Charles III, da ya kasance yarima mai jiran gadon sarautar Birtaniya mafi dadewa a tarihi, a yanzu ya zama Sarki.
Ya dauki shekara 70 a matsayin mai jiran gadon sarautar ta Birtaniya, wanda hakan ya sanya shi mutum mafi shekaru da yawa da ya zama sabon Sarki.
Ga wasu daga cikin muhimman hotunan rayuwar Sarki Charles na III mai shekara 73 a yanzu.
Asalin hoton, Mirrorpix / Getty Images
Bayanan hoto, An haifi Charles Philip Arthur George ranar 14 ga watan Nuwamban 1948, inda yana shekara uku aka nada mahaifiyarsa a matsayin Sarauniyar Ingila
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Yana dan shekara daya, mahaifiyarsa ta tafi da shi zuwa Malta domin samun Yarima Philip wanda a lokacin yake aiki da rundunar sojin ruwa
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, An rika barin Charles a hannun jami'an kiwon lafiya don kula da shi lokacin da mahaifiyarsa ta dauke shi zuwa Malta
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Charles ya yi karatun boko a gida har zuwa shekara takwas, inda kuma ya zama mutum na farko mai jiran sarautar Birtaniya da ya fara zuwa makaranta - nan, shi ne yake buga kwallo tare da 'yan uwansa dalibai a shekarar 1957
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Alakarsa ta kasance ta kut-da-kut da kakarsa, mahaifiyar Sarauniya
Asalin hoton, Keystone / Getty Images
Bayanan hoto, A wani yunkuri na karfafa Charles, an tura shi zuwa Gordonstoun da ke Scotland, domin kammala karatunsa. Sai dai, ya roki iyayensa da su bar shi ya bar wajen saboda musguna masa da wasu ke yi
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Charles ya karanta fannin nazarin kayan tarihi da ke binne a kasa da nazarin halittu da kuma tarihi a kwalejin Trinity da ke Cambridge - shi ne mai jiran gadon sarautar Birtaniya na farko da ya kammala karatun digiri
Asalin hoton, Central Press / Getty Images
Bayanan hoto, A watan Yulin 1969, an nada Charles a matsayin Yariman Wales a wani kasaitaccen biki da ya gudana a fadar Caernarfon, inda ya yi jawabi cikin harsunan Welsh da Ingilishi
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Ya bi sahun al'adar iyalansu ta yin aikin soja, inda ya zama matukin jirgin sama a makarantar sojoji ta RAF da ke Cranwell kafin ya zarce zuwa kwalejin jami'an soji na ruwa a Dartmouth
Asalin hoton, Central Press / Getty Images
Bayanan hoto, Ya samu horo na jami'an soji, inda ya samu mukamin ''Mutum mai hazaka'', a cikin wani jerin sojoji na musamman, inda ta kai har yana sauka daga jiragen sama da horo na jiragen ruwa da sauransu
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Bayan aiki da jiragen ruwa daban-daban, Charles ya zama kwamanda a sashin masu farauta na HMS Bronington a wa'adinsa na karshe a rundunar sojin ruwa ta gidan sarauta
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Lokacin da ya kusa cika shekara 30 da haihuwa, an koma sanin tsohon yariman na Wales da yaro mai son wasa
Asalin hoton, Hulton Archive / Getty Images
Bayanan hoto, A nan, an dauki hoton Charles yana wasan ninkaya da na tudun ruwa
Bayanan hoto, Charles ya kuma yi soyayya da mata da yawa, wanda ya kunshi har da Camilla Parker Bowles
Asalin hoton, Hulton Archive / Getty Images
Bayanan hoto, Duk da cewa an yi ta magana kan batun samar wa Yariman ''aikin yi'', ya yi ziyara daban-daban na gidan sarauta da kuma shiga aikin agaji, inda ya kafa gidauniyarsa ta Prince Trust a shekarar 1976
Asalin hoton, Hulton Archive / Getty Images
Bayanan hoto, A shekarar 1981, bayan yayata batun soyayyarsa a kafofin yada labarai, an sanar da cewa an yi wa Charles baiko da Lady Diana Spencer
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Watanni biyar bayan baikon, an gudanar da aurensu a Cocin St Paul - inda aka yi kiyasin cewa mutum 600,000 ne suka cika titunan birnin Landan domin yi musu fatan alkhairi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Nan, ma'auratan ne ke daukar hoto a kusa da kogin Dee a Balmoral, da ke Scotland, a kwanakin karshe na hutun aurensu da suka je yi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Duk da cewa sun sami haihuwar 'ya'ya biyu, Yarima William a 1982 da ƙaninsa, Yarima Harry a 1984, auren nasu ya shiga matsala, inda har ta kai ga rabuwarsu a watan Yulin 1996 saboda wasu dalilai da aka kasa daidaitawa
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Bayan mutuwar Diana a wani hadarin mota a birnin Paris a shekarar 1997, Charles ya nace cewa a yi mata jana'iza ta alfarma ta sarauta
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mutuwar Diana ta sanya gidan sarautar sake duba ƙimarta, inda Charles ya sauya nan take, har ta kai ga ya zama uba mai taimaka wa a matsayinsa na yarima mai iran gado
Asalin hoton, PA
Bayanan hoto, Bayan zargin Charles da kadaicewa da kuma kin shiga mutane bayan mutuwar Diana, ya yi kokarin sauyawa da kuma sake kulla hulda da jama'a
Asalin hoton, Tim Graham Photo Library via Getty Images
Bayanan hoto, Ya kasance yana magana a kan batutuwa da dama, inda yake nuna goyon bayansa ga bangaren noma da samar da magani da kuma adawa da kayan amfanin gona da aka gyara
Asalin hoton, Shutterstock
Bayanan hoto, Charles, yana kuma da sha'awar fannin zanen gine-gine na zamani, inda ya samu damar tsara kauyen Poundbury da ke Dorset zuwa wani birni mai kyau
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A shekarar 2002, ya yi magana kan kakarsa - mahaifiyar Sarauniya - wacce ta rasu salin-alin lokacin da take bacci tana shekara 101. A nan, yana tsaye ne wajen da aka ajiye gawar ta a wani babban daki a Westminster da ke birnin Landan
Asalin hoton, Wireimage / Getty Images
Bayanan hoto, Bayan haduwar Charles da Camilla Parker Bowles shekarar 1970, dangantakarsu ta ci gaba da wanzuwa a tsawon shekaru, inda suka sanar da baikonsu a 2005
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ya zama mutum na farko daga gidan sarauta da aka yi wa biki irin na sauran mutane - Mrs Parker Bowles ta zama Duchess ta Cornwall, inda kafin Charles ya zama yarima mai jiran gado, ita kuma ta zama matar Sarki
Asalin hoton, PA
Bayanan hoto, A shekarar 2011, baban dansa, Yarima William, ya auri Kate Middleton a Westminster Abbey
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, An haifi jikokin Sarkin, Yarima George da Sarauniya Charlotte a shekarun 2013 da 2015
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Sarki Charles III ke tafiya zuwa cikin coci riƙe da hannun Meghan Markle lokacin da ta auri Yarima Harry a 2018
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Hankalin Sarkin a tashe lokacin da ya jagoranci mutane zuwa inda gawar mahaifinsa Philip take yayin binne shi a fadar Windsor a 2021
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Charles ya zama Sarki a lokacin da halayen jama'a kan sarauta ke sauyawa