Ko akwai rashin jituwa tsakanin Iran da Oman kan Mashigar Hormuz?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Rahotannin kafofin yaɗa labarai na ƙasashen Larabawa sun yi nazari kan tasirin wata hanyar ruwa ta wucin gadi da Oman ta samar a ruwanta domin jiragen ruwa da ke bi ta Mashigar Hormuz.

Wasu kafofin sun ce wannan hanya ba wai ta zama madadin hanyar da aka saba bi ta Mashigar Hormuz ba ne, amma wasu sun yi hasashen cewa hakan na iya rage wata muhimmiyar damar da Iran ke amfani da ita wajen ƙarfafa tasiri a yankin.

A gefe guda kuma, kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewa akwai saɓani tsakanin Iran da Oman kan batun karɓar kuɗin fito daga jiragen ruwa da ke bi ta Mashigar Hormuz.

Batun Mashigar Hormuz na daga cikin manyan batutuwan da kafafen yaɗa labarai a ƙasashen Larabawa ke mayar da hankali a kai, inda wasu suka yi nazari kan tasirin sabuwar hanyar ruwa ta wucin gadi da Oman ta samar domin jiragen ruwa masu bi ta wannan mashigar.

A ranar 23 ga Yuni, Oman ta sanar da samar da hanyar ruwan ta wucin gadi tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Ruwa ta Duniya (IMO), domin sauƙaƙa zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar.

BBC ya gano yawancin manyan kafafen Larabawa sun fi mayar da hankali kan sanarwar haɗin gwiwa da Amurka da ƙasashen Gulf suka fitar bayan taronsu a Manama, wadda ta yi watsi da duk wani yunƙurin sanya kuɗin fito ga jiragen ruwa da ke bi ta Mashigar Hormuz.

Akwai kafafen yaɗa labaran sun fi mayar da hankali kan jaddada "manufarsu ta bai ɗaya na hana Iran mallaka ko kuma ƙera makamin nukiliya ta kowace hanya."

Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ci gaba da bibiyar saɓanin ra'ayi da ke tsakanin Oman da Iran kan batun karɓar kuɗin fito daga jiragen ruwa da ke ratsawa ta Mashigar Hormuz.

Shin Iran za ta iya rasa ƙimarta?

Tashar Al Jazeera mallakin ƙasar Qatar ta yi nazari kan ko Iran za ta rasa ƙimarta idan aka samu makwafin Mashigar Hormuz da kuma wata hanya ta matsa mata lamba a tattaunawarta da ƙasashen Yamma.

Rahoton ya kuma yi tsokaci kan saɓanin ra'ayi da ake gani tsakanin Iran da Oman kan yadda za a gudanar da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, inda ya ce Iran ba ta gamsu da sabuwar hanyar ruwa ta wucin gadi da Oman ta buɗe ba.

Masanin harkokin soji, Nidal Abu Zeid, ya shaida wa Al Jazeera cewa sabuwar hanyar na iya zama babbar hanyar da jiragen ruwa za su riƙa amfani da ita, kasancewar jiragen yaƙin ƙasashen Yamma da ke samun goyon bayan Amurka na samar da tsaro a yankin, kuma hanyar ba ta ƙarƙashin ikon dakarun IRGC na Iran.

Ya ce hakan na iya rage tasirin Iran a tattaunawarta da Amurka, domin za ta rasa ɗaya daga cikin manyan hanyoyin matsa lamba da take da su. Ya kuma ƙara da cewa hakan na iya sa Iran ta yi ƙoƙarin kawo cikas ga sabuwar hanyar da Oman ta samar.

Wannan ba mafita ba ce

Tashar Sky News Arabia ta ce sabuwar hanyar ruwa ta wucin gadi da Oman ta samar ba za ta maye gurbin hanyar da aka fi sani ta Mashigar Hormuz ba, inda jiragen ruwa tsakanin 120 zuwa 140 ne ke ratsa mashigar a kullum kafin yaƙin baya-bayan nan, yayin da sabuwar hanyar za ta iya ɗaukar jiragen ruwa kaɗan ne kawai.

