A nan muka kawo karshen shirin
A nan muka kawo muku karshen shirin da fatan za ku tara a sauran wasannin gasar cin kofin duniya 2026 da za mu ke kawo muku kai tsaye.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada nake muku asuba ta gari.
Mai gabatarwa Mohammed Abdu da taimakon AI
A nan muka kawo muku karshen shirin da fatan za ku tara a sauran wasannin gasar cin kofin duniya 2026 da za mu ke kawo muku kai tsaye.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada nake muku asuba ta gari.

Asalin hoton, BBC Sport

Asalin hoton, BBC Sport
An tashi wasan farko a rukuni na uku da ci 1-1.
Moroko mai wakiltar Afirka ta samu maki ɗaya a wasan farko.
Afirka ta Kudu kuwa ta yi rashin nasara a hannun Mexico a wasan farko.
Saura kasa takwas daga Afirka daga 10 da za su wakilci Afirka su buga wasanninsu.
Har munci minti bitar daga goma da aka kara, saura biyar a tashi daga karawar.
Kamar dai tawagogin biyu sun gamsu da raba maki a wannan karawar.
Fabinho ya yi keta koda yake daga tsakiyar fili ne, kuma ba a bashi katin gargaɗi ba mai ruwan ɗorawa.
An samu bugun kusurwa daga Moroko ta kuma buga, amma dai ba ta amfana da wannnan damar ba, ƙwallo ta fita jifa gidan Brazil.
An samu bugun kusurwa da Brazl ta yi ta wajen Cunha, amma babu hatsari Moroko ta fitar da ƙwallon ba wata matsala.
An yi karin minti 10, Kda ka je ko ina, domin komai zai iya faruwa a cikin minti 10 a wasan tamaula.
Yassine Bounou ya ci gaba da tsare ragar Morocco, duk da ɗan ciwo da ya ji a kafaɗa, kuma yanzu lokaci ya ja sosai.
Carlo Ancelotti ya canja ɗan wasa na biyar a karawar, inda Danilo Santos, wanda ya taka leda shekara biyu tare da Nottingham Forest ya canji Bruno Guimaraes na Newcastle.

Asalin hoton, Getty Images
Raphinha ya buga kwallon zuwa ga Vinicius Jr daga kusa da gefen layi, amma Yassine Bounou na kwallon Morocco ya fahimci abin da ake son yi ya fito ya samu ƙwallon..
Chemsdine Talbi ya buga ƙwallo da kafar dama, amma babu wani ɗan Moroko da zai ɗauka.
An sanar da waɗanda suka shiga filin wasa a karawar Brazil da Morocco sun kai 80,663.
Shin za su iya ganin wadda za ta haɗa maki a karawar nan ko kuma haka za su tashi?
Yanzu dai Moroko ne suka yi bani in baka tun daga gurbin masu tsaron baya ana wani gudu da ƙwallo har kusa da ragar Brazil, daga karshe an fitar da ƙwallon ba wani haɗari.
An buga kwallon daga can gefe ta wuce ta cikin gidan Moroko, amma babu wani ɗan Brazil da ya kamata ya yi wani abu, kenan ƙwallon ya yi faɗi.
A wannan lokacin ana fuskantar yanayi mai zafi a Amurka, hakan ya sa ya zama wajibi alkalin wasa ya bayar da damar aje a sha ruwa a hutu a goge gumi, sannan a ci gaba da taka leda.
Fabinho ya ji rauni a lokacin da aka bugi bakinsa, yana da kyau ya je a duba lafiyarsa.
Morocco ta yi canja ƴan wasa biyu, inda Azzedine Ounahi da Bilial El Khannouss suka maye gurbin mai taka leda a Sunderland, Chemsdine Talbi da kuma Samir El Mourabet mai shekara 20, wanda ke taka leda a Faransa tare da Strasbourg.
Wannan shi ne canji na huɗu daga biyar da Carlo Ancelotti ya sauya ƴan wasa kawo yanzu. An canja Igor Thiago an maye gurbinsa da Matheus Cunha na Manchester United.
Saura canji ɗaya ya rage wa Brazil
Dukkansu tawagogin na neman kara cin ƙwallo, amma babu wata dama da aka samu, kuma a zagaye na biyu Brazil ta fi dannawa, amma kuma babu wani kalubale daga Moroko.
Watakila sun gamsu da wannan sakamakon 1-1, domin babu wanda ya yunkura ya kara cin ƙwallo, amma an fi gara leda a gidan Moroko.