Farashin mai ya ƙaru saboda fargabar cikas ga jigilar mai ta Mashigar Hormuz

Asalin hoton, Getty Images
Farashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwannin duniya bayan fargabar cewa rikicin da ke yankin zai iya haddasa cikas ga jigilar mai ta Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar mai.
Farashin ɗanyen mai na Brent ya ƙaru da kashi 1.2 cikin ɗari zuwa dala 90.12 kan ganga, yayin da ɗanyen man Amurka ya tashi da kashi 1.3 cikin ɗari zuwa dala 84.67.
Hauhawar farashin ta biyo bayan rahotannin cewa an dakatar da wasu jiragen dakon mai ko kuma aka tilasta musu sauya hanya ta mashigar Hormuz.
Yaƙin Iran ya rage yawan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, yayin da barazanar mayaƙan Houthi kan jiragen ruwa a Bab al-Mandab ke ƙara jefa sauran hanyoyin fitar da mai cikin haɗari.


