Real Madrid na harin Fernandes, Bayern Munich na son Saibari

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta tuntubi West Ham kan dan wasanta Mateus Fernandes amma Manchester United na kan gaba wajen siyan dan wasan Portugal din, mai shekara 21.(Teamtalk), external

Manchester United ba ta shirya biyan kudin da West Ham ta ke son a kan Fernandes ba ,wanda ya kusan fam miliyan 80, amma kuma Paris St-Germain da Real Madrid sun nuna sha'awar daukarsa. (Mirror), external

Bayern Munich na shirin dauko dan wasan Morocco Ismael Saibari, mai shekara 25, daga PSV Eindhoven kan kudi sama da fam miliyan 45.(Talksport), external

Real Madrid ta tambayi halin da Felix Nmecha ke ciki a Borussia Dortmund, duk da cewa tsohuwar kungiyar dan wasan na Jamus watau Manchester City da kuma abokiyar hamayyarta Manchester United duk suna zawarcin dan wasan mai shekara 25.(Sky Sport Germany - in German), external

Newcastle United na shirin kara tattaunawa da Osasuna kan dan kasar Sifaniya Victor Munoz mai shekaru 22 a wannan makon.(Mail), external

Wa'adin da aka debar wa Barcelona don siyan Marcus Rashford kan Yuro miliyan 30 na dab da karewa ba tare da ta yanke shawara kan ko za ta maida aron da aka bada dan wasan Ingila mai shekara 28 daga Manchester United na dindindin.(ESPN), external

Leeds United na shirin daukar dan wasan Ivory Coast Ousmane Diomande mai shekara 22 daga Sporting, wanda zai iya maye gurbin dan wasan yankin Wales Joe Rodon mai shekara 28.(Football Insider), external

Ipswich da Hull City na zawarcin mai tsaron ragar Ingila Nick Pope, inda Newcastle ta nuna alamun za ta sayar da da dan wasan mai shekara 34 kan fam miliyan 5 (Teamtalk), external

West Ham na cikin kungiyoyin ingila da ke bibiyar dan wasan Watford, Nestory Irankunda, mai shekara 20, da ke buga wa Australia wasa a gasar cin kofin duniya ta Fifa. (Football Insider)