Firaministan Birtaniya ya ce ba zai yi murabus ba

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Birtaniya Kier Starmer ya ce ba zai yi murabus daga muƙaminsa ba duk da matsin lambar da ake yi.
A hirarsa da BBC, Starmer ya ce gwamnatinsa ta ƙara kuɗin da ake ware wa fannin tsaro kuma yana daga cikin abin da ya fi ba muhimmanci.
Wannan na zuwa ne bayan da Sakataren Tsaron Birtaniya John Healey da mataimakinsa suka yi murabus domin nuna adawa da rashin kasafin kuɗin fannin tsaro mai kyau a ƙasar, da kuma sukar tsarin Starmer.
Ya shaida wa BBC cewa ya ɗauki matakai masu tsauri domin ganin ya ƙara kasafin kuɗin fannin tsaro.
Karanta wannan - Iran ta gargaɗi Amurka kan barazanar kai ma ta hari

































