Netanyahu ce "dama ce ta samar da yarjejeniya mai cike da tarihi".

Firaministan Lebanon Nawaf Salam ya ce yana fatan yarjejeniyar za ta ba da dama ga waɗanda aka raba da muhallansu su koma gidajensu.

Ita ma Hezbollah ta nuna alamar yin biyayya ga tsagaita wutar, amma ta ce dole "a dakatar da kai mata hare-hare" a faɗin Lebanon da kuma hana dakarun Isra'ila "zirga-zirga yadda suka ga dama" a yankin.

Ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran, tana da tasiri a Lebanon duk da yake ba ta cikin tsarin gwamnatin ƙasar da tsaronta.

Ministan harkokin wajen Iran ya yi maraba da tsagaita wutar, inda kakakinsa Esmail Baghaei ya bayyana mubaya'arsa ga Lebanon. Tehran ta nace cewa tsagaita wutar da aka yi tsakaninta da Amurka na makonni biyu ya haɗa har da Lebanon, inda Isra'ila da Amurka suke ce ba haka lamarin yake ba.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, ya yaba da rawar da Amurka ta taka wajen tsagaita wutar, inda ya buƙaci dukkanin ɓangarorin su "mutunta" yarjejeniyar da dokokin ƙasa da ƙasa.

Shugabar Ƙungiyar Tarayyar Turai Ursula von ​der Leyen ta bayyana yarjejeniyar a matsayin "salama", inda ta ce Tarayyar Turai za ta ci gaba da kiran a "mutunta ƴancin cin gashin kan Lebanon da kare ƙimarta"

Jami'iar kula da harkokin waje na EU Kaja Kalas ta ƙara da cewa dole ne a yi amfani da damar tsagaita bude wuta don "dakatar da tashe-tashen hankula" da samar da damar tattaunawa da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ina ne wuraren da Iran ta mamaye?

Duk da yarjejeniyar, Netanyahu ya ce dakarun Isra'ila za su ci gaba da zama a tsakanin tazarar kilomita 10 a kudancin Lebanon da ta mamaye, inda ya ce: "Za mu zauna a can, ba za mu tafi ba"

Ya ƙara da cewa inda ta mamaye zai ci gaba da zama "wajen kariya daga kutse".

Isra'ila ta sake shiga Lebanon ne bayan hare-haren da Hezbollah ta kai mata a farkon watan Maris, inda ta ci wani yanki da ta ce ya zama dole domin kare al'ummarta da ke arewacin Isra'ila

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya tsakanin Isra'ila da Hezbollah - wadda ta kawo ƙarshen rikicin watanni 13 - har yanzu ana kai hare-hare a kusa da kan iyaka.

Ya aka cimma yarjejeniyar?

Isra'ila da Lebanon sun gudanar da wata tattaunawar kai tsaye a farkon makon nan a birnin Washington, da nufin dakatar da yaƙin, wanda aka yi ta kai munanan hare-hare ta sama a wani ɓangare na Beirut babban birnin kasar Lebanon da kuma fada a kudancin ƙasar.

Sanarwar ta Trump ta ce yarjejeniyar ta zo ne bayan tattaunawa mai ma'ana tsakanin Aoun da Netanyahu, amma bai ambaci ko Hezbollah na cikin tattaunawar ba.

Ya buƙaci Hezbollah "ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar, a wannan lokaci mai muhimmanci."

Shi ma Netanyahu, yayin da yake maraba da tsagaita wutar, ya bayyana cewa yana shirin yin wasu rangwame.

Ya ce Hezbollah ta nace kan buƙatu biyu: a janye dakarun Ira'ila daga Lebanon, da kuma dokar kowa ya maida makami.

Sai dai da alama sanarwar tsagaita wuta ta zo wa Isra'ila da mamaki - kamar yadda rahotanni suka ce hatta cikin majalisar ministocin tsaro a gwamnati ba kowa ya sani ba.

Ta yaya wannan zai shafi yaƙin Iran?

A lokacin da aka sanar da tsagaita wuta da Iran, an yi ta samun saƙonni iri-iri kan ko Lebanon ciki. Jami'an Pakistan da suka shiga tsakani a tattaunawar cimma yarjejeniyar da kuma jami'an Iran sun ce haka ne, amma Isra'ila ta ce ba haka ba. Sakatariyar yaɗa labaran shugaban Amurka Donald Trump, Karoline Leavitt ita ma daga baya ta ce Lebanon ba ta cikin yarjejeniyar.

A ranar 2 ga watan Maris ne Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Lebanon a matsayin martani ga hare-haren da ƙungiyar Hezbollah ta kai mata. Hakan ya biyo bayan farmakin da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran - lamarin da ya janyo ramuwar gayya daga Tehran kan ƙawayen Amurka a yankin Gulf, da kuma na Iran da suka haɗa da ƙungiyar a Lebanon.

Tun a wancan lokaci Isra'ila da Hezbollah ke ci gaba da musayar wuta, duk da roƙon da Firaministan Labanon ya yi na a daina.

Fiye da mutane 2,100 ne aka kashe tare da raunata wasu 7,000 a hare-haren da Isra'ila ta kai kan Lebanon tun daga ranar 2 ga Maris, a cewar ma'aikatar lafiya ta ƙasar, ko da yake ba ta banbance tsakanin mayaƙa da fararen hula ba. Adadin ya haɗa da mata aƙalla 260 da yara 172.

Ma'aikatar ta ce an kashe ma'aikatan lafiya 91 tare da raunata wasu 208 a yaƙin, yayin da Isra'ila ta kai hare-hare sama da 120 kan motocin daukar marasa lafiya da kuma cibiyoyin kiwon lafiya.

Binciken BBC Verify ya gano an lalata sama da gine-gine 1,400 a Lebanon.

Hare-haren Hezbollah sun kashe fararen hula biyu a Isra'ila a lokaci guda, yayin da aka kashe sojojin Isra'ila 13 a yaƙin da aka gwabza a Lebanon, in ji hukumomin Isra'ila.

A ranar Alhamis sojojin Isra'ila suka lalata gadar ƙarshe da ta haɗa kudanci da sauran sassan ƙasar, lamarin da ya kara mayar da yankin saniyar ware tare da sake sabunta fargabar da dama daga cikin 'yan kasar ta Lebanon, inda ake ganin hakan na iya haifar da mamayar wasu yankuna na tsawon lokaci.