An kai wa wasu tankokin dakon man Saudiyya hari a mashigar Hormuz
A cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kamar yadda muka ruwaito, an kai hare-hare kan aƙalla tankokin ɗanyen mai biyu a mashigar Hormuz ta hanyar harba wasu makamai da ba a gano ko su waye suka harba su ba.
Yanzu an fitar da ƙarin bayani game da lamarin.
A cewar Reuters, manyan tankokin ɗanyen mai guda biyu da ke ɗauke da man fetur na Saudiyya sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da ba a san ko wa ya harba su ba, a tazarar mintuna kaɗan da juna, yayin da suke wucewa ta mashigin Hormuz a daren ranar Litinin. Kamfanonin tattara bayanan zirga-zirgar jiragen ruwa, Marisax da Kepler, ne suka bayar da wannan bayani.
A cikin wata sanarwa da Marisax ta fitar, ta ce: "Wadannan hare-hare da suka faru kusan a lokaci guda suna nuna ƙarin tsananta yanayin barazanar tsaro a yankin mashigar Oman."
Bayanan Kepler sun nuna cewa tankokin biyu sun ɗora gangar ɗanyen mai miliyan biyu na Saudiyya daga tashar Juaima, da ke kudancin gabar Tekun Fasha, a makon da ya gabata.
Kamfanin mai na Saudiyya, Saudi Aramco, ya koma ɗora da sayar da mai ta mashigin Hormuz ne a watan Agusta da ya gabata, bayan ya dakatar da wasu ayyuka a yankin a baya.
































