Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane aiki ƴan sandan jihohi za su riƙa yi a Najeriya?
- Marubuci, Chukwunaeme Obiejesi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Sabon ƙudirin dokar kafa rundunar 'yan sandan jihohi a Najeriya, wanda Shugaba Bola Tinubu ya aika wa Majalisar Tarayya kuma Majalisar Dattawa ta amince da shi a ranar Laraba, na daf da zama doka, watakila ma kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Dama Majalisar Wakilai ta riga ta amince da irin wannan ƙudiri, ko da yake akwai wasu bambance-bambance tsakanin nata da wanda Majalisar Dattawa ta amince.
A yanzu mataki na gaba shi ne kwamitin haɗaka na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai zai tantance ƙudurorin biyu tare da haɗa su wuri guda kafin amincewa da shi ya zama doka a kundin tsarin mulkin ƙasar.
Yanzu kuma za a aika da ƙudirin zuwa majalisun dokokin jihohi 36 na ƙasar, inda dole ne aƙalla majalisun jihohi 24 su amince da shi kafin a miƙa wa shugaban ƙasa ya sanya hannu inda daga nan ne ya zama doka.
Jam'iyyar APC mai mulki na da jihohi 32 cikin 36 na Najeriya a halin yanzu. Haka kuma a wasu jihohin da ba APC ce ke mulki ba, kamar Anambra da Abia, gwamnonin jihohin na da kyakkyawar alaƙa da Shugaba Tinubu, lamarin da masu sharhi ke ganin akwai yiwuwar ƙudirin ya samu goyon bayan majalisun dokokin jihohin.
Ga wasu daga cikin sauye-sauyen da ake sa ran za su faru idan ƙudirin kafa 'yan sandan jihohi ya zama doka:
Mene ne aikin ƴan sandan jihohi?
A yayin muhawara kan ƙudirin dokar kafa rundunar 'yan sandan jihohi a Majalisar Dattawa a ranar Laraba, shugaban masu rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele, ya ce idan ƙudirin ya zama doka, za a samu rundunar ƴan sandan Najeriya guda biyu. Rundunar 'Yan Sandan Tarayya da kuma Rundunar 'Yan Sandan Jiha.
Sai dai kafin wata jiha ta kafa rundunar ƴan sandanta, dole ne ta fara zartar da dokar da za ta kafa rundunar, kuma dole dokar ta cika ƙa'idojin da Majalisar Tarayyar ƙasar ta shimfiɗa.
Ƙudirin ya tanadi cewa rundunar 'yan sandan jiha za ta riƙa gudanar da ayyuka da suka haɗa da:
- Tabbatar da doka da oda a jiha
- Tsaron al'umma da wanzar zaman lafiya
- Daƙile aukuwar laifuka da kuma binciken waɗanda suka faru a cikin jihar
- Kare rayuka da dukiyoyin al'umma
- Gudanar da sauran ayyukan tsaro da suka shafi jihar
Sai dai ƙudirin ya kuma tanadi cewa Rundunar 'Yan Sandan Tarayya za ta iya shiga cikin harkokin tsaro na jiha a wasu lokuta na musamman.
Idan aka samu take doka da oda a lamarin da ya wuce gona da iri a wata jiha, ko kuma idan gwamnan jihar ya nemi taimako daga gwamnatin tarayya.
Haka kuma rundunar tarayya za ta iya bayar da gudummuwa idan rundunar 'yan sandan jihar ta kasa gudanar da ayyukanta saboda, ƙarancin kuɗaɗe ko kuma matsalolin gudanarwa ko wasu dalilan.
Yadda za a gudanar da ƴan sandan jihohi
Ƙudirin dokar ya tanadi cewa gwamnonin jihohi za su samu ikon naɗa kwamishinonin ƴan sanda na jihohinsu daga cikin jami'an rundunar da ke aiki a jihar, tare da ba su umarni kai tsaye kan harkokin tsaro.
Sai dai naɗin ba zai tabbata sai ya samu amincewar majalisar dokokin jihar da kuma hukumar kula da ayyukan ƴansanda.
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Yemi Adaramodu, ya bayyana cewa tsarin ya yi kama da yadda ake naɗin manyan alƙalan jihohi, inda gwamna zai iya gabatar da sunan wanda yake so, amma wata hukuma mai zaman kanta ce ke da ikon amincewa da naɗin.
