Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na 21/05/2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman MINJIBIR

  1. APC ta tabbatar da Abba, Radda da Dauda ƴantakarar gwamna

    Jam’iyyar APC ta tabbatar da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takararta na maslaha domin shiga zaɓen 2027.

    Jam'iyyar ta zabi gwamna Abba a yayin taron amincewa da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a yau Alhamis.

    Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/FB

    A jihar Zamfara ma, gwamna Dauda Lawal da ke neman wa'adi na biyu ya samu tikitin takarar a jam’iyyar APC.

    An tabbatar da gwamna Dauda a matsayin dan takarar APC ba tare da hamayya ba.

    Dauda Lawal

    Asalin hoton, Dauda Lawal

    Shi ma gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar domin neman wa’adi na biyu.

    Ya samu nasarar ne bayan zama ɗan takara tilo na jam’iyyar ta hanyar amincewar bai-ɗaya daga wakilan dukkan mazaɓu 225 da ke faɗin jihar.

    Nasir Idris

    Asalin hoton, Nasir Idris/FB

    Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ma ya samu tikitin a yayin wani taro da aka gudanar domin tabbatar da shi a yau Alhamis.

    Dikko Radda

    Asalin hoton, Hannatu Musawa/FB

    Gwamna Ahmad Aliyu na Sokoto ma ya samu tikitinsa na takarar a karo na biyu bayan da magoya bayan jam'iyyar ta amince da shi.

    Gwamnan Sokoto Ahmed Aliyu

    Asalin hoton, Sokoto Govt

    Jam'iyar APCn ta ɗage zaɓen a jihohin Bauchi da Kwara, inda ake jiran jihohin Adamawa, Jigawa, Yobe, Niger, Taraba, Filato da Borno a yankin Arewacin Najeriya, duk da yake yawancinsu an cimma masalaha.

    A jihar Kaduna kuwa an amince da Uba Sani a matsayin dantakarar, sai kuma Jamilu Isiyaku Gwamna a jihar Gombe.

    Mataimakin gwamnan jihar Legas Obafemi Hamzat ne aka tabbatar a matsayin ɗantakarar gwamnan jihar.

  2. An ɗage zaɓen fitar da ɗantakarar gwamnan Bauchi na APC

    APC

    Asalin hoton, APC/X

    Ana ci gaba da zaman jira a jihar Bauchi, bayan da aka ɗage zaɓen fitar da ɗantakarar gwamna na jam'iyar APC.

    Bayanan da BBC ta samu sun tabbatar da cewa har yanzu ƴantakarar da jam'iyyar a matakin jihar ba su san dalilin ɗagewar ba, amma suna jiran mataki na gaba daga uwar jam'iyyar.

    Kakakin jam'iyyar APC a Bauchi, Shehu Dauda Muhammad ya shaida wa BBC cewa, sun samu umarni ne daga uwar jam'iyya kuma za a sanar da su wata ranar da za a gudanar da zaɓukan.

    "Mu a matakin jiha ba abin da za mu iya fadi, tun da ba mu san dalili ba," in ji shi.

    Kusan ƴantakara bakwai ne suke neman wannan kujera, ciki har da tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar, da tsohon babban jami’in NNPCL, Bala Wunti.

    Akwai kuma Nura Manu Soro, da M. A. Abubakar, da Kabir Baba Maaji, da Baba Abubakar Suleiman da Yakubu Yakubu Abdullahi,

    Kakakin Tuggar ɗin, Alkasim Abdulkadir ya shaida wa BBC cewa har yanzu suna jiran mataki na gaba daga uwar jam'iyyar.

  3. APC ta tabbatar da Jamilu Gwamna ɗantakarar gwamnan Gombe

    Dr. Jamil Isiyaku Gwamna

    Asalin hoton, Dr. Jamil Isiyaku Gwamna/FB

    Jam’iyyar APC a jihar Gombe ta ayyana Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna a matsayin zaɓaɓɓen ɗantakarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2027.

    A sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce Dr. Gwamna ya yi nasara ne bayan ya samu kuri’u 247,161 inda ya doke sauran ‘yan takara biyu da suka fafata a zaɓen.

    Yayin da ya ke sanar da sakamakon, shugaban kwamitin zaɓen Sanata Sani Danladi, ya ce Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu kuri’u 12,120, sai kuma tsohon Ministan Sufuri, Sanata Said Ahmed Alkali, ya samu kuri’u 11, 612.

    An gudanar da taron ne a sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar Gombe, inda ya samu halartar jami’an INEC karkashin jagorancin kwamishinan zabe na jihar, Alhaji Umar Mukhtar Gajiram.

