KAI TSAYE, Man United ta koma kamar wajen wasan kwaikwayo - Keane

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin kai tsaye a BBC Hausa daga 11 zuwa 18 ga watan Oktoban 2026.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ta samu ribar Euro miliyan 4.1, Faransa

    Kylian Mbappe

    Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa (FFF) ta sanar a ranar Alhamis cewa ta samu ribar Euro miliyan 4.1 (dala miliyan 4.60), tare da kara yawan kudin tallafi ga kwallon kafa daga tushe da tawagar ta mata zuwa sabon matsayi mafi girma na kusan Euro miliyan 120 a shekarar kudi ta 2025-26.

    Tallafin da aka ware wa kwallon kafa har da ta Kwararru da sauran shirye-shiryenta ya kai Euro miliyan 117.2, wanda ya zarce na kakar da ta gabata da sama da Euro miliyan 10.

    A karo na biyu a jere, FFF ta amince da yafewa Hukumar Gasar Kwallon Kafa ta Kwararru ta Faransa bashin Euro miliyan 10, inda ta ci gaba da bayar da tallafin kudi ga wasan kwallon kafa na ƙwararru.

    FFF ta ce kudin shigar da ta samu sun kai sabon matsayi mafi girma na kusan Euro miliyan 300 (dala miliyan 336.30), sakamakon sabunta yarjejeniyar daukar nauyi da Nike da kuma kara sababbin abokan hulɗar kasuwanci guda shida.

  2. An dage gasar tenis a Saudiya, saboda rikicin gabas ta Tsakiya, Wasan kwallon tennis

    An dage babbar gasar tennis ta Six Kings Slam da aka tsara gudanarwa a Riyadh a Saudiyya mai dan karen kudi mai tsoka.

    An sanar da hakan, sakamakon tashin hankalin da yake faruwa a wasu wurare a Gabas ta tsakiya, ciki har da kai hari ga fifin sauka da tashin jirgin sama a Riyadh.

    Tun farko an tsara gudanar da gasar mai 'yan wasa shida daga ranar 21 zuwa da 24 ga watan Oktoba,

  3. Southgate ba ya ganin zai koma koyar da kungiyar Premier League, Premier League

    Gareth Southgate

    Wasan karshe da Gareth Southgate ya jagoranta a matsayin kocin Ingila shi ne karawar karshe a Euro 2024, inda suka sha kashi a hannun Sifaniya.

    Southgate, tsohon kocin Ingila ya ce ba ya ganin zai sake komawa horas da wata kungiyar kwallon kafa a gasar Premier League.

    Mai shekara 56 ya daina aikin horarwa tun bayan da ya yi murabus daga mukaminsa na kocin Three Lions bayan da ya kai su wasan karshe a Euro 2024, inda suka sha kashi a hannun Sifaniya.

    Southgate, wanda kuma ya kai Ingila wasan karshe a Euro 2020, bai taba horas da wata kungiyar kwallon kafa ba tun bayan shekara uku da ya shafe a Middlesbrough daga shekarar 2006.

    Tun bayan barin aikin kociyan Ingila, Southgate ya kuma yi aiki a kafafen yada labarai, sannan a farkon wannan shekarar ya jagoranci wani shirin BBC inda ya yi tattaki a fadin Birtaniya domin fahimtar kalubalen da matasa maza da yara maza ke fuskanta a fannin taka leda.

  4. Getafe ta yi tayin daukar Sancho wanda bai da kungiya, Getafe

    Jadon Sancho

    Getafe ta gabatar da tayi a hukumance domin daukar tsohon dan wasan Manchester United, Jadon Sancho.

    Mai shekara 26 a duniya ba shi da kungiya, bayan kwantiraginsa ya kare a lokacin bazara.

    Kungiyar Getafe ta Sifaniya, wanda ke matsayi na 14 a La Liga kuma tana buga gasar Europa Conference League a wannan kakar, na da kwarin gwiwar samun daukar dan kwallon domin ya taimaka maka da gogewarsa.

