Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mun shirya tsaf domin mika sunayen 'yan takararmu ga hukumar INEC — APC
Yayin da yarage kwanaki guda Hukumar Zaben Najeriya, INEC, ta buɗe shafinta na intanet domin jam'iyyun siyasa su aika da sunayen 'yan takararsu a mukamai daban-daban a babban zaben da za a gudanar a 2027, jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta ce ita ma a shirye ta ke ta mika sunayen nata 'yan takarar.
Bala Ibrahim, shi ne daraktan yada labarai na jam'iyyar APC na kasa, ya shaida wa BBC cewa, kamar sauran jam'iyyu suma sun shirya mika nasu sunayen 'yan takarar.
Ya ce," Dama dai anjima ana aiki akan wadannan sunaye, kuma na tantance wadanda suka cancanci tsayawa takarar , Hukumar INEC dama muke jira ta bayar lokacin da za a fara mika sunayen wadannan 'yan takara."
" To tun da yanzu INEC ta shirya karbar sunayen, to muma zamu mika mata su don tabbatar da an cika dukkan sharudan da INEC din ta gindaya." In ji shi.
Bala Ibrahim, ya ce," Yanzu daga tsakanin lokacin da Hukumar zabe ta INEC ta bayar da umarnin a mika sunayen 'yan takarar zuwa loakcin da za a rufe, za mu mikan amu, sannan za mu ba wa wadanda suka samu nasara a zabukan fitar da gwani takardar shaidar Takara."
Ya ce, "Idan mutum na so ya yi abu cikin tsafta ma'ana a ka'idance da shari'ance ba tare da an bakantawa wani ba, to dole ne sai an yi taka tsan-tsan an ja kafa an yi komai ta yadda kowa zai gamsu."
Bala Ibrahim, ya bayar da tabbaci, cewa jam'iyyar tasu ba za ta bari wani abu ya kawo matsala ba, wajen mika sunayen 'yan takarar da aka tantance.
Ana dai zargi jam'iyyar APCn da jan kafa wajen fayyace wadanda da suka sami nasara a zabukan fid da gwanin bayyana damuwa game da jinkirin ba su takardun shaidar lashe zaben.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriyar dai ta yi wannan shiri na mika sunayen 'yan takarartata a zaben 2027 ne,bayan da hukumar INEC ta ce za ta buɗe shafinta na intanet, domin jam'iyyun siyasa su aika da sunayen 'yan takararsu a babban zaben da za a gudanar a 2027.
INEC ta ce, za a bude shafin ne a ranar 27 ga watan Yunin, 2026.
Mai magana da yawun hukumar ta INEC, Zainab Aminu, ta shaida wa BBC cewa tuni hukumarsu ta fara horaswa ta musamman inda aka bukaci jam'iyyun siyasa da su aiko da wakilansu da za a bawa horaswa ta musamman saboda a koya musu yadda ke amfani da shafinmu don su san yadda za su aiko da sunayen 'yan takarar jam'iyyunsu.