"Idan gwamna ya naɗa kwamishinan 'yan sanda, za a tura sunan gaban hukumar kula da ayyukan ƴansanda ta tarayya, wadda za ta tantance tarihinsa da cancantarsa kafin ta amince da naɗin," in ji Adaramodu.
Ƙudirin ya kuma tanadi wasu matakan da aka bayyana cewa za su hana amfani da rundunar ƴan sandan jihohi ta hanyar da ba ta dace ba.
- Ba dole ne kwamishinan ƴan sandan jiha ya bi duk wani umarni da ya saɓa wa doka daga gwamna ba. Maimakon haka, zai iya kai rahoton lamarin ga hukumar kula da ƴansanda ta ƙasa.
- An haramta amfani da ƴan sandan wajen biyan wasu buƙatun siyasa, ko ƙabilanci da addini ko yanki ko wata buƙata ta ƙashin kai.
- Majalisar Tarayya za ta ci gaba da tsara ƙa'idojin ɗaukar aiki, horaswa, tantancewa, ƙarin girma da kuma hukunta jami'an ƴansanda.
- Rundunar ƴansandan tarayya za ta iya bayar da gudummuwa idan aka samu take-haƙƙin ɗan adam, ko razana jama'a, ko kuma idan an samu barazanar tsaron ƙasa.
- Sai dai ƙudirin ya ce duk wani matakin da rundunar tarayya za ta ɗauka na bayar da gudummuwa dole ne ya samu amincewar shugaban ƙasa a rubuce.
Yadda aka daɗe ana muhawara kan kafa ƴan sandan jihohi
Batun kafa rundunar 'yan sandan jihohi ba sabon abu ba ne a Najeriya. Sai dai matsalar rashin tsaro da ta bazu zuwa kusan dukkan sassan ƙasar ce ta sake dawo da hankalin jama'a kan buƙatar.
Mutane da dama da a baya ba su goyi bayan ra'ayin ba sun fara sauya matsayinsu, suna ganin hakan na iya taimakawa wajen magance matsalolin tsaro. Duk da haka, har yanzu akwai masu nuna damuwa cewa ƴan siyasa za su iya amfani da rundunar domin cimma muradunsu.
Tsohon shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan'ƙdam ta Ƙasa, Chidi Odinkalu, wanda ya sha sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana damuwarsa kan shirin, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Odinkalu ya ce: "Manufar ita ce a kafa ƴan sandan jihohi kafin zaɓen 2027 sannan a ba gwamnonin APC rundunonin da za su yi aiki a ƙarƙashin ikonsu."
Shi ma mai gabatar da shirye-shiryen a gidan talabijin na Arise, Rufai Oseni, ya ce yana goyon bayan kafa ƴan sandan jihohi, amma ya nuna damuwa kan yadda aka tsara ƙudirin, inda ya ce har yanzu kusan dukkanin ikon gudanar da tsarin na hannun shugaban ƙasa.
Oseni ya bayyana cewa mambobin hukumar ƴansanda ta ƙasa, wadda za ta kula da rundunar, har yanzu suna ƙarƙashin shugaban ƙasa ne "saboda haka babu wani abin da zai canza," in ji shi.
Shi ma Sanata Ali Ndume ya ce akwai wasu batutuwan da suka kamata a ƙara nazari a kansu kafin a aiwatar da tsarin inda ya buga misali da yadda za a gudanar da bincike idan wanda ake nema ruwa a jallo ya tsallaka daga wata jiha zuwa wata.
"Misali idan ana bin wani da ake zargi da sata daga Kaduna ya tsere zuwa Abuja, me zai faru? Za a bar shi ne saboda ya fita daga yankin ikon rundunar?" in ji Ndume.
Sai dai masu goyon bayan ƙudirin na ganin wannan tsarin zai taimaka sosai wajen inganta tsaro a ƙasar.
Wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum a jihar Enugu, Ambrose Igbokwe, ya ce: "idan an kafa rundunar, gwamnoni ba za su sake samun hujjar ɗora alhakin matsalolin tsaro kan wasu ba."
Ya ƙara da cewa jihohi da dama sun riga sun kafa wasu matakan tsaro kamar dakarun tsaron gandun daji da ƴan sintiri, don haka abin da ya rage shi ne horaswa, tsara aikin da kuma ɗaukar ƙarin ma'aikata.