    An ce Sancho, wanda ya koma Manchester United fam miliyan 73 daga Borussia Dortmund a 2021, ya fi son komawa wata kungiyar da ba a Ingila take ba, amma har yanzu yana jiran a gabatar masa da kwantiragi mai tsoka ko daga ina ne.

    Sancho ya shafe kakar wasan da ta gabata a matsayin aro a Aston Villa, inda ya buga wasa 39, yayin da kungiyar, Unai Emery ta samu gurbin shiga gasar Zakarun Turai tare da lashe Europa League. Ya shiga wasan a matsayin canji a karshen nasarar da suka samu kan Freiburg.

    Ya kuma buga wasannin aro a Dortmund da Chelsea a cikin shekaru biyar da ya shafe a Manchester United.

    Komawarsa Chelsea a kakar 2024-25 ta kunshi sharadin saye na dindindin. Sai dai Chelsea ta biya tarar fam miliyan biyar domin mayar da Sancho Old Trafford bayan ya buga mata wasa 41.

    Sancho na ci gaba da wallafa bidiyon atisayensa a shafinsa na Instagram yayin da yake neman sabuwar kungiya. Hakan ya hada da ziyararsa ga kungiyar Flixton da ke matakin da ba na kwararru ba.

  5. Infantino ya ba Majalisar Fifa hakuri amma an ce har yanzu bai cancanci, Fifa

    Gianni Infantino

    Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino ya bai wa Majalisar Fifa hakuri kan shirinsa na sayar da wasu hakkokin gasar Kofin Duniya, amma an shaida masa cewa bai cancanci ya ci gaba da jagoranci ba matukar bai fitar da dukkan takardun da suka shafi lamarin tare da amsa muhimman tambayoyi ba.

    Majalisar Fifa ta yi zama a Zurich ranar Alhamis karo na farko tun bayan janye shirin sirri na Fifa Forward Enterprise (FFE) daga Infantino, wanda zai bai wa wani kamfanin masu zaman kansu domin saka hannun jari wani kaso daga hakkokin kasuwancin a wasannin da take shiryawa.

    Infantino ya kuma fuskanci karin tambayoyi kan jan katin Folarin Balogun, wanda daga baya ya buga gasar kofin duniya, an kuma bukaci ya yi bayani kan Kyautar Zaman Lafiya ta Fifa da ya bai wa shugaban Amurka da kuma tallafin da ake bai mambobin Fifa.

    Shugabar Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, Debbie Hewitt, wadda kuma mataimakiyar shugabar Fifa ce, ta ce bayan taron har yanzu akwai tambayoyi da dama da ba a samu amsarsu ba.

  6. Man United ta koma kamar wajen wasan kwaikwayo - Keane, Manchester United

    Lisandro Martinez

    Tsohon kyaftin, Roy Keane ya ce Manchester United ta koma kamar wajen wasan kwaikwayo bayan mai tsaron bayanta, Lisandro Martinez ya soki shugabannin kungiyar.

    Da yake magana bayan shan kashin da United ta yi da ci 2-0 a hannun Atletico Madrid a gasar Zakarun Turai ranar Talata, Martinez ya ce ya yi tsammanin za a zuba jari fiye da kima a cikin kungiyar a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara.

    A sakon da ya wallafa a kafafen sada zumunta ranar Laraba, ya ce ya yi wadannan kalamai ne cikin "fushi da takaici".

    Wannan rashin nasara a Madrid ya sa United ta kai wasanni biyar a jere ba tare da samun nasara ba, sannan ta ci wasa daya kacal cikin shida da fara kakar Premier League ta bana.

    Keane, da yake magana a shirin tattaunawa na The Overlap, ya ce bayanin da Martinez ya yi yana nuna halin da kungiyar din ke ciki baki daya.

