Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Atiku ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar ADC domin yin takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Wannan na nufin Atiku zai iya shiga cikin jerin ƴan takarar shugaban ƙasa da za su ƙalubalanci shugaban Najeriya mai ci Bola Tinubu.
A lokacin sanar da sakamakon zaɓen fitar da ɗan takarar da aka yi a daren ranar Laraba, Atiku ya samu jimillar ƙuri'a 1,846,370, inda ya kayar da sauran ƴan takara biyu - Rotimi Amaechi da kuma Muhammed Hayatu-Deen.
Rotimi Amaechi ne ya zo na biyu a zaɓen inda ya samu jimillar ƙuri'u 504,117, sai Muhammed Hayatudden a matsayi na uku da jimillar ƙuri'u 177,120.
A ranar Litinin 25 ga watan Mayu jam'iyyar ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin a jihohi na Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ƴan takara uku da suka fafata su ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi da kuma masanin tattalin arziki Mohammed Hayatu-Deen.
Shugabannin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin David Mark, sun zaɓi gudanar da zaɓen kai tsaye bayan ƙoƙarin cimma matsaya kan ɗan takara guda ɗaya tsakanin manyan masu neman takarar ya ci tura.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafin X bayan ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, Atiku ya ce "wajibi ne mu yi shiri sosai domin yaƙin neman zaɓen da zai ba mu nasara a babban zaɓe mai zuwa a ƙoƙarin da muke yi na ceto ƙasarmu da mutanenta da suka ɗaɗe suna shan wahala daga wannan gwamnati".
Kafin gudanar da zaɓen, jam'iyyar ta buƙaci 'yan takara da wakilai da sauran mambobinta su tabbatar da haɗin kai da bin doka domin tabbatar da zaman lafiya a yayin zaɓen.
Sai dai a ranar Talata, ɗaya daga cikin ƴan takaran uku, wato Rotimi Amaechi ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda aka gudanar da zaɓen.
A wani bayani da ya wallafa a shafin X, Amaechi ya ce: "Na yi fatali da sakamakon zaɓen da ake kitsawa bayan samun rahotannin hana mutