Ana fargabar gurɓacewar muhalli daga ayyukan haƙo mai a DR Congo

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi gargaɗin cewa ayyukan hako mai da kamfanin Perenco ke gudanarwa a yankin Muanda da ke lardin Kongo a tsakiyar Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo na iya zama barazana ga lafiyar al'umma da muhalli.
Rahoton ya ce hayaƙin da kamfanin ke fitarwa da kuma ƙona tarkacen mai sun gurɓata ingancin iska, yayin da malalar mai daga rijiyoyi da bututun mai ta gurɓata koguna da ƙasa.
Mazauna yankunan sun ce suna fama da matsalolin numfashi, ciwon ƙirji da tashin zuciya, kuma suna danganta waɗannan matsaloli da ayyukan kamfanin.
Sai dai Perenco ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa binciken da aka yi na da kura-kurai.
Kamfanin ya ce ya zuba jari wajen rage gurɓacewar muhalli da kuma tallafa wa ayyukan kiwon lafiya, tare da bayyana cewa ya dakatar da fitar da hayaƙin gas a wurare sama da 200 kuma yana aiki tare da hukumomin Kongo.
Gwamnatin Kongo, wadda ta ba da umarnin a gudanar da binciken muhalli kan ayyukan kamfanin tun ƙarshen shekarar 2024, har yanzu ba ta fitar da sakamakon binciken ba.
Human Rights Watch na kira ga gwamnati da ta bayyana sakamakon binciken tare da ɗaukar matakan kare lafiyar jama'a.
Perenco, wanda shi ne kaɗai kamfanin da ke samar da mai a Kongo, na gudanar da ayyuka a kan tudu da kuma a teku a bakin gaɓar ƙasar mai tsawon kilomita 37.


















