Manyan ƴan siyasar Najeriya da suka kafa jam'iyyar APC

    • Marubuci, Usman MINJIBIR
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

A ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 2013 ne jam'iyyun adawa a Najeriya suka haɗe domin kafa sabuwar jam'iyyar APC da ta ƙalubalanci gwamnatin shugaba Jonathan ta PDP a 2015.

Jam'iyyun huɗu ne dai suka haɗe domin kafa APC kuma sun haɗa da ACN da CPC da ANPP da wani ɓangare na PDP da ake kira "Sabuwar PDP" da kuma wani ɓangare na jam'iyyar APGA.

Haɗakar ce ta bai wa marigayi Muhammadu Buhari samun nasarar lashe zaɓen da ya kara da Goodluck Jonathan a 2015, wani abu da ya kawo ƙrshen shekaru 16 na mulkin babbar jam'iyyar ta Najeriya.

Kuma tun shekarar ta 2015 jam'iyyar ta APC a Najeriya.

BBC ta yi nazari kan muhimman mutanen da suka kafa wannan jam'iyya mai shekaru 13 da haihuwa sannan mai shekaru 11 da jan ragamar ƙasa.

Bola Ahmed Tinubu

Bola Ahmed Tinubu wanda shi ne shugaban Najeriya na yanzu da ke neman ƙarin wa'adi na biyu ya kasance babban jigo a haɗakar da ta samar da jam'iyyar APC kasancewarsa jagoran jam'iyyar ACN.

Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen haɗa kan jam'iyyun adawa domin ƙalubalantar PDP.

Saboda tasirinsa wajen gina APC da kuma siyasar ƙasar gaba ɗaya, ana yawan kiransa da "jagoran APC" ko kuma ɗaya daga cikin manyan masu tsara siyasar Najeriya ta zamani.

Tinubu ya yi gwamna a jihar Legas karo biyu daga 1999 zuwa 2007. Ya kuma zama ɗan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Legas a jamhuriyar ta uku - 1992 -1993.

Bayan soke zaɓen June 12, ya goyi bayan buƙatar a tabbatar da nasarar MKO Abiola kuma a mayar da mulkin dimokuraɗiyya.

Ya shiga cikin ƙungiyoyin masu rajin dimokuraɗiyya, musamman National Democratic Coalition (NADECO), wadda ta yi gwagwarmaya da gwamnatin soja domin a mutunta sakamakon zaɓen June 12.

Tinubu ya yi gudun hijira zuwa ƙasashen waje sakamakon matsin lamba daga gwamnatin soji ta lokacin, inda ya ci gaba da goyon bayan fafutukar dawo da mulkin farar hula.

Muhammadu Buhari

Marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya shugabanci najeriya da 2015 har zuwa 2023 ya kasance jigo a kafa haɗakar jam'iyyar ta APC.

Muhammadu Buhari shi ne jagoran jam'iyyar CPC kuma shi ne ya jagoranci jam'iyyar shiga haɗakar.

A zaɓen 2015, Buhari a matsayin ɗan takarar APC ya kayar da shugaban ƙasa mai ci Goodluck Jonathan. Wannan ne karo na farko a tarihin Najeriya da jam'iyyar adawa ta kayar da jam'iyya mai mulki a zaɓen shugaban ƙasa.

Bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, Buhari ya nemi kujerar shugaban ƙasa sau da dama. Daga baya ya kafa kuma ya jagoranci jam'iyyar CPC, ɗaya daga cikin jam'iyyun da suka haɗe suka kafa APC a 2013.

Muhammad Buhari ya kasance shugaban mulkin soja daga ranar 31 ga Disamba 1983 zuwa Agusta 1985 lokacin da aka yi masa juyin mulki.

Bisi Akande

Cif Adebisi Akande da aka fi sani da Bisi Akande fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne, tsohon gwamnan Jihar Osun, kuma ɗaya daga cikin manyan jagororin da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam'iyyar APC.

