Shugaba Trump ya ce zai hana wasu manyan kafofin yada labarai na Amurka guda uku shiga Fadar White House nan take.
A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya zargi CNN da MS Now da Politico da ci gaba da yada "labaran karya," inda ya ce wannan matakin hana shiga martani ne kan hakan.
Wakiliyar BBC ta ce A baya shugaba Trump Ya dauki matakin shari'a kan wasu kafofin yada labarai da suka hada da New York Times da BBC, kuma akai-akai yana samun sabani tare da cin mutuncin yan jarida.
A cikin wata sanarwa, CNN ta bayyana matakin a matsayin cin zarafi da ya saba wa doka, tare da take hakkinsu na gudanar da aiki ba tare da cikas ko tsangwama daga gwamnati ba.