    Farfesa Pantami da Sanata Alkali dai sun sanar da ƙauracewa zaɓen, bisa zargin taka dokokin zaɓe.

  4. Uba Sani ya lashe tikitin takarar gwamnan Kaduna da ƙuri’u 459,393

    Uba Sani

    Asalin hoton, Uba Sani/FB

    Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027

    A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ya zama ɗantakarar jam'iyyar ne bayan samun kuri’un amincewa daga wakilan jam'iyyar 459,393 a a yayin zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a yau Alhamis.

    "Uba Sani, wanda shi kaɗai ne ya tsaya takara a zaɓen, ya samu cikakken goyon baya daga wakilai da shugabannin jam’iyya a jihar," in ji sanarwar.

    Ta ce an gudanar da zaɓen fitar da gwanin ne a gaban jami’an hukumar zaɓe ta INEC.

    Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen Hon. Hafiz Ibrahim Kawu, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana.

  5. Najeriya ta kammala jigilar maniyyata aikin hajji zuwa Saudiyya

    Hajj in Nigeria

    Asalin hoton, Independent Hajj Reporters of Nigeria/FB

    Hukumar kula da mahajjata ta Najeriya ta sanar da cewa ta kammala aikin jigilar maniyyata aikin hajjin bana daga ƙasar zuwa Saudiyya.

    Hukumar ce ta sanar da haka a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a yau Alhamis.

    A ranar Talata 26 ga watan Mayu ne ake sa ran hawan Arfa, ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan aikin hajji a addinin Musulunci.

    Sanarwar da hukumar alhazan ta Najeriya ta fitar ta ce ta kammala aikin jigilar mahajjatan ne a da misalin ƙarfe 10:44 na safiya.

    Sanarwar ta ƙara da cewa an kwashe jimillar maniyyata 38,888 zuwa ƙasar ta Saudiyya, 24,159 maza, 14,729 mata.

    Akasarin maniyyatan (32,924) an yi jigilar su ne zuwa birnin Madinah, yayin da aka kai 5,964 birnin Makkah.

  6. Saliyo ta karɓi rukunin farko na ƴan Afirka da aka kora daga Amurka

    ..

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Saliyo ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta karɓi ƴan ci rani na Afirka ta Yamma da aka kwaso daga Amurka.

    Wani jirgi ɗauke da ƴan ci rani tara har da maza bakwai da mata biyu daga Ghana da Senegal da Guinea da Najeriya sun isa birnin Freetown ranar Laraba.

    Saliyo ta amince ta karɓi ƴan ci-rani 300 duk shekara inda a kowane wata za a rika samun mutum 25 da za su isa ƙasar bisa yarjejeniyar tallafin dala miliyan 1.5 daga gwamnatin Amurka.

    Hukumomi sun bai wa mutanen wurin kwana na tsawon mako biyu kuma za su iya zama har tsawon kwana 30 domin bai wa hukumomi damar shirya mayar da su ƙasashensu na asali.

    Akasarin ƴan ci-ranin sun bayyana sha'awar zuwa gida. Amurka ta ƙulla makamanciyar yarjejeniyar da Ghana da sauran ƙasashen Afirka inda aka tusa ƙeyar baƙin duk da kotu ta umarci a basu kariya.

    Ma'aikatar harkokin wajen Saliyo ta ce ƙasar tana karɓar baƙi daga ƙasashe 12 mambobin ECOWAS da mutanen da ba a taɓa samun su da aikata miyagun laifuka ba.

    Su ma za a duba lafiyarsu sannan ma'aikatar bai wa ƴan ƙasashen ECOWAS damar zama na tsawon kwanaki 90.

  7. An kafa sabuwar Jam'iyyar Kyankyasai a Indiya

    ...

    Asalin hoton, Cockroach Janta Party

    Wata jam'iyyar barkwanci a Indiya mai suna Jam'iyyar Kyankyasai ta samu fiye da mabiya miliyan 15 a shafin Instagram.

    An kafa jam'iyyar ne bayan da ake zargin babban ministan shari'a na Indiya ya kwatanta matasan da ba su da aikin yi da kyankyasai da ƙwari.

    Daga baya ya yi ƙarin haske cewa yana magana ne kan masu digirin bogi.

    Ƙa'idojin zama mamba a jam'iyyar su ne zama cima zaune da rashin aikin yi da kuma shagala a shafukan intanet.

