Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 21/09/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Shettima ya isa New York don halartar taron UNGA

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa birnin New York da ke Amurka don wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da jagorantar tawagar Najeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

    Wannan ne karo na uku da Shettima yake wakiltar Tinubu a babban taron na UNGA.

    Mai bai wa mataimakin shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, ya ce abubuwan da Najeriya za ta mayar da hankali a kai yayin taron za su kasance bisa muradun ƙasar, goyon bayanta ga haɗin gwiwar ƙasashe da kiraye-kirayen da Shugaba Tinubu ke yi na sake fasalin cibiyoyin duniya don su yi daidai da yanayin tattalin arziki da yawan al'umma na wannan zamani.

    "Saƙonmu a New York a bayyane yake. Najeriya ta yadda da haɗin gwiwa da ƙasashe amma dole ne masu gwamnati su zama wakilan kowa kuma masu adalci," in ji Shettima.

    Maitaimakin shugaban Najeriyar ya isa New York ne tare da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara da ƙaramar ministar kasafi, Dr Doris Uzoka-Anite da sauran manyan jami'an gwamnati.

    A birnin na New York kuma, Shettima ya samu tarba daga gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da ministar harkokin mata, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim da sauran manyan jami'an gwamnati da na diflomasiyya.

    A babban taron na UNGA, Shettima zai gabatar da jawabi inda zai bayyana matsayar Najeriya kan muhimman batutuwan da suka shafi duniya musamman kan zaman lafiya da kuma tsaro, ci gaba da bunƙasar tattalin arziki da kuma haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

  2. Za mu bai wa duniya mamaki idan Amurka ta sake kai mana hari - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran ta yi gargaɗi cewa idan har Amurka ta kuskura ta kai wa ƙasar hari, Iran za ta yi amfani da sabbin makamai tare da faɗaɗa yaƙin zuwa wasu yankunan da ba a kai wa hari ba.

    Kakakin IRCG, Hossein Mohebi ya ce idan dai har Amurka ta yi gangancin sake kai hari a Iran, to Iran ɗin kuwa za ta bai wa duniya mamaki.

    A cewarsa, Iran ta ƙera makamai tare da bunƙasa wasu dabarun yaƙi waɗanda ba ta yi amfani da sub a a yaƙin da ake a yanzu.

    Ya kira makaman a matsayin „makaman dabarun yaƙi” waɗanda Iran za ta yi amfani da su “idan buƙatar hakan ta taso” kuma “duniya za ta ga abin da zai faru”.

  3. Amurka da China sun tattauna kan matsalolin AI

    Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce Amurka da China sun tattauna wani shiri na haɗin gwiwa wajen faɗakarwa akan matsalolin da suka shafi ƙirƙirarriyar basirar AI.

    Mista Bessent ya bayyana cewa, ƙarƙashin wannan shiri, ƙasashen biyu za su iya sanar da juna idan aka samu wani lamari da ya shafi AI wanda zai iya zama barazana ga tsaron ƙasarsu.

    Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da Mataimakin Firaministan China, He Lifeng, a birnin New York.

    Tattaunawar sharar fage ce ga ganawar da ake sa ran shugabannin Amurka da China za su yi a mako mai zuwa a Fadar White House.

    Ko da yake babu wata sanarwa daga gwamnatin China game da tattaunawar, a baya dai shugaba Xi Jinping na China ya yi kira da a samar da wani tsari na ƙasa da ƙasa da zai rinka sanya idanu a kan harkokin ƙirƙirarriyar basira ta AI.

  4. An miƙa mutum 18 ga Amurka kan zargin hannu a kisan Shugaba Moise

    Jami’an Amurka sun ce an tafi da mutane 18 da ake zargi da hannu a kisan tsohon shugaban ƙasar Haiti, Jovenel Moïse, shekaru biyar bayan kisan nasa zuwa jihar Florida domin fuskantar shari’a.

    Wakilin BBC ya ce an miƙa wasu tsoffin sojojin Colombia 17 da kuma wani babban jami'in gwamnatin Haiti ga gwamnatin Florida domin su fuskanci tuhuma kan kisan tsohon shugaban ƙasar na Haiti.

    Ana zargin waɗannan mutanen da hannu a kisan tsohon shugaban ƙasar Jovenel Moïse, wanda aka harbe har lahira a gidansa da ke birnin Port-au-Prince a shekarar 2021.

    An harbe Mista Moïse har lahira a gidansa da ke birnin Port-au-Prince ne wanda wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai, yawancinsu waɗanda ake zargin ‘yan Kolombiya ne suka aikata.

  5. 'Za a rushe gini sama da 250 da hare-haren Isra'ila suka lalata a Gaza'

    Jami’ai a Gaza sun sanar da shirye-shiryen kwashe mutane tare da rusa fiye da gine-gine 250 da hare-haren da Isra’ila ta kai suka lalata, saboda fargabar cewa za su iya ruftawa a kowanne lokaci.

    An ɗauki matakin sakamakon yawaitar rushewar gine-ginen da suka lalace ciki har da wani gini da ya rufta a ranar Laraba, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 21.

    Sai dai hukumomin sun yi gargaɗin cewa shirin na fuskantar manyan ƙalubale, ciki har da ƙarancin manyan injinan aikin gini saboda killace yankin da Isra’ila ta yi, da kuma rashin isasshen fili da za a tsugunnar da waɗanda suka rasa matsugunansu.

    Wakiliyar BBC ta ce ma’aikatar kula da gidaje ta Gaza ta bayyana kusan gine-gine 3,000 a matsayin masu matuƙar haɗari, saboda irin ɓarnar da suka yi fama da ita a yaƙin da ake yi tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hamas.

  6. Salam Alaikum!

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kowace rana, barka da warhaka.

    Da fatan mun wayi gari lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a duniya - musamman a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Za ku iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta – Fesbuk da X da kuma Instagram inda a nan ma muka wallafa ƙarin labarai da bidiyo.

    Sai ku kasance tare da mu.