Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda launukan rigar Ka'aba suka riƙa sauyawa tsawon shekaru
An gudanar da sauyin rigar Ka'aba (Kiswa) na shekara-shekara a ranar Litinin 15 ga watan Yunin 2026, kuma hakan na zuwa ne a watan farko (Muharram) na shekarar hijiriyya.
A shekarun baya ana gudanar da aikin sauya rigar ta Ka’aba ne ranar 10 ga watan Dhul Hijjah, wanda ke zuwa daidai da ranar Idin layya, amma a baya-bayan nan an mayar da shi zuwa ranar farko ta Muharram, wata na farko a kidayar watannin Musulunci.
Kafin sauya rigar, akan kewaye da'irar ɗakin na ka'aba ta yadda mutane ba za su iya kaiwa jikin ɗakin ba, inda daga nan tawagar ma'aikata ke kwance tsohuwar rigar, sannan su nannaɗe ta cikin tsanaki.
Wannan zai ba da damar rataya sabuwar rigar bisa tsari, a tsanake.
Ana gudanar da aikin sauya eigar Ka'aba ne cikin ƙwarewa kasancewar ana cire tsohuwar rigar ce a tsanake, ɓagare bayan ɓangare, sannan a ja sabuwar rigar zuwa saman ka'aba a shimfiɗa ta.
Miliyoyin mutane ne suke tsayawa domin kallon yadda ake yin haka.
A yanzu rigar ta Ka’aba takan kasance baka ce mai ado da siliki da kuma ruwan zinare.
To amma ko kun san cewa an sha sauya launin rigar ka’aba a tsawon tarihi?
Launin Ja
Rigar Ka'aba gabanin zuwan Annabi Muhammadu ta kasance mai launin ja. An riƙa haɗa rigar da wani yadi mai inganci ɗan Yemen.
A wancan lokaci ana kallon yadin a matsayin mafi inganci a ɗaukacin yankin Larabawa.
Launin Fari
Sai dai bayan zuwan Annabi Muhammad an sauya launin rigar Ka'aba zuwa fari.
Rigar ta kasance ana hada ta da wani yadi mai inganci dan Misira, wanda ƙibɗawa ke haɗawa, kuma ya kasance sanannen yadi a wancan lokaci.
An riƙa amfani da wannan farin yadi a matsayin rigar Ka'aba daga shekara ta farko zuwa ta 11 bayan Hijira.
Launin Kore da fari
An ci gaba da amfani da yadi mai launin fari a matsayin rigar Ka'aba har zuwa wasu shekaru, sannan daga baya aka riƙa hadawa da launin kore.
An yi amfani da wannan launin ne a lokacin khalifofin Annabi Muhammad da kuma na iyalin Umayyad.
Hakan ya faru ne tun daga shekara ta 11 zuwa ta 132 bayan Hijira.
Sai dai an ci gaba da amfani da launin kore har zuwa shekara ta 198 bayan Hijira.
Launin baƙi - gwal
Baƙi shi ne launin rigar ka'aba na baya-bayan nan, wanda kuma ya kwashe sama da shekara 1200 ana amfani da shi.
An fara amfani da launin ne daga shekarar 206 bayan Hijira har zuwa yanzu (1447 bayan hijira).
Ya zuwa shekara ta 648 bayan Hijira an ci gaba da amfani da baƙi a matsayin launin rigar ta ka'aba inda ake haɗawa da rubutu mai launin gwal.
An ci gaba da ƙawata rigar ka'abar da zaren siliki mai launin gwal har zuwa yanda yake a yanzu..
Wa ke samar da rigar Ka'aba a yanzu?
Tun daga 1962, Saudiyya ce ke ɗaukar nauyin samar da rigar ta Ka'aba da duk wasu hidindimu da ake yi mata.
A zamanin mulkin daular Bani Umayya, ana ɗinka rigar ce a ƙasar Sham (Syria) sai a aika da ita Makka duk shekara.
Daga baya Masar ta ɗauki nauyin samar da rigar, abin da ta riƙa da cikakken alfahari.
A shekarar 1926 Sarki Abdulaziz wanda ya kafa daular Al Saud, ya bayar da umarnin kafa masana'antar rigar Ka'aba a birnin Alkahira na Masar.
A 1927, sarkin ya bayar da umarnin ware wani gida a kusa da Haramin Makka don saƙar rigar, kuma wannan shi ne karon farko da aka saƙa rigar a Saudiyya.
Masar ta dakatar da saƙa sabuwar rigar Ka'aba saboda wani saɓani na siyasa tsakaninta da Saudiyya, abin da kenan ya sa Saudiyya ta rungumi aikin gaba-gaɗi.
An fara amfani da na'urori na zamani wajen saƙa rigar Ka'aba a 1965. A shekarar 1972, Sarki Faisal bin Abdulaziz ya ba da umarnin kafa masana'anta ta musamman don saƙa rigar.
A 2017, Sarki Salman ya ba da umarnin sauya duka injinan da ake amfani da su wajen saƙa rigar ta Ka'aba, inda ya ba da umarnin a saka na zamani.
Wasu bayanai na cewa masaƙar, ita ce masakar tufafi mafi girma kuma mafi kyawun na'urori a duniya.
Fiye da ƙwararru 200 ne daga ƙasashen duniya suke aiki a masaƙar, inda suke shafe shekara guda suna ɗinka riga ɗaya da aka yi imanin ita ce mafi tsada a duniya.
An ƙiyasta cewa ana kashe kusan dala miliyan shida wajen samar da rigar ta Ka'aba.
Ya ake yi da rigar Ka'aba da aka cire?
A duk shekara ana kai rigar Ka'aba da aka cire zuwa wani wajen ajiye kayayyaki na gwamnatin Saudiyya, inda ake adana ta ta yadda ƙwayoyin cutar bakteriya ba za su taɓata ba, ko kuma tasirin sinadarai su yi mata illa.
A wannan wajen ne ake yayyanka rigar zuwa ƙyallaye da dama, a rarraba wa manyan mutane na duniya da suka kai ziyara Saudiyya.
Ana kuma aike wa ƙasashe da ofisoshin jakadanci da ke ƙasar ta Saudiyya.
An gina wannan labari ne daga bayanan shafin masallatan harami.