    Wani hoto da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Instagram don murnar nasarar da ta yi ya ce "A kwana huɗu kacal muka samu wannan nasara. A daina raina ƙarfin tasirin matasa".

  8. An jinkirta aikin kwashe ƴan Ghana daga Afirka ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, GHANA HIGH COMMISSION IN SOUTH AFRICA

    Ma'aikatar harkokin waje ta Ghana ta jinkirta tashin jirgin da aka tsara kwashe ƴan ƙasar da ke Afirka ta Kudu sakamakon ƙaruwar zanga-zangar ƙyamar baƙin haure a Afirka ta Kudun.

    A wata sanarwa, ministan harkokin wajen Ghana Sam Okudzeto Ablakwa ya ce an ɗage shirin da wasu kwanaki saboda wasu dalilai.

    Hakan na zuwa ne sakamakon wasu rahotanni daga kafafen yaɗa labarai a Afirka ta Kudu da ke cewa ɗan Ghana guda aka gani ya je inda jirgin zai kwashi ƴan ƙasar.

    Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta ce 800 cikin jama'arta sun nuna sha'awar komawa gida, an samu ƙari ke nan daga 300 da aka samu a farkon makonnan.

    Ta ƙara da cewa an jinkirta tashin jirgin ne saboda adadin mutanen da aka samu sun ƙaru.

    Ma'aikatar ta kuma ce buƙatar a bi wasu ƙa'idoji na shari'a har da tantance fasinjoji na daga cikin dalilan da suka janyo tsaikon.

    Sai dai babu ƙarin bayani kan mutum nawa ne cikin 800 ɗin za su fice daga Afirka ta Kudu kaancewar kafafen yaɗa labaran ƙasar na ruwaito cewa babu fasinjoji a filin jirgin saman.

    Ana fargabar cewa zanga-zangar baya-bayan nan a sassan Afirka ta Kudu na iya janyo dawowar rikicin ƙyamar baƙi.

    A 2019, aƙalla mutum 12 aka kashe sannan a 2008, baƙi 62 ne suka mutu a hare-haren da aka kai kan baƙi a sassan ƙasar.

  9. Philippines ta ce tana farautar Ronald Dela Rosa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar shari'a a ƙasar Philippines ta ce ta fara farautar Sanatan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo dangane tuhume-tuhumen da ke da alaƙa da yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

    Ronald Dela Rosa ya ɓace ne makon jiya bayan wani harbi da aka yi a zadai ya bayyana ne na wani dan lokaci don tabbatar da cewa wani abokin tsohon mai gidansa, Rodrigo Duterte, ya yi nasarar zama shugaban majalisar dattawan kasar.

    Ana zargin Mista Dela Rosa ne da haɗa baki da Mista Duterte wajen kashe wasu mutum talatin da biyu masu ta'ammali da miyagun kwayoyi.

    Tuni dai aka riga aka cika hannu da Mista Duterte wanda ay ke tsare a halin yanzu.

  10. Columbia ta kori jakadan Bolivia

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Colombia ta kori jakadan Bolivia a wani mataki na sa-in-sa na diflomasiyya, sa'o'i kadan bayan da aka nemi ita ma jakadanta ya bar Bolivia.

    Takaddamar diflomasiyya ta samo asali ne daga kalaman shugaban Colombia Gustavo Petro na cewa zanga-zangar da aka yi a Bolivia na adawa da shugaba Rodrigo Paz ta yi nuni da rashin da farin jininsa.

    Shugaban na Bolivia ya bayana kalaman takwaransa na Colombia a matsayin katsalandan a cikin al'amuran kasarsa.

    Ana zaman dar-dar a Bolivia inda zanga-zangar da ake yi kan tsadar rayuwa ta ta rikide ta zama ta adawa da gwamnatin Mr Paz a fadin kasar.

  11. Tinubu ya nada ɗan shekara 39 a matsayin shugaban JAMB

    ..

    Asalin hoton, Onanuga/X

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar da ke tsara jarrabawar shiga jami'a, JAMB.

    Aina wanda shekarunsa 39 ya maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede wanda wa'adinsa ke ƙarewa ranar 31 ga watan Yulin 2026.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya bayyana Aina a matsayin fitaccen masanin kuma ƙwararre da yake da gogayya a harkokin jarrabawa da intanet da kuma sauye-sauye a abubuwan da suka shafi al'umma.

  12. Ƙungiyar agaji ta zargi sojojin Isra'ila da azabtarwa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ƙungiyar ba da agaji ta Falasdinawa ta ce masu fafutuka da aka tsare daga wani jerin gwanon jiragen ruwan Gaza sun zargi sojojin Isra'ila da cin zarafi da kuma azabtarwa.

