Barcelona ta ce 'yansanda sun yi amfani da karfi kan magoya bayanta
Rikicin Crystal Palace da Mateta na kara dagulewa
Arbeloa da Alonso abokan juna da za su fafata a Premier
Rahoto kai-tsaye
Muhammad Buhari Fagge
A nan gaba Baleba ka iya zama abin mamaki - Carrick
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United Michael Carrick ya yabawa sabon dan wasan kungiyar Carlos Baleba sosai, inda ya ce "Mun yi matukar farin cikin samun Carlos.
Yana da babbar damar ci gaba, kuma saye ne mai matukar kayatarwa a gare mu. Ingancin da yake da shi da kuma halayen wasansa suna kara daidaita tsarin tawagar da muke da ita.
Yana kawo karfi iri daban-daban da kuma sabbin zabuɓɓuka a cikin kungiyar.
Har yanzu akwai abubuwa da yawa da za su fito daga gare shi, don haka wannan abu ne mai kayatarwa a gare mu."
Baleba da Diallo ba za su buga mana wasa ba - Carrick, Manchester United da Ipswich (Lahadi, 16:30 BST)
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United, Michael Carrick, ya bayyana cewa sabon ɗan wasan da kulob ɗin ya saya, Carlos Baleba, yana fama da ƙaramin rauni a idon sawunsa, don haka ba zai kasance cikin tawagarmu ba na tsawon kusan makonni biyu masu zuwa.
Ya kuma tabbatar da cewa Amad Diallo har yanzu yana jinya, bayan da ɗan wasan na Ivory Coast ya bai buga wasan da United ta sha kashi a hannun Hull City a ƙarshen makon da ya gabata ba. Carrick ya ce yana fatan Amad zai dawo kafin hutun wasannin ƙasashe na wata mai zuwa.
A wani labarin mai daɗi ga Manchester United, Mason Mount ya dawo yin atisaye tare da tawagar. Carrick ne ya bayyana wannan labari "Babban labari mai kyau ne a gare mu."
Wannan na nufin Mount na ci gaba da murmurewa kuma yana matsowa kusa da komawa cikin tawagar farko ta Manchester United.
, Premier League
Asalin hoton, Getty Images
Yanzu mun koma kan harkokin Premier League, yayin da manyan kociyoyi da dama ke shirin bayyana ra'ayoyinsu gabanin wasannin karshen mako.
Nan ba da jimawa ba za mu ji ta bakin:
Xabi Alonso (Chelsea)
Michael Carrick (Manchester United)
Unai Emery (Aston Villa)
Keith Andrews (Brentford)
Gary O'Neil (Ipswich Town)
Daniel Farke (Leeds United)
Régis Le Bris (Sunderland)
Roberto De Zerbi (Tottenham Hotspur)
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu domin jin abin da za su ce game da shirye-shiryensu, sabbin labaran 'yan wasa da kuma hasashensu kan wasannin wannan karshen mako.
Ranakun wasannin Conference
Ranakun Wasannin Matakin League:
Rana ta 1: 15 Oktoba 2026
Rana ta 2: 22 Oktoba 2026
Rana ta 3: 5 Nuwamba 2026
Rana ta 4: 26 Nuwamba 2026
Rana ta 5: 10 Disamba 2026
Rana ta 6: 17 Disamba 2026
Ranakun Wasannin Zagayen Fitar da Gwani:
Wasannin Share Fagen Knockout: 18 da 25 Fabrairu 2027
Zagayen 'Yan 16: 11 da 18 Maris 2027
Kwata-fainal: 8 da 15 Afrilu 2027
Semi-fainal: 29 Afrilu da 6 Mayu 2027
Fainal: 2 Yuni 2027, a birnin Istanbul na Turkiyya.
Wasannin Hearts na Conference
Monaco (a gida)
Pafos (a waje)
Borac (a gida)
Trabzonspor (a waje)
Nordsjaelland (a gida)
Thun (a waje)
Asalin hoton, Getty Images
Wasannin Brighton a gasar Conference
Asalin hoton, Getty Images
Monaco (a gida)
Panathinaikos (a waje)
Universitatea Craiova (a gida)
Getafe (a waje)
Kauno Zalgiris (a gida)
Jablonec (a waje)
Ƙungiyoyin Burtaniya da ke Conference
Asalin hoton, Getty Images
Yanzu lokaci ya yi na jadawalin raba kungiyoyi na gasar Conference League.
Brighton and Hove Albion, wadda ke cikin tukunya ta biyu, ita ce kadai kungiyar Premier League da za ta fafata a gasar Conference League a wannan kakar wasannin.
