Jana'izar Khamenei da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kai tsaye dangane da jana'izar Ayatollah Ali Kahamenei da sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 07/07/2026
An kai wa jiragen ruwa uku hari a Mashigar Hormuz cikin awa 24
Hukumar tsaron ruwa ta Birtaniya ta ce an kai wa wasu tankoki guda uku hari a kusa da mashigar Hormuz cikin sa'o'i 24 da suka wuce.
Daya daga cikin jirgin ruwan na Qatar ne dake ɗauke da gurɓatacciyar iskar gas da wani jirgin marar matuƙi ya ƙona.
Qatar ta zargi Iran da kai harin amma babu dai wani ƙarin haske daga Tehran.
A watan da ya gabata ne Iran ta amince ta sake buɗe mashigar a wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka.
Me ya sa ake taƙaddama kan sanya hijabi a makarantun Najeriya?
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Ƴan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da wani hukuncin Kotun Ɗaukaka a Najeriya da ya hana ɗalibai sanya hijabi a wata makarantar sakandire da ke Ibadan. Ga cikakken bayani game da wannan batu.
ICPC ta kama likitan Nasir El-Rufai
Asalin hoton, Nasir El-Rufai/Facebook
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya ta ce ta kama likitan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke tsare a wajenta saboda saɓa ƙa'idojin duba lafiyarsa da kotu ta bayar.
Hukumar ta ce ta kama Farfesa Bello Abubakar, bisa zarginsa ba da bayanan ƙarya a yayin da ake bincike.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, John Odey, ya fitar, ICPC El-Rufai ya ƙi amincewa ya halarci zaman kotun da ya kamata a gudanar a Kaduna a ranar 6 da 7 da 8 ga watan Yuni, inda ya nace sai an haɗa shi da likitansa.
Sakamakon hakan ne hukumar ta ce ta ce ta amince da duba lafiyar tsohon gwamnan kamar yadda kotu ta yi umarni.
Hukumar ta ƙara da cewa kamar yadda iyalansa suka buƙata, jami'anta sun fita daga ɗakin a lokacin duba shi a babban asibitin ƙasa domin mutunta sirrinsa.
Sai dai ICPC ta ce daga bisani ta gano wasu hotuna da wani abokin siyasar El-Rufai, Isa Ashiru Kudan, ya wallafa a shafinsa na Facebook, waɗanda ke nuna tsohon gwamnan tare da wasu baƙi, ciki har da likitansa, a lokacin da aka ware domin duba lafiyarsa.
Hukumar ta ce hakan ya nuna cewa an yi amfani da damar ziyarar jinya wajen yin wasu abubuwan da ba su cikin abin da kotu ta amince da shi.
ICPC ta kuma ce za ta sanar da kotu abin da ta kira saɓa wa umarninta da aka yi.
Sanarwar ta ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da tsare Farfesa Bello Abubakar domin ci gaba da bincike kan zargin da ake masa.
Tinubu ya umarci ICPC ta yi bincike kan kafa hukumar bogi
Asalin hoton, Bola Tinubu/FB
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gudanar da bincike kan wata hukuma ta bogi da ake zargin an ƙirƙire ta ba tare da sahalewar fadar shugaban ƙasar ba.
A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ƙasar ya umarci ICPC ta kammala binciken tare da gabatar masa da rahoto cikin kwanaki 30.
Sanarwar ta ce umarnin ya biyo bayan gano cewa majalisar bai wa shugaban shawara kan tattalin arziki da zuba jari daga ƙasashen ƙetare (PFIPC) hukuma ce ta bogi da ba a taɓa kafa ta ba.
Gwamnatin ta ce mutumin da take zargi mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya riƙa bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar, yana kuma iƙirarin cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa shi.
Sanarwar ta ce binciken zai mayar da hankali kan zargin ƙirƙirar takardun naɗi da sauran takardun gwamnati na bogi, da kuma amfani da sunan shugaban ƙasa wajen neman ganawa da hukumomi da tattaunawar diflomasiyya.