    "Za a samu wasu magoya baya da za su ce ya yi daidai, sannan wasu kuma su ce bai kamata ya yi wadannan kalaman ba, musamman daga dan wasan da shi kansa bai yi abin kirki ba a lokacin da kungiyar ke fama da matsaloli," in ji shi.

    "Ina ganin idan aka dubi yanayin United din gaba daya a bayyane take akwai rudani sosai, kamar wani wajen wasan kwaikwayo.

    "Lokacin da kuke cikin mawuyacin hali irin wanda United ke ciki, abin da nake gani matsala shi shi ne lokacin da wasu 'yan wasa ke yin irin wadannan kalamai. Ya kamata mutum ya fara duban kansa kafin ya fito yana yin duk wadannan tsokaci."

  7. Barcola ya ci kwallo uku rigis, bayan Liverpool ta caskara LASK, Champions League

    Barcola

    Bradley Barcola ya zura ƙwallaye uku rigis, yayin da Liverpool ta lallasa LASK a wasan Champions League da aka ci ƙwallaye tara.

    Ƙungiyar Andoni Iraola ta fara samun cin kwallo a wasan da ta buga a Austria, bayan da Ronald Araujo ya ci kwallonsa ta farko a kungiyar.

    Mintuna biyu tsakani, Bradley Barcola ya ci kwallonsa ta farko shima a Liverpool tun bayan komawarsa daga PSG kan fam miliyan 123 a lokacin bazara.

    Barcola, wanda bai ci ƙwallo ko bayarwa a zura a raga ba a wasanninsa shida na farko, ya ƙara ta biyu daf da hutun rabin lokaci bayan da Florian Wirtz ya tsallake ya bar masa ƙwallon.

    Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Jeremie Frimpong ya sa aka koma 4-1.

    LASK ta farke ɗaya ta hannun Robert Ljubicic, amma mintuna uku bayan haka Barcola ya kammala cin ta uku rigis a karawar.

    Daga baya Lewis Koumas shi ma ya shiga cikin masu cin ƙwallaye yayin da Frimpong ya sake yin hannu a cin ƙwallo.

    Sai dai masu gida sun zare karin biyu da karawar ta koma 6-3.

    Iraola, wanda ya yi sauye-sauye huɗu daga ƙungiyar da ta sha kashi a hannun Manchester City ranar Lahadi, ciki har da hutar da Virgil van Dijk, yanzu ya jagoranci ƙungiyarsa zuwa nasara biyu cikin wasanni biyu a gasar Champions League.

    Liverpool za ta je gidan Brentford a gasar Premier League ranar Asabar, kafin ta karɓi baƙuncin Villarreal a Anfield ranar Talata mai zuwa.

  8. PSG ta je Etihad ta doke City 4-2 a Champions League, Champions League

    Champs

    Manchester City ta sha kashi a hannun zakarun Champions League Paris St-Germain a Etihad, bayan da PSG ta doke ta 4-2.

    City, wadda tsohon kocinta Pep Guardiola ya halarci kallon karawar, shi ne karon farko da ya je Etihad tun bayan barin kungiyar a karshen kakar da ta wuce.

    Desire Doue ne ya bude tamaula a minti na 13, kafin daga bisani ya samar da kwallo ta biyu ga Ousmane Dembele, wanda ya kai kai cikin raga mintuna biyu bayan haka.

    PSG ta ci gaba da tarwatsa City, inda Vitinha ya ci ta uku a minti na 32.

    Maresca ya yi sauye-sauye uku a hutun rabin lokaci, kuma City ta sauya fasali gaba daya bayan an dawo wasa, inda ta samar da damammaki masu yawa kafin Erling Haaland ya zare kwallo daya.

    Sai dai burin City na dawowa cikin wasan ya fuskanci koma baya a minti na 62 lokacin da Donnarumma ya fara tare bugun Akliouche, amma daga baya kwallon ta fada raga.

    Duk da haka, City ba ta yi kasa a gwiwa ba. Haaland ya ci kwallonsa ta biyu a fafatawar.

    A karshen wasan kuma, Donnarumma ya ceci bugun fenaritin da Ferran Torres ya buga masa.