Kungiyar Hearts ta kasar Scotland kuma tana cikin tukunya ta hudu.
Ranakun wasan Europa
Ranakun Wasannin Matakin League:
Rana ta 1: 16/17 Satumba 2026
Rana ta 2: 15 Oktoba 2026
Rana ta 3: 22 Oktoba 2026
Rana ta 4: 5 Nuwamba 2026
Rana ta 5: 26 Nuwamba 2026
Rana ta 6: 10 Disamba 2026
Rana ta 7: 21 Janairu 2027
Rana ta 8: 28 Janairu 2027
Ranakun Wasannin Zagayen Fitar da Gwani:
Wasannin Share Fage na Knockout: 18 da 25 Fabrairu 2027
Zagayen 'Yan 16: 11 da 18 Maris 2027
Kwata Fainal: 8 da 15 Afrilu 2027
Semi-fainal: 29 Afrilu da 6 Mayu 2027
Fainal: 26 Mayu 2027, a birnin Frankfurt na Jamus.
Wasannin Celtic na Europa
Asalin hoton, Getty Images
Marseille (a gida)
Benfica (a waje)
Ferencvaros (a gida)
Union SG (a waje)
Celta Vigo (a gida)
Omonia (a waje)
Besiktas (a gida)
Torreense (a waje).
Wasannin Sunderland na Europa
Asalin hoton, Getty Images
AZ Alkmaar (a gida)
AC Milan (a waje)
Dinamo Zagreb (a gida)
Anderlecht (a waje)
Jagiellonia (a gida)
Lech Poznan (a waje)
Levski Sofia (a gida)
Torreense (a waje)
Wasannin Bournemouth na Europa
Asalin hoton, Getty Images
AC Milan (a gida)
Real Sociedad (a waje)
Viktoria Plzen (a gida)
Sparta Prague (a waje)
Sturm Graz (a gida)
Celta Vigo (a waje)
Hapoel Beer Sheva (a gida)
Lillestrom (a waje)
Wasannin Crystal Palace na Europa
Asalin hoton, Getty Images
Real Sociedad (a gida)
Lyon (a waje)
Sparta Prague (a gida)
Red Bull Salzburg (a waje)
Lech Poznan (a gida)
Jagiellonia (a waje)
Hoffenheim (a gida)
Besiktas (a waje).
Bournemouth da Sunderland za su fafata da AC Milan
Manyan karawa biyu masu kayatarwa ga Bournemouth da Sunderland!
Sunderland za ta yi tattaki zuwa filin wasa na San Siro a Italiya, yayin da Bournemouth za ta karɓi baƙuncin ƙattun Italiya a filin Vitality Stadium.
Za a kawo cikakkun bayanai nan gaba, ciki har da waɗanda Celtic da Crystal Palace za su kara da su a gasar.
Ƙungiyoyin Burtaniya da ke Europa
Da farko, za a gudanar da zaben jadawalin gasar Europa League.
Kungiyar Celtic ta Scotland tana cikin Tukunya ta Biyu.
Kungiyoyin Premier League guda uku, wato Crystal Palace, Bournemouth da Sunderland, suna cikin Tukunya ta Uku.
Za a raba jadawalin Europa Conference
Asalin hoton, Getty Images
Ana gudanar da jadawalin raba kungiyoyi na gasar Europa League da kuma Conference League a birnin Monaco.
Za a gudanar da jadawalin ne a wani taro guda, inda za a fara da jadawalin Europa League kafin na Conference League.
Kamar yadda yake a gasar Champions League da Europa League, gasar Conference League za ta kunshi kungiyoyi 36.
Sai dai akwai bambanci, domin a gasar Conference League kowace kungiya za ta buga wasanni shida ne kacal a matakin league phase, maimakon wasanni takwas da ake bugawa a Champions League da Europa League.
Babu tabbas a makomar Fougerolles
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Fulham Alvaro Arbeloa ya ce har yanzu kungiyar ba ta tabbatar da tsananin raunin da Luc de Fougerolles ya samu ba, wanda ya tilasta masa fita daga fili a rabin na biyu na wasan da suka buga ranar Alhamis. Ya ce suna fatan raunin ba mai tsanani ba ne.
Ya kuma yi magana kan makomar dan wasan na kasar Canada a kungiyar:
"Yana bukatar ya rika buga wasa a kowane mako. Wata kila za mu dauki matsaya cikin kwanaki masu zuwa kan abin da zai kasance mafi alheri a gare shi."
Ko Arbeloa zai ƙaro 'yan wasa ?