    An kai mutum uku daga cikinsu asibiti, ko da yake a halin yaznu an sallame su. Tun da farko dai Ministan Tsaron Isra'ila Itamar Ben Gvir ya sha suka bayan ya fitar da wani bidiyo inda ya ke yi wa masu fafutukar izgili yayin da ake tsare da su.

    Bidiyo ne na tsawon dakika talatin da takwas da ya nuna jerin wadanda aka tsare suna zaune a kasa a daure yayin da Ben Gvir ya ke musu dariya yana cewa maraba da zuwa Isra'ila mu ne masu iko a nan.

    Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce abin da ministan aikata ya ci karo da dabi'un isra'ila.

  13. Al'ummar Diffa a Nijar na fuskantar barazanar ƙarancin abinci

    ..

    Asalin hoton, ORTN

    Manoma a jahar Diffa da ke jamhuriyar Nijar sun koka kan fuskantar wasu matsaloli guda da ke barazana ga samar da abinci a yankin.

    Manyan matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya sun haɗa da rashin tsaro da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, da sauyin yanayi, da hare-haren da kwari ke kai wa muhimman amfanin gona, lamarin da ya haifar da karancin albarkatun noma a kasuwanni.

    Tuni dai manoman suka koka da matsalar suna masu cewa lamarin ya jefa su cikin halin ha'u'la'i.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da damuna ke ƙara ƙaratowa sannan kuma ake ta gyare-gyaren gonaki.

  14. Ana cece-kuce tsakanin Atiku da Amaechi kan takarar shugaban ƙasa a ADC

    ..

    Asalin hoton, bbc collage

    A Najeriya takaddama ta kaure tsakanin manyan masu neman takarar shugabancin kasar a jama'iyyar ADC Rotimi Amaechi da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar.

    An dai jiyo wasu kalamai daga bakin Amaechin, inda ya ce Atiku Abubakar ba mutum ne da zai iya lashe zaɓe ba, ko da kuwa ya samu takara a jama'iyyar.

    Amaechi ya kafa hujja da zaɓukan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya tsaya a baya, kuma ya sha kaye, yana mai cewa a yanzu kamata ya yi jam’iyyarsu ta mayar da hankali ga wanda jama’a za su iya zaɓa, ba wanda ya saɓa takara ba.

    Sai dai kuma ɓangaren Atiku sun ce Kalaman na Amaechi na "tsoro ne" saboda sun san cewa Atiku ya fi ƙarfinsu sannan zai fi samun karɓuwa daga yan Najeriya.

    Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya, Atiku Abubakar dai ya yi takarar shugaban ƙasa karo na huɗu kuma idan ya samu takarar a 2027, hakan zai kasance takararsa ta biyar kenan.

  15. Ƴan Ghana da ke Afirka ta Kudu za su koma gida

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Alhamis ɗin nan ne wata tawagar 'yan ci-rani 'yan asalin ƙasar Ghana da ke Afirka ta Kudu za su koma ƙasarsu.

    Suna tserewa ne daga zanga-zangar ƙin jinin baƙi a biranen Afirka ta Kudu, inda masu zanga-zangar ke zargin baƙi da asassa matsalar tabarbarewar tattalin arziki

    Gwamnatin Ghana dai ta ce yan kasarta guda dari uku ne da ke Afrika ta kudu suka mika bukatar komawa gida, masu zanga-zangar suna zargin bakin haure ne da ta'azzara matsalar karancin albashi da rashin aikin yi.

    Najeriya ma ta ce sama da ƴan kasarta 100 ne suka nemi a mayar da su gida. A na ta bangaren Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da duk wani cin zarafi da ake kai wa ƴan kasashen waje.

  16. Shugaban Cuba ya yi watsi da tuhumar da Amurka ta yi wa Raul Castro

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Tsohon shugaban Cuba Raul Castro lokacin da yake bayani a Majalisar Dokoin ƙasar bayan da Diaz-Canel ya ci zaɓe a 2018 a Havana

    Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya yi watsi da tuhumar da Amurka ta yi wa magabacinsa Raul Castro a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.

    Zarge-zargen da a ke yi wa tsohon shugaban na Cuba mai shekara 94 sun samo asali ne daga wani lamari da ya faru a shekarar 1996 inda jiragen yakin Cuban suka harbo jiragen sama guda biyu da wata kungiyar yan sa kai ta 'yan gudun hijirar Cuban ke amfani da su.