Haka kuma ICPC za ta binciki zargin buɗe asusun banki na CBN da sahalewar wasu hukumomin gwamnati ta hanyar amfani da takardun da ake zargin na bogi ne.
"Dole ne a kare martabar fadar shugaban ƙasa da cibiyoyin gwamnatin tarayya daga masu yin sojan gona, masu ƙirƙirar takardu na bogi da masu amfani da sunan gwamnati ba bisa ƙa'ida ba," in ji sanarwar.
Gwamnatin ta ƙara da cewa duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a lamarin, za a hukunta shi bisa tanadin doka.
Majalisar Dattawan Najeriya na so a daina yi wa tubabbun Boko Haram afuwa
Asalin hoton, NALTF
Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin gyaran hali da sake haɗa tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al'umma.
Majalisar ta cimma wannan matsaya ne a zamanta na ranar Talata, sakamakon ci gaba da sace-sace da kashe jami'an soji da ƴanbindiga ke yi a ƙasar.
Shugaban kwamitin majalisar kan rundunar sojin Najeriya, Sanata Abdulaziz Yar'Adua, mai wakiltar Katsina ta tsakiya ne ya fara gabatar da ƙudurin kan abubuwan da ke faruwa na rasin tsaro a ƙasar.
Ya ce hare-hare da sace-sace da kashe jami'an tsaro masu aiki da kuma waɗanda suka yi ritaya na ƙaruwa, musamman Manjo Janar Rabe Abubakar da ya mutu a hannun ƴanbindiga a makonnin da suka gabata.
Bayan gabatar da ƙudurin ne kuma Sanata Joseph Ikpea daga Edo ta tsakiya ya buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin yi musu afuwa da maida su cikin al'umma.
Da yake goyon bayan ƙudurin, Sanata Adams Oshiomhole, mai wakiltar Edo ta Arewa, ya ce, "Hankali ba zai ɗauka ba, a ce ana yi wa masu aikata laifuka afuwa sannan a sake yi musu gyaran hali. Saboda haka ina goyon baya."
Daga bisani majalisar ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da buƙatar inda ta umarci kwamitocinta masu kula da harkokin tsaro su ƙara sa ido kan ayyukan hukumomin tsaro tare da tabbatar da cewa suna ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan matsalolin a ƙasar.
Abin da ya sa na yaɗa sunayen yaran da aka sace - Davido
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Fitaccen mawaƙin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya ce kishin ƙasa ne ya sa ya saka wata riga ta musamman mai ɗauke da sunayen yaran da aka sace yayin wani biki da ya je. Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce a ƙasar.
Ban taɓa haɗuwa da Adeyemi ba — Gbajabiamila
Asalin hoton, Femi Gbajabiamila/X
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya musanta cewa ya taɓa haɗuwa ko yin wata mu’amala da Adeniyi Adeyemi, wanda ya bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar PFIPC.
Adeyemi wanda gwamnatin tarayyar ƙasar ta ce ya naɗa kansa a matsayin shugaban majalisar bai wa shugaban shawara kan tattalin arziki da zuba jari daga ƙasashen ƙetare, ya zargi Gbajabiamila da yin barazana ga rayuwarsa bayan turka-turka ta ɓarke tsakaninsu.
Sai dai Gbajabiamila ya ce ba shi da wata alaƙa ko mu’amala da Adeyemi a baya.
A cikin wata wasiƙa da lauyansa, Kemi Pinheiro ya aika wa Adeyemi a madadinsa, Gbajabiamila ya buƙaci Adeyemi ya janye kalamansa tare da neman afuwarsa a gidajen jaridu biyar na ƙasar da kuma shafukan sada zumunta da aka yaɗa zarge-zargen.
"Wanda mu ke wakilta [Gbajabiamila] ya shaida mana cewa, ba ka taɓa haɗuwa da shi ba, ba ka taɓa yin wata mu’amala, ko wata hulɗa ta sirri ko aiki da shi ba,” in ji Lauyan.