Kocin Fulham, Alvaro Arbeloa, lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar sayen sabbin 'yan wasa kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa a mako mai zuwa, ya ce:
"Ina ganin za mu iya inganta kowace matsayi a cikin tawagar. Idan ka tambayi kowane koci, kowa yana tunanin zai iya inganta tawagarsa.
"Ni da na fara aiki kwanan nan, ina neman 'yan wasan da za su dace da tsarin wasan da nake son amfani da shi. Ina ganin muna shirye mu kara karfin tawagar a cikin 'yan kwanaki masu zuwa."
Fulham ce gaba
Asalin hoton, Getty Images
Abu na gaba ga Fulham shi ne tafiya mai nisa zuwa arewacin ƙasar domin karawa da Sunderland.
Sunderland ta yi fice sosai a komawarta gasar Premier League a kakar da ta gabata, inda har ta samu tikitin buga gasar Turai duk da cewa da yawa sun yi hasashen za ta koma Championship kai tsaye.
Tawagar Régis Le Bris ba ta bai wa Fulham wata matsala ba a kakar da ta gabata, inda Fulham ta yi nasara da ci 1-0 a gida a watan Nuwamba, sannan ta samu gagarumar nasara da ci 3-1 a filin Stadium of Light a watan Fabrairu.
A gaskiya ma, karo na ƙarshe da Sunderland ta doke Fulham a gasar Premier League ya kasance shekaru 17 da suka wuce, kuma wasanni shida kenan ba tare da nasara a kan Fulham ba, tun watan Janairun 2009.
Shin Arbeloa zai iya jagorantar Fulham zuwa wata nasara a wannan karon?
Brentford ta ɗauki Diouf daga West Ham £40m
Asalin hoton, Getty Images
Brentford ta kammala daukar mai tsaron bayan West Ham, El Hadji Malick Diouf, a yarjejeniya da darajarta za ta iya kaiwa fam miliyan 40.
Dan wasan bayan hagu dan kasar Senegal mai shekaru 21 ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar, tare da zabin kara masa shekara guda.
A karkashin yarjejeniyar, Brentford za ta biya fam miliyan 35 a farko, sannan karin fam miliyan 5 ta hanyar wasu sharuddan kari.
Diouf ya buga wasan farko na West Ham a Championship da Burnley, amma ba a saka shi cikin tawagar wasanni biyu na gaba ba yayin da ake ci gaba da tattaunawar cinikinsa.
Shi ne babban dan wasan baya da Brentford ta fi mayar da hankali wajen nema a wannan kasuwar musayar 'yan wasa. Tattaunawar ta tsaya cak a farkon bazarar nan kafin a sake farfado da ita a farkon wannan makon.
Diouf ya dawo Premier League bayan West Ham ta fadi daga gasar a kakar da ta gabata.
Haka kuma, sayar da shi ya kawo wa West Ham riba mai yawa, domin sun saye shi daga Slavia Prague kan fam miliyan 19 ne shekara guda da ta wuce.
Diouf ya buga wasanni 34 a West Ham a kakar da ta gabata, inda ya taimaka aka zura kwallaye biyar.
Kocin Brentford, Keith Andrews, ya ce "Shi dan wasa ne da ya dace da tsarin shekarun da muke nema, kuma har yanzu yana da babban damar ci gaba da inganta kansa."
Diouf kuma ya ce Andrews ya gamsar da shi cewa zai iya ci gaba da bunƙasa da inganta wasansa a Brentford.
'Muna buƙatar 'yan wasan da za su iya buga ko ina a fili'
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Everton, David Moyes, kan yadda ‘yan wasa ke taka rawar a wasu wuraren da ba inda suke bugawa ba na asali.
“Ina ganin idan kana da ƙaramin tawaga kamar tamu, kana buƙatar ‘yan wasan da za su kasance masu sassauci, su iya taka leda a wurare daban-daban kuma su amince da ayyuka daban-daban a lokuta mabambanta.
“Misali mai kyau shi ne yadda James Garner ya taka leda lokacin da aka mayar da shi matsayin mai tsaron baya na dama.
“Muna son ‘yan wasan da ba za su rika tambayar dalili ba, waɗanda za su kasance a shirye su yi aikin da aka ba su. Mun yi hakan sau biyu ko fiye a wasu lokuta. Harrison Armstrong ma ya taka leda a wrare daban-daban a wasu wasanni a kakar bara.
“Da yake muna da ƙaramar tawaga, dole ne mu sa ‘yan wasanmu su kasance masu iya taka rawar daban-daban, kuma abin farin ciki shi ne muna da kaɗan daga cikinsu da ke yin hakan.”