    Ana tuhumar Raul Castro da laifuffuka hudu na kisan kai, amma manazarta sun ce wani yunkuri ne na Washington na tabbatar da sauyin gwamnati a Havana.

    Takunkuman da Amurka ta kakabawa tsibirin ya durkusar da tattalin arzikinsa baki daya.

    Shugaba Trump ya bayyana tuhumar a matsayin lamari mai cike da tarihi amma ya yi watsi da yiwuwar daukar matakin soji

  17. Ana samun hauhawar hannun jari a Asia saboda tsagaita yakin Iran

    An sami hauhawar darajar hannun jari a kasuwannin Asiya, sakamakon bunƙasar kamfanonin fasaha da fatan da ake da shi cewa nan ba da jimawa ba za a warware rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Kasuwar Nikkei ta Japan ta tashi da sama da kashi uku cikin ɗari, yayin da hannayen jarin kamfanonin Koriya ta Kudu suka tashi da kusan kashi biyar cikin ɗari.

    Muhimmin cigaban da aka samu a kamfanin kera-keren fasaha na Amurka , (Nvidia), da shawarar da ma'aikatan Samsung suka yanke na kin shiga yajin aiki, da shirin da ake yi na sayar da hannayen jari a kamfanonin SpaceX da OpenAI sun taimaka wurin bunkasa darajar hannayen jarin kamfanonin fasaha.

  18. Muna ƙoƙarin samun maganin cutar Ebola - Jami'in Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jami'in ma'aikatar lafiya ta Amurka ya ce wata hukumar gwamnati tana aiki tare da wani ƙaramin kamfanin sarrafa magunguna don sarrafa wani maganin gwaji na cutar Ebola.

    Asali dai an kirkiri maganin ne domin yaki da wani na'uin cutar amma bayan gwaje-gwaje sun nuna cewa zai iya yin tasiri a kan nau'in Bundibugyo wanda a halin yanzu ake fama da shi a gabashin Kongo.

    Wani jami'in hukumar lafiya ta duniya, ya ce ana kuma nazari kan wata allurar rigakafi ta daban.

    Ya ce "Wancan wani aikin hadin gwiwa ne tsakanin jami'ar Oxford da cibiyar sarrafa maguguna ta India, kuma ana kan sarrfata a halin yanzu amma babu isasun bayanai a kan tasirinta".

    Sama da mutane 130 ne ake tunanin cutar ta kashe a gabashin Kongo, inda ake zargin mutane 600 sun kamu da cutar a lardin Ituri mai iyaka da Uganda da Sudan ta Kudu.

  19. Kamfanin SpaceX na Elon Musk na son tallata hajarsa a kasuwar Nasdaq

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin SpaceX na Elon Musk ya gabatar da takarda a hukumance a gaban masu kula da harkokin kuɗi na Amurka don neman izinin tallata hannun jarinsa a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nasdaq.

    Yana daya daga cikin tallar hannun jari da ya fi jan hankali a tarihi, kuma kamfanin yana shirin zama kamfani na farko da zai fara kasuwancin hannun jari da darajar dala trillian ɗaya.

    Wakiliyar BBC ta ce Ko da bayan siyar da hannayen jarin, ana sa ran Elon Musk zai ci gaba da kasancewa mai cikakken iko, har yanzu dai kamfanin bai bayyana adadin hannun jarin da yake shirin sayarwa ba da kuma a kan wani farashi.

    Takardun da kamfanin ya gabatar sun tabbatar da cewa SpaceX yanzu ya kunshi kamfanin kirkirarriyar basira na Elon Musk (XAI), da kuma dandalin sada zumunta na X wanda a baya aka sani da Twitter

  20. Iran ta ce tana yin duban tsanaki kan sabbin buƙatun Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce tana nazari kan sabbin shawarwarin da Amurka ta gabatar kan kawo ƙarshen yaƙin da take da Iran ɗin.

    Ana tunanin Pakistan ce ta gabatar da sabon daftarin ga shugabancin Iran, bayan ministan harkokin wajenta ya ziyarci Tehran a jiya Laraba.

    Shugaba Trump ya ce zai jira na kwanaki domin samun martanin Iran, amma ya sake yin barazanar ɗaukar matakin soji idan har Iran ba ta amince da daftarin ba.

    Tehran ta ɗauki wani mataki na ƙara tabbatar da ikonta a mashigar Hormuz inda ta buƙaci jiragen ruwa su yi aiki tare da wata sabuwar hukumar kula da mashigar da aka ƙirƙira.