Ya kasance mataimakin gwamnan tsohuwar Jihar Oyo daga 1982 zuwa 1983 a gwamnatin Bola Ige a Jamhuriya ta Biyu.

Alhaji Bisi Akande ya kasance shugaban riƙo na farko na jam'iyyar ta APC sannan ɗaya daga cikin jagororin haɗakar daga ɓangaren jam'iyyar ACN.

Akande yana daga cikin kusoshin siyasa na Bola Ahmed Tinubu, kuma dukkansu sun kasance manyan jagororin tafarkin siyasar ci gaban yankin Kudu maso Yammacin Najeriya tun daga zamanin AD, AC, ACN har zuwa APC.

Ibrahim Shekarau

Sanata Ibrahim Shekarau fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga Jihar Kano, kuma ya kasance ɗaya daga cikin jagororin ANPP da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam'iyyar APC.

Tsohon gwamnan jihar Kanon karo biyu, lokacin fara tattaunawar haɗewa a 2013, Shekarau ya kasance Shugaban Kwamitin Haɗakar ANPP cikin tattaunawar da ta kai ga kafuwar APC.

Shekarau ya shiga APC tare da magoya bayansa, amma daga baya ya samu sabani da wasu jagororin jam'iyyar a Kano kuma ya fice zuwa PDP.

To sai dai a yanzu Malam Shekarau ya sake komawa jam'iyyar ta APC.

Rochas Okorocha

Owelle Rochas Anayo Okorocha fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga Jihar Imo, tsohon gwamna, tsohon sanata, kuma ɗaya daga cikin jagororin da suka taka rawa wajen kafa jam'iyyar APC.

Okorocha ya kasance jagoran wani ɓangare na APGA wanda ya mara wa haɗakar da ta samar da APC baya. Ana ayyana shi cikin manyan jagororin da suka taimaka wajen gina jam'iyyar a farkon shekarunta.

A baya-bayan nan Okorocha ya shiga zaɓen fidda gwani na APC domin neman tikitin Sanatan Imo ta Yamma, inda ya fafata da Gwamnan jihar Imo mai ci, Hope Uzodimma, inda gwamna Hope ya samu nasara a kansa.

Har yanzu Rochas bai sauya sheƙa ba. Sai dai, duk da kasancewarsa a APC, an daɗe ana samun saɓanin siyasa tsakanin Okorocha da wasu shugabannin APC a Jihar Imo, musamman tsakanin sa da Hope Uzodimma.

Atiku Abubakar

Atiku Abubakar fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne, ɗan kasuwa, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa daga 1999 zuwa 2007 a ƙarƙashin gwamnatin Olusegun Obasanjo.

Ana ɗaukarsa ɗaya daga cikin manyan 'yan siyasar Najeriya tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.

Atiku na daga cikin jagororin sabuwar PDP da suka shiga APC a 2014 kafin zaɓen 2015. Ya kuma nemi takarar shugaban ƙasa a APC amma ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari a zaɓen fidda gwani.

Daga baya, a 2017, ya fice daga APC ya koma PDP.

Atiku Abubaka rya yi takarar neman shugaban ƙasa karo fiye da huɗu kuma zai sake a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam'iyyar ADC.

Rabiu Musa Kwankwaso

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga Jihar Kano, tsohon gwamnan Kano har karo biyu, tsohon minista, kuma jagoran ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin siyasa a Arewacin Najeriya da ake kira Kwankwasiyya.

Kwankwaso ya kasance jigo a jam'iyyar PDP, amma ya shiga ƙungiyar sabuwar PDP wadda ta yi adawa da shugabancin PDP a 2013. Daga baya ya shiga APC tare da sauran jagororin nPDP kafin zaɓen 2015.

Shigarsa APC t samar da babbar gudummawa ga jam'iyyar musamman a Kano da ma Arewa gaba ɗaya, lamarin da ya taimaka wa APC a zaɓen 2015.

