Za mu ceto ɗaliban da aka sace a Borno da Oyo - Tinubu

Asalin hoton, STATE HOUSE
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ceto ɗalibai da malaman da ƴan bindiga suka sace a jihohin Borno da Oyo a baya-bayan nan.
Shugaban ƙasar ya bayar da wannan tabbaci ne a wani saƙo da ya fitar domin zagayowar ranar yara, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan hare-haren da aka kai kan makarantu a ƙasar cikin kwanakin nan.
"Yayin da muke murnar zagayowar wannan rana wadda ta faɗo a ranar bikin babbar sallah, ya kamata a ce ɗalibai da malaman nan na Oyo da Borno sun kasance tare da iyalansu, to amma suna can hannun bara-gurbi.
"An jefa (waɗannan) yara cikin tsoro, kuma wasu daga cikin iyaye ba za su iya yin muranar wannan rana ba saboda hankalinsu ya koma kan abu ɗaya: ' A dawo da yaranmu gida'," in ji Tinubu a saƙon nasa.
Hare-haren da aka kai kan makarantu a jihohin Oyo da Borno sun sake ɗaga hankalin al'ummar Najeriya kan amincin yara a makarantun da ke faɗin ƙasar, inda a halin yanzu gomman yara ke hannun ƴan bindiga.
A jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar, mahara ɗauke da makamai sun kai hari ne ranar 15 ga watan Mayu kan makarantar yara ta Community High School, Ahoro-Esinele, inda suka sace shugaban makarantar da malamai da kuma ɗalibai da dama, sannan suka kashe malami ɗaya.
Sai kuma a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar inda mahara suka sace ɗalibai a wata makaranta da ke ƙaramar hukumar Askira-Uba.
Najeriya na da tarihin sace-sacen ɗalibai da garkuwa da su a sanadiyyar rashin tsaro, musamman a jihohin arewa maso gabas da kuma arewa maso yammacin ƙasar.













































