Rasha ta ce ta lalata jirage marasa matuƙa 605 da Ukraine ta harba cikin dare
Ma'aikatar Tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kakkabo jiragen marasa matuƙa 605 na Ukraine a hare-haren da ta kai cikin daren Laraba.
A cewar ma'aikatar, an daƙile hare-haren ne a yankuna da dama, ciki har da Moscow da Yaroslavl, inda ɗaya daga cikin manyan matatun man Rasha, Slavneft-Yanos, take.
Rahotanni sun ce an ga baƙin hayaƙi mai yawa na tashi sama a birnin Yaroslavl bayan harin da jiragen marasa matuƙa da Ukraine suka kai.
Gwamnan yankin, Mikhail Evraev, ya ce wannan shi ne hari mafi girma da yankin ya taɓa fuskanta, kumaan lalata jirage marasa matuƙa 92 a yankin kaɗai.
A gefe guda kuma, jami'an Ukraine sun ce hare-haren Rasha sun kashe mutum uku a birnin Balakliya, yayin da wasu 12 suka jikkata a yankin Sumy.