Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da muka sani kan amfani da AI da aka ce Boko Haram da ISWAP na yi
Sabon bincike ya nuna cewa ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Najeriya, musamman ISWAP da Boko Haram sun fara amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI ta hanyoyi daban-daban wajen gudanar da ayyukansu.
Rahoton ya bayyana cewa mayaƙan na amfani da fasahar wajen tsara dabarun yaƙi, gudanar da bincike bayan hare-hare, da kuma samun ilimin fasaha da zai iya taimaka musu wajen ƙara ƙwarewa a ayyukansu.
Binciken, wanda Antonia Juelich, wata ƙwararriya kan harkokin AI da ke aiki tare da Jami'ar Cambridge ta Birtaniya ta gudanar, ya dogara ne kan tattaunawa da tsofaffin mayaƙan ISWAP da Boko Haram.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa binciken ya gano yadda waɗannan ƙungiyoyi ke ƙara rungumar sabbin fasahohi domin ƙarfafa ayyukansu.
Me hakan ke nufi?
Wani masanin fasahar zamani, Umar Saleh Gwani, ya ce ko da yake AI ba ita ce ke yanke hukuncin kai hari ba, tana taimakawa wajen samar da bayanai da shawarwari cikin sauri.
"Hanyoyin da aka ruwaito suna amfani da shi akwai tsara hare-haren soji da za su kai, da yadda za su rarraba mayaƙansu zuwa fannoni daban-daban na gudanarwa da kuma kai hare-hare. A nan, AI ba ita ce ke yanke hukunci ba, sai dai tana taimakawa wajen bayar da shawarwari cikin sauri," in ji shi.
A cewarsa, ana kuma amfani da kyamarori da ke haɗe da fasahohin AI wajen nazarin abubuwan da suka faru bayan kai hari.
Wannan na ba mayaƙan damar fahimtar kurakuran da suka tafka da kuma hanyoyin inganta hare-haren da za su kai a gaba.
"AI na iya taimakawa wajen nazarin bidiyo bayan harin ya faru, ta gano kura-kurai da kuma ba da shawarar yadda za a inganta aiki da haɗin kai a tsakanin mayaƙan," ya ƙara da cewa.
Buƙatar taka-tsantsan
Sai dai duk da waɗannan bayanai, wasu masana tsaro sun nuna cewa akwai buƙatar a yi taka-tsantsan wajen karɓar rahoton ba tare da tambaya ba.
Barista Dr Audu Bulama Bukarti, masani kan batutuwan tsaro a Afirka, ya ce babban ƙalubalen rahoton shi ne yadda aka tattara bayanansa.
"Akwai maganganu da dama kan inganci ko sahihancin wannan rahoto. Babu wata hanya mai sauƙi ta tabbatar da bayanan saboda rahoton ya ta'allaka ne kan tattaunawa da tsofaffin mayaƙan Boko Haram da ISWAP waɗanda suka yi waɗannan ikirari," in ji shi.
Duk da haka, ya ce wasu bayanai da suka fito a baya na nuna cewa akwai yiwuwar ƙungiyoyin sun fara amfani da fasahar AI tun shekaru da dama.
Dr Bukarti ya ce wasu rahotanni sun nuna cewa mayaƙan ISIS daga ƙasashe irin su Libiya, Faransa da wasu ƙasashen Larabawa sun kai ilimin AI zuwa yankin Tafkin Chadi.
A cewarsa, bayanan sirri da rahotannin bincike sun nuna cewa tun daga shekarar 2023 wasu rassan ISWAP da Boko Haram sun kafa ƙananan sassa na musamman da ke kula da hanyoyin amfani da AI wajen ayyukansu.
"Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyoyin sun samar da wasu sassa masu zaman kansu da aikinsu shi ne bincike da lura da yadda za a yi amfani da AI wajen ƙara inganta ayyukansu," in ji shi.
Wace barazana ayyukan ke yi?
Masanin tsaron ya yi gargaɗin cewa amfani da AI zai iya ƙara wa ƙungiyoyin ta'addanci ƙarfi ta fannoni daban-daban.
Ya ce fasahar na iya taimakawa wajen hanzarta sadarwa, tattara bayanai da kuma nazari kan dabarun tsaro.
Dr Bukarti ya kuma yi gargaɗin cewa idan hukumomi ba su ɗauki matakin da ya dace ba, akwai yiwuwar wannan sabon salon amfani da fasaha ya ƙara jefa yankunan da ke fama da rikici cikin matsala.
"Akwai gaggarumar rawa da AI za ta iya takawa wajen ƙara inganta ayyukan ta'addanci. Don haka wajibi ne hukumomi su ɗauki matakan da suka dace domin hana ƙungiyoyin amfana da wannan fasahar wajen ci gaba da aikata laifuka," ya ce.
A baya-bayan nan, rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa tana mai cewa mayaƙan Boko Haram da ISWAP na samun tallafi da horo daga wasu mayaƙan ƙasashen waje. Har ila yau, sojojin sun wallafa hotuna da suka nuna wasu mutane da aka ce 'yan ƙasashen waje ne da ke taimaka wa mayaƙan a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Ko da yake har yanzu akwai buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da cikakkun bayanan da rahoton ya ƙunsa, masanin tsaron ya yi ittifakin cewa ƙara amfani da fasahohin zamani, musamman AI, na cikin manyan ƙalubalen tsaro da hukumomi za su fuskanta a shekaru masu zuwa.
Yayin da duniya ke ci gaba da cin moriyar fasahar AI a fannoni irin su kiwon lafiya, ilimi da tattalin arziki, rahotanni na nuna cewa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ma na neman amfani da ita domin cimma manufofinsu.
"Wannan ya ƙara bayyana muhimmancin samar da dokoki, sa ido da kuma ƙarfafa tsaro domin hana fasahohin zamani fadawa hannun masu aikata laifuka." in ji Bulama Bukarti.