A cikin wasiƙar, lauyoyin Gbajabiamila sun ce idan Adeyemi bai cika waɗannan buƙatu cikin sa’o’i 72 ba, za su ɗauki matakin shari’a a kansa, ciki har da shigar da ƙara kan zargin ɓata suna.
Sun ce za su kuma nemi diyyar Naira biliyan 10, tare da umarnin kotu da zai tilasta masa bayar da haƙuri da kuma dakatar da sake yaɗa irin waɗannan zarge-zarge.
Wannan rikici ya samo asali ne daga zarge-zargen da Adeyemi ya yi a wani taron manema labarai da ya gudanar a watan da ya gabata, inda ya yi ikirarin cewa Gbajabiamila na da hannu wajen tafiyar da harkokin PFIPC.
An kai gawar Ali Khamenei birnin Najaf domin jana'izarsa a Iraƙi
An kai gawar tsohon jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, zuwa birnin Najaf da ke Iraƙi domin gudanar da jana'izarsa.
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya isa birnin Najaf domin halartar bikin jana'izar.
Kamfanin dillancin labaran Iran ta IRNA ta ce bayan halartar taron, zai kuma gana da Firaministan Iraki.
Za a fara gudanar da jana'izar Khamenei a birnin Najaf, daga bisani kuma a ci gaba da ita a birnin Karbala, waɗanda ke daga cikin muhimman wuraren addini na mabiya Shi'a.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya rawaito cewa, baya ga Pezeshkian, babban ɗan marigayi Khamenei, Mostafa Khamenei, da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, na cikin waɗanda za su halarci jana'izar a Iraki.
Bayan kammala bukukuwan jana'izar a Iraki, ana sa ran za a binne Ali Khamenei ranar Alhamis a haramin Imam Reza da ke birnin Mashhad, garinsu na asali.
An kama masu zanga-zanga a Kenya
An kama mutane da dama a Nairobi, babban birnin Kenya, bayan sun tsallake shingen ’yan sanda domin shiga wata zanga-zangar da gwamnati ta haramta.
Masu fafutukar kare dimokuradiyya ne suka shirya zanga-zangar domin tunawa da cikar shekara daga zanga-zangar neman sauyi ta shekarar 1990.
’Yan sanda sun ce zanga-zangar ba ta halatta ba, saboda masu shirya ta ba su sanar da hukumomi tun da wuri ba, kamar yadda doka ta tanada.
An baza jami’an tsaro da dama a sassa daban-daban na Nairobi, tare da kafa shingayen bincike a manyan hanyoyin shiga birnin.
A bara irin wannan zanga-zanga ta rikide zuwa tashin hankali, inda akalla mutum talatin da takwas suka rasa rayukansu
Xi Jinping ya nemi a gudanar da ayyukan ceto bayanan matsanancin yanayi
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar China , Xi Jinping, ya yi kira da a gudanar da ayyukan ceto cikin gaggawa da dukkan ƙarfi, bayan da matsanancin yanayi a sassa daban-daban na ƙasar ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 15 tare da raba dubban mutane da muhallansu.
A lardin Hubei da ke tsakiyar ƙasar, munanan guguwa da ruwa sama sun afakawa birane da gundumomi da dama, inda suka kashe aƙalla mutum takwas.
A lokaci guda kuma, mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa da guguwar Typhoon Maysak ta haddasa sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum biyu a yankin Guangxi da ke kudancin ƙasar.
A lardin Gansu da ke yammacin kasar kuwa, an ba da rahoton cewa zaftarewar ƙasa a wani yanki mai tsaunuka ta binne fiye da mutum 30.
Yadda aka tsara jana'izar Ayatollah Ali Khamenei
An kama mahaifin Adeyemi Adeniyi: Me dokar Najeriya ta ce?
Asalin hoton, Prince Adeniyi Adeyemi/Instagram
Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da rahotonnin kamen da ake zargin jami'an tsaro sun yi wa mahaifi da dangin shugaban hukumar PFIPC da ake zargi ta bogi ce.