Bayan wasu shekaru a APC, Kwankwaso ya fice ya koma PDP, sannan daga baya ya shiga NNPP inda ya zama jagoranta mafi shahara.

Sai dai kuma a 2026 Kwankwaso ya fice daga NNPP ya koma jam'iyyar ADC kafin daga bisani ya sake ficewa ya kuma koma jam'iyyar NDC, inda zai yi takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Peter Obi.

Bukola Saraki

Dr. Abubakar Bukola Saraki fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne, tsohon gwamnan Jihar Kwara, tsohon shugaban Majalisar Dattawa, kuma ɗaya daga cikin manyan jagororin sabuwar PDP da ake kira nPDP da suka taimaka wajen ƙarfafa jam'iyyar APC kafin zaɓen 2015.

A 2013, Saraki ya shiga ƙungiyar sabuwar PDP tare da wasu gwamnoni da manyan jiga-jigan PDP da suka yi saɓani da shugabancin jam'iyyar. Daga baya ya shiga APC tare da sauran jagororin nPDP kafin zaɓen 2015.

To sai dai kuma a shekarar 2018, Saraki ya fice daga APC ya koma PDP tare da wasu 'yan majalisa bayan rikice-rikice na cikin gida a jam'iyyar.

Rotimi Amaechi

Chibuike Rotimi Amaechi fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga Jihar Ribas, tsohon gwamna, tsohon ministan sufuri, kuma ɗaya daga cikin manyan jagororin nPDP da suka taimaka wajen ƙarfafa APC kafin zaɓen 2015.

A lokacin rikicin cikin gida na PDP a 2013, Amaechi ya shiga APC tare da sauran jiga-jigan nPDP, lamarin da ya taimaka wajen ƙarfafa jam'iyyar kafin zaɓen 2015.

Bayan nasarar APC a 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Amaechi a matsayin Ministan Sufuri.

A shekarar 2022, Amaechi ya nemi takarar shugaban ƙasa a APC, amma ya sha kaye a zaɓen fidda gwani da Bola Ahmed Tinubu ya lashe.

Sai dai kuma Rotimi Amaechi ya fice daga APC inda ya koma ADC a 2025.

Murtala Nyako

Vice Admiral Murtala Hamman-Yero Nyako, mai ritaya ɗan siyasar Najeriya ne kuma tsohon babban jami'in rundunar ruwan ƙasar.

Ya kasance Gwamnan Jihar Adamawa daga 2007 zuwa 2014, kuma yana daga cikin manyan jiga-jigan nPDP da suka mara wa APC baya kafin zaɓen 2015.

A lokacin rikicin cikin gida na PDP a 2013, Nyako ya kasance ɗaya daga cikin gwamnonin da suka shiga nPDP tare da Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Bukola Saraki, Rotimi Amaechi da Aliyu Wamakko.

Wannan ƙungiya ta nPDP ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa APC kafin nasarar jam'iyyar a zaɓen 2015.

Har yanzu Murtala Nyako na cikin jam'iyyar APC duk da ba acika jin amonsa ba.

Sai dai abin da ya fi fitowa a rahotannin baya-bayan nan shi ne batun ɗansa, Abdulaziz Nyako. Abdulaziz ya taɓa barin APC ya shiga ADC, amma a watan Maris 2026 ya sanar da cewa ya koma APC.

Sauran waɗanda suka kafa APC
  • Tom Ikimi - wakilin ACN a kwamitin haɗakar jam'iyyun.
  • Abdulfatah Ahmed - gwamnan Kwara a lokacin.
  • Aliyu Magatakarda Wamakko - gwamnan Sokoto a lokacin.
  • Aminu Waziri Tambuwal - Kakakin Majalisar Wakilai a lokacin.
  • Annie Okonkwo - wakilin ɓangaren APGA da ya shiga haɗakar.
  • Buba Galadima - Wakili daga jam'iyyar CPC
  • Cif Tony Momoh
  • Cif John Oyegun - Tsohon shugaban jam'iyyar APC
  • Sam Nda-Isaiah