Gasar kofin duniya 2026: Ingila ta fara da cin Croatia 4-2

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
England 4 , Croatia 2 at Full time
Ingila
Croatia
Full time
Hutun rabin lokaci Ingila 2 , Croatia 2

Key Events

Ingila

  • H. KanePenalty 12 minutes, Goal 42 minutes
  • J. BellinghamGoal 47 minutes
  • M. RashfordGoal 85 minutes

Croatia

  • M. BaturinaGoal 36 minutes
  • P. MusaGoal 45 minutes plus 5
Ba da ƙwallo a ci
Ingila,D. Rice (42 minutes), E. Anderson (47 minutes), B. Saka (85 minutes)
Croatia,P. Sučić (36 minutes), I. Perišić (45 minutes plus 5)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan za ku ci gaba da bibiyar BBC Hausa, don kawo muku sharhi da bayanan wasannin cin kofin duniya da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.

    Sunana Mohammed Abdu nake yi muku fatan alheri. Sai da safe.

  2. Wasannin da za a ci gaba a gasar kofin duniya

    Liv

    Asalin hoton, BBC Sport

  3. Yadda aka taka leda a zagaye na biyu

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  4. An tashi wasan, England 4-2 Croatia

    Ingila ta samu maki uku a kan Croatia, bayan nasara da cin 4-2 a wasan farko a rukuni na 12.

    Sai da tsakar dare Ghana za ta kece raini da Panama.

  5. , England 4-2 Croatia

    An buga kwallo ta fada cikin yan kallo, wani ya kama ya rike ba zai bayar ba, zai ajiye a matsayin tarihi da zai nunawa yan baya.

  6. , England 4-2 Croatia

    Kowa ya samu dama mai kyau tsakanin Croatia da Ingila, amma babu wadda ta amfana.

    Muna daf da tashi daga karawar nan, kuma wasan ya yi kyau an ci kwallo shida.

  7. , England 4-2 Croatia

    Na manta ban sanar da ku cewar dan wasan Manchester City, Marc Guehi ya canji takwaransa, John Stones.

  8. An yi karin minti shida

    Ko Ingila za ta hada maki uku a wasan farko a rukuni na 12 ko kuma Croatia za ta yi wani abin kafin lokaci ya cika?

  9. GOAL - England 4-2 Croatia, Marcus Rashford

    Saka ne ya jawo kwallon daga gefen dama ya kuma bai wa Rashford daga gefen hagu, shi kuma ya shiga gidan Croatia, sai da ya dakatar da dan wasa sannan ya buga ta fada raga.

    Rashford ya koma kan ganiya tun bayan da ya buga wasannin aro a kakar da ta wuce a Barcelona daga Manchester United.

    Marcus Rashford # 11 na Ingila ya zira kwallo ta hudu a tawagarsa

    Asalin hoton, Getty Images

  10. , England 3-2 Croatia

    Kadan ya rage sabon dan wasan Ingila da ya shiga wasan ya ci kwallo, wato Spence ya buga kwallon amma ta taba mai tsaron ragar Croatia.

    Rashford yana jan kwallo daga bangaren hagu, har yanzu bai samu wata babbar dama ba.

  11. Croatia da Ingia sun yi canjin yan wasa, Ingila 3-2 Croatia

    Martin Baturina ya fita daga filin, inda Nikola Vlasic ya maye gurbinsa.

    A Ingila kuwa, Jude Bellingham ya fita, yayin da Djed Spence ya samu damar shiga filin.

  12. , Ingila 3-2 Croatia

    Jude Bellingham na Ingila (R) ya yi murna

    Asalin hoton, Getty Images

  13. , England 3-2 Croatia

    Croatia ta nemi ragar Ingila, amma mai tsaron ragar Ingila, ya kama kwalon cikin ruwan sanyi.

  14. Ingiula ta sauya yan wasa uku, Ingila 3-2 Croatia

    Wadanda suka shiga wasan sun hada da Morgan Rogers da Marcus Rashford da kuma Bukayo Saka.

    Wadanda aka cire sun hada da Declan Rice da Anthony Gordon da kuma Noni Madueke.

  15. An ci gaba da wasan

    An shiga gangare a wasan, kenan kasa da minti 20 za a tashi daga karawar, kuma wannan sakamakon ya yi wa Ingila daidai idan har za a tasghi haka.

  16. An je hutun shan ruwa

  17. Croatia ta yi canjin yan wasa, Ingila 3-2 Croatia

    Ta saka Marco Pasalic da Igor Matanovic, sun maye gurbin Luka Vuskovic da kuma Petar Musa.

  18. Yadda Ingila ta mamaye wasan nan, Ingila 3-2 Croatia

    Yadda Ingila ta mamaye karawar nan

    • Kai hari sau 18
    • Wadanda suka nufi raga 10
    • Manyan damar cin kwallo sau shida
    Jude Bellingham na Ingila (C) ya yi murna

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Croatia ta yi canjin dan wasa, Ingila 3-2 Croatia

    Kyaftin, Luka Modric ya fita daga wasan, yayin da Mateo Kovacic ya maye gurbinsa.

  20. , England 3-2 Croatia

    Golan Croatia, Livokovic ya cancanci jinjina, yadda yake haka Ingila zura masa kwallo a raga, Ingila ta matsa sai ta kara, ganin ita take cin kwallo ana farkewa.

    Ta kwan da sanin cewa maki uku a wasan farko a cikin rukuni yana da mahimmaci.