A ranar Litinin ne bayanai suka ce ƴansanda sun kai samame gidan Prince Adeniyi Adeyemi da ke Ogbomoso na jihar Oyo tare da kama wasu daga cikin danginsa ciki har da mahaifinsa.
A baya-bayan nan ne dai aka zargi Prince Adeniyi Adeyemi da kafa sabuwar hukumar gwamnati ta bogi, wadda kuma har ta samu kaso a kasafin kuɗin ƙasar na 2026.
Bayanai sun ce an kama dangin nasa ne a lokacin da suka ziyarci gidan Adeyemi a ranar Litinin.
Sai dai babu bayani dangane da ko jami'an tsaron sun kama dangin Prince Adeyemi bisa hannu a laifin da ake zargin ɗan uwan nasu da aikatawa.
A cikin wannan muƙala mun duba abin da dokokin Najeriya suka tanada kan kama wani bisa laifin ɗan'uwansa.
Trump ya isa Turkiyya domin halartar taron shugabannin NATO
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya isa birnin Ankara na ƙasar Turkiyya domin halartar taron ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO, inda Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya tarbe shi.
Ana sa ran Trump zai gana da Erdogan kafin a fara liyafar shugabannin ƙasashen NATO da za a gudanar a daren Talata, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Babban taron shugabannin ƙasashen NATO kuma zai gudana ne a ranar Laraba.
Rahotanni sun ce shugabannin ƙasashen ƙungiyar na fatan samun goyon bayan Trump, wanda a watannin baya ya riƙa sukar NATO da kuma yadda Amurka ke ɗaukar nauyin tsaron ƙungiyar.
A don haka ne ma, ƙasashen suka yi alƙawarin ƙara yawan kuɗaɗen da suke warewa fannin tsaro.
Taron na bana ya zo ne shekara guda bayan da mambobin NATO suka amince da ƙara yawan kuɗaɗen tsaro zuwa kaso biyar cikin ɗari na yawan kuɗin shiga na ƙasashensu sakamakon matsin lambar Trump.
Kafin isowar Trump, ƙawayen NATO sun sanar da sabbin yarjejeniyoyin sayen makamai na biliyoyin daloli, tare da jaddada ƙudirin ƙara kasafin kuɗin tsaro, matakin da ake ganin na da nufin kwantar masa da hankali kan yadda Turai ke taka rawa wajen tsaron ƙungiyar.
An kwashe ma'aikatan jirgin dakon gas na Qatar bayan kai masa hari a Mashigar Hormuz
An kwashe ma'aikatan wani jirgin dakon iskar gas na ƙasar Qatar bayan da wani abu da ba a tantance ko menene ba ya harbi jirgin yayin da yake wucewa ta Mashigar Hormuz.
Kamar yadda wasu majiyoyi uku suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, jirgin ya aika da saƙon neman agajin gaggawa bayan abin ya harbi ɓangaren hagun sashen jirgin.
Sun ƙara da cewa harin ya yi wa jirgin mummunar ɓarna, sai dai har yanzu ba a tabbatar da cikakken yanayin da yake ciki ba.
Tun da farko, an ruwaito cewa wani jirgin dakon man fetur ma ya gamu da irin wannan hari yayin da yake ratsawa ta Mashigar Hormuz daga ɓangaren Oman.
Har zuwa yanzu babu wata ƙungiya ko ƙasa da ta ɗauki alhakin harin.
Za a kai gawar Ali Khamenei zuwa Najaf bayan kammala jana'iza birnin Qom
Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran za a tafi da gawar marigayi Ayatollah Ali Khamenei zuwa birnin Najaf na ƙasar Iraki a yau, bayan kammala jana'izar da ake yi masa a birnin Qom na Iran.
Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ruwaito cewa babban ɗan marigayin, Mustafa Khamenei, da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, da Kakakin Majalisar Dokokin ƙasar, Mohammad Baqer Qalibaf, za su halarci jana'izar da za a gudanar a Najaf.