  9. Sakamakon wasannin da aka buga

    Champ
  10. Wasannin da aka tashi, City 2-4 PSG

    Slovan Bratislava 0-3 Stuttgart

    Bodo/Glimt 1-0 Borussia Dortmund

    Shakhtar Donetsk 3-1 AEK Athens

    Roma 3-4 Real Madrid

    Real Betis 3-2 Porto

  11. An tashi wasan, Man City 2-4 PSG

    Wasa ne mai dan karen kalubale!

    PSG ta nuna dalilin da ya sa take zakarun Turai.

    Manchester City ta yi ƙoƙarin dawowa cikin wasan da jarumtaka, amma hakan bai wadatar ba a ƙarshe.

  12. Rudiger ya kara kwallo na hudu a ragar Roma, Roma 3-4 Real Madrid

    Mene ne sirrin Real Madrid da gasar Champions League ne haka?!

    Mintuna 15 da suka gabata ana cinta 3-1, amma yanzu sun samu kansu suna jagorantar wasa da cin 4-3 a dakikokin ƙarshe na lokacin wasa na yau da kullum.

    Abin da ya ƙara muni ga magoya bayan Roma shi ne cewa tsohon ɗan wasansu, Antonio Rudiger, ne ya ci ƙwallon daga kusa da raga.

  13. An bai wa PSG bugun fenariti, Man City 2-4 PSG

    Matheus Nunes ne ya kwanta ya nemi kwallo amma sai aka ce ya taba kafar Nuno Mendes da ta kai an bayar da fenariti.

    An kuma buga fenaritin da ta kai golan City ya kwanta ya tare.

  14. Endrick ya farke wa Madrid wasan, Roma 3-3 Real Madrid

    To, Roma za ta sake buƙatar zura ƙwallo idan tana son kawo ƙarshen shekara 19 da ta kwashe ba tare da doke Real Madrid ba, domin Endrick ya sa kai ya farke kwallo..

    Wasa ne mai kayatarwa matuƙa da aka ci Roma a daren nan.

  15. Champ
  16. Sakamakon wasannin da ake bugawa

    Slovan Bratislava 0-2 Stuttgart

    Bodo/Glimt 1-0 Borussia Dortmund

    Shakhtar Donetsk 1-1 AEK Athens

    Roma 3-1 Real Madrid

    Real Betis 2-2 Porto

  17. Aston Villa ta yi canji, Aston Villa 5-0 Fenerbahce

    Nicolas Jackson ba zai samu damar cin uku rigis ba, domin an canja shi wanda ya zura biyu a raga, kuma Tammy Abraham ne ya maye gurbinsa.

    Kamar kuma Ibrahim Mbaye ya ji rauni, amma an sauya shi, inda aka saka Alejandro Garnacho.

  18. Sakamakon wasannin da ake bugawa a yanzu haka, Champions League

    Slovan Bratislava 0-2 Stuttgart

    Bodo/Glimt 1-0 Borussia Dortmund

    Shakhtar Donetsk 1-1 AEK Athens

    Roma 3-1 Real Madrid

    Real Betis 2-2 Porto

  19. Man City 2-4 PSG, Erling Haaland

    Kwallo mai kyau daga wajen - Ayyoub Bouaddi wanda ya juya ya bai wa Erling Haaland shi kuma bai jira ba ya buga ta gefe ta fada raga.

    Yanzu haka Manchester City tana fatan rage kwallo biyu kan tashi.

  20. Aston Villa 5-0 Fenerbahce, Ross Barkley

    Aston Villa na huce haushi a kan kungiyar Turkiya

    Ibrahim Mbaye ya kutsa ta gefen hagu kafin ya samo Ross Barkley, wanda ya buga ƙwallo kai tsaye daga wajen akwatin bugun daga kai sai mai tsaron gida.

    Ƙwallon ta shiga raga daga wanda ya maye gurbin, Bartug Elmaz.