Rahoton ya kuma ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta dakatar da wani shirin wucin gadi na gudanar da zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz, bayan da Amurka ta zargi Iran da kai hari kan wani jirgin dakon kaya a Tekun Oman.

Duk da haka wasu kafafen yaɗa labarai sun ci gaba da maida hankali wajen bayyana saɓanin da ke tsakanin Oman da Iran kan batun karɓar kuɗin fito daga jiragen ruwa da ke ratsa Mashigar Hormuz.

Tashar Al Arabi ta Qatar ta rawaito gargadin rundunar sojojin ruwa ta IRGC cewa duk jiragen ruwa da ke amfani da Mashigar Hormuz su bi hanyoyin da Iran ta amince da su kawai.

Shi ma shafin Middle East Online ya ce yadda ake tafiyar da Mashigar Hormuz ya haifar da saɓani tsakanin Iran da Oman.

A ina mashigar take?

Mashigar Hormuz na tsakanin Iran da Oman ne.

Taswirar tekun ta nuna ɓangarorin da suke da kyau a tsaya, da wuraren da ba a so a tsaya da kuma tudun mun tsira a tsakanin ɓangarorin biyu.

Idan tankokin mai za su wuce, sai su wuce ta kusa da tsibirin Greater da Lesser Tunb - inda ake takun-saƙa tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa kan mallakinsa.

Masana sun ce yaƙi na cikin abubuwan da suke jawo tsaiko a hada-hada ta mashigar kamar yadda ya faru a yakin Iran da Iran a shekarar 1980 zuwa 1988.

Muhimmancin mashigar

Hukumar ƙididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta ƙiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a a kullum ta tekun.

Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun.

Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man.

Farfesa Ahmad Adamu, masanin tattalin arzikin man fetur da iskar gas da ke jami'ar Philomath da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Ya ce hanyar ruwa ce da ba ta girma sosai, amma take da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.

"Ita wannan mashiga hanyar ruwa ce wadda tsayinta bai wuce kilomita 33 ba, wadda ta a daidai ƙasar Iran. Kuma hanya ce da jiragen dakon ɗanyen man fetur ke wucewa a kullum."

Ya ce daga jiragen dakon man da ke wucewa ta hanyar, akwai na ƙasashen Saudiyya da Kuwait da Iraqi da sauransu.

"Kullum ana wucewa da gangar ɗanyen mai kusan miliyan 20. Kusan kashi 20 cikin 100 na ɗanyen mai da ake buƙata a duniya," in ji shi.

Masanin ya ƙara da cewa ƙasashen da aka hana fitar da su ne suka fi sayar da man fetur mai sauƙi a kasuwannin duniya, wanda a cewarsa hakan ke taimakawa wajen rage farahinsa.

Akwai wata hanya daban bayan mashigar?

Saboda barazanar da ake yawan fuskanta ta datse mashigar a shekarun da suka gabata ne ya sa ƙasashen da suke dakon man fetur a yankin suka samar da wata hanyar daban.

Wani rahoton EIA ya ce Saudiyya ta fara amfani da bututun gabas maso yammaci mai nisan kilomita 1,200, wanda za a iya tura ganga miliyan 5 a kullum.

A shekarar 2019, Saudiyya ta gyara wasu bututun gas domin su yi ɗaukar ɗanyen man fetur.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta haɗa gaɓar tekunta na tudu da gaɓar Fujairah da ke gaɓar Oma da bututun da zai iya ɗaukar gangan mai miliyan 1.5.

A watan Yulin 2021, Iran ta ƙaddamar da bututun Greh-Jask, wanda zai iya jigilar mai zuwa gaɓar Oman. Yanzu haka bututun zai iya ɗaukar ganga 350,000 a kullum.

Rahoton EIA ta ƙiyasta cewa waɗannan hanyoyin za su iya jigilar ganga miliyan 3.5 a kullum - kusan kashi 15 na man da ake jigila ta tekun a kullum.