Rahotanni sun ce za a gudanar da bukukuwan jana'izar Khamenei a ranar Laraba a biranen Karbala da Najaf na Iraki.
Bayan kammala jana'izar a Iraki, ana sa ran za a mayar da gawarsa Iran domin binne ta a ranar Alhamis a harabar Hubbaren Imam Reza da ke garinsu na haihuwa, Mashhad.
Macron yana cikin ƙoshin lafiya bayan wata fashewa a Damascus
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Faransa ta sanar da cewa Emmanuel Macron na cikin koshin lafiya, bayan rahotonnin AFP cewa an ji ƙarar fashewar wani abu a birnin Damascus a ranar Talata.
Hotunan da aka fitar daga Damascus sun nuna hayaki mai ƙauri a kusa da otal ɗin da Emmanuel Macron ya sauka a lokacin ziyararsa zuwa Syria.
Rahotanni daga Syria sun ce aƙalla mutum 18 sun jikkata sakamakon fashe-fashen da suka auku a tsakiyar Damascus.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa BBC cewa fashe-fashen sun samo asali ne daga bama-bamai biyu da aka ƙera da hannu kuma sun jikkata mutane da dama.
Kafofin yaɗa labarai na Syria sun ruwaito cewa jami’an ‘yan sanda huɗu na cikin waɗanda suka jikkata a lamarin.
A halin yanzu Mista Macron yana babban birnin Syria, inda yake tattaunawa da Shugaba Ahmed Sharaa a fadar shugaban ƙasa, a cewar wata sanarwa daga Fadar Elysee.
Fadar Elysee ta kuma ce ziyarar “na ci gaba kamar yadda aka tsara.”
Mista Macron shi ne shugaban wata ƙasa na farko daga ƙasar Tarayyar Turai da ya ziyarci Syria tun bayan da sabuwar gwamnati ta hau mulki.
Za mu iya gamawa da Iran a ƙanƙanin lokaci amma na zaɓi mu tattauna - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce farashin mai bai tashi sosai ba duk da rufe mashigin ruwa na Hormuz, yana mai cewa: “Mun karɓi mai mai yawa daga gare su. Mutane ba su san haka ba, kuma duk wannan ya faru ne cikin wata ɗaya da rabi kacal.”
A wata hira da ya yi ta talabijin, Shugaban Amurkan ya sake jaddada cewa ya lalata jiragen ruwan yakin Iran da kuma dukkan jiragen saman rundunar sojin saman Iran.
“Daga ƙarshe sun fahimci cewa ba su da na’urorin hangen jirage na rada kuma, domin an lalata tsarin radarsu. Saboda haka muka kai musu hari cikin dare da kuma a cikin duhu.”
“Rundunar ruwanmu mai ƙarfi ta ƙaƙaba mafi girman takunkumi da aka taɓa gani, inda suka yi wa tashoshin Iran ƙawanya kuma tsawon watanni biyu babu wani jirgin ruwa da ya iya ketare ƙawanyar. Daga baya muka kusan cimma yarjejeniya, sai muka sassauta ƙawanyar. Ban sani ba, wataƙila za mu iya cimma yarjejeniya.”
Mista Trump ya nace cewa: “Za mu yi nasara ta kowace hanya ce. Ko dai mu cimma yarjejeniya, ko kuma mu kammala lamarin.”
Ya ce kammala murƙushe Iran abu ne mai sauƙi: “Ba zai yi wahala mu gama da ita ba. Amma tabbas, na fi son a samu yarjejeniya, domin ba na son mutane miliyan 91 su fuskanci illa.”
“Za mu iya rusa gadojinsu cikin sa’a guda. Za mu iya lalata cibiyar samar da wutar lantarkinsu. Dukkan waɗancan tashoshin wutar lantarki da suka gina manyan, kyawawa kuma na zamani. Suna da kuɗi da yawa a baya, amma yanzu ba su da kuɗi. Ba mu ba su ko sisin kwabo ba, amma za mu iya katse musu wutar lantarki da kuma lalata tashoshin samar da wutar nasu.”
A kwanaki kaɗan da suka gabata, Mista Trump ya ce ya bai wa Iran mako guda domin ta binne tsohon shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
An nemi Iraniyawa su shigar da ƙorafi kan raɗaɗin rashin Khamenei
Asalin hoton, Getty Images
Ministan Shari'a na Iran: Mutane na iya shigar da ƙara saboda "raɗaɗin tunani da na zuciya da rashin jagora ya haifar."
Ministan Shari'a na Iran, Amin Hossein Rahimi, ya bayyana cewa Ma'aikatar Shari'a da gwamnati sun samar da dukkanin hanyoyin da suka dace domin mutane su shigar da ƙorafe-ƙorafe da ƙara dangane da "lahanin tunani da na ƙwaƙwalwa da rasuwar jagoran ƙasar ta haifar musu".
Ya ce ana iya yin hakan ta hannun lauyoyi ba tare da biyan kuɗi ba, a gaban hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa.
"Ana ci gaba da bibiyar laifukan da maƙiya suka aikata a ƙungiyoyi da kotunan ƙasa da ƙasa da kuma hukumomin cikin gida, kuma an tattara hujjoji masu ƙarfi kan lamarin."
Ya ƙara da cewa:
"Bisa doka, hukumomin shari'a na Jamhuriyar Musulunci ta Iran suna da ikon binciken waɗannan laifuka, kuma akwai yiwuwar gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata su, ciki har da gwamnatin Amurka da kuma gwamnatin Isra'ila."
Ministan ya kuma bayyana akwatin gawar jikar Ali Khamenei a matsayin "shaidar irin zaluncin da aka yi wa jagoran Iran", inda ya kwatanta lamarin da Ali Asghar, ɗan Imam Husaini bn Ali, Imam na uku a wajen mabiya Shi'a.
A ƙarshe, Rahimi ya jaddada cewa "Wannan wata fafatawa ce ta shari'a da za ta gudana tare da sauran fannoni na tinkarar waɗanda suka aikata wannan hari."
An gabatar da hujjoji a gaba kotu kan Charlie Kirk
Asalin hoton, Getty Images
Masu gabatar da ƙara a jihar Utah ta Amurka sun gabatar da hujjoji a gaban wata kotu gabanin shariar da za a yiwa mutumin da ake zargi da kashe fitaccen mai ra'ayin rikau din nan , Charlie Kirk.
Suna ƙoƙarin gamsar da alƙali cewa suna da shaidar da za su iya amfani da ita wajan gurfanar da wanda ake zargin, Tyler Robinson, a gaban kotu domin fara shari'a.
Har yanzu Robinson bai bayyana ko ya amsa ko ya musanta zargin da ake yi masa ba.
Mista Kirk, wanda ke da kusanci da Shugaba Trump, ya mutu ne bayan an harbe shi yayin da yake jawabi ga ɗalibai a harabar wata jami'a a watan Satumban bara.
An fara gudanar da jana'izar Khamenei a birnin Qom.
Asalin hoton, Getty Images
Bayan kammala jana'izar a hukumance da aka yi wa tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci a Tehran, tare da kai akwatin gawarsa da kuma na wasu daga cikin 'yan iyalansa da aka kashe tare zuwa birnin Qom, an fara gudanar da jana'izarsa a hukumance a wannan birni da ke lardin tsakiyar ƙasar.
Kamar yadda aka ruwaito, Ayatullah Javadi Amoli ne ya jagoranci sallar jana'izar a Masallacin Jamkaran da ke Qom, sannan aka fara gudanar da jana'izar a gaban dubban magoya bayan marigayi Ali Kahamenei
Bayan wannan taro, za a gudanar da wani makamancin taron jana'izar a birnin Najaf bayan an kai gawarwakin zuwa Iraki.
Daga bisani kuma, za a kammala jerin jana'izar a birnin Mashhad ranar Alhamis.