Man United na son Summerville, Arsenal za ta taya Nusa

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta mayar da hankali kan sayen dan wasan gefe na West Ham, Crysencio Summerville, mai shekara 24, idan Marcus Rashford ya bar kungiyar a wannan bazarar. Ana kyautata zaton dan wasan na Netherlands zai kai kusan fam miliyan 30.
Arsenal na shirin gabatar da tayin kusan fam miliyan 34 domin sayen danwasan gefe na RB Leipzig kuma dan kasar Norway, Antonio Nusa, mai shekara 21.
Manchester City ta sanar da matashin dan wasan tsakiya na Lille, Ayyoub Bouaddi, mai shekara 18 kuma dan kasar Morocco, cewa tana son shigar da shi kai tsaye cikin tawagar farko maimakon ta maida shi aro zuwa kungiyar ta Faransa.
Manchester City na kuma bibiyar matashin dan wasan gaba na Senegal, Ibrahim Mbaye, mai shekara 18 daga Paris Saint-Germain, bayan da Aston Villa da Tottenham suka nuna sha'awar sayensa.
Sunderland na kokarin daukar dan wasan baya na Faransa mai shekara 19, Dayann Methalie, daga kungiyar Toulouse.
Everton na nazarin yiwuwar daukar mai tsaron baya na dama na Manchester City, Rico Lewis, mai shekara 21. Sai dai kuma Nottingham Forest, Bournemouth da Fulham su ma na zawarcin dan wasan na Ingila.
Ana sa ran Hull City za ta kammala sayen dan wasan gefe na Sweden, Elliot Stroud, mai shekara 24 daga Mjallby a wannan makon kan kudi kusan fam miliyan uku. Haka kuma kungiyar na fatan kammala cinikin gole na Olympiacos kuma dan kasar Girka, Konstantinos Tzolakis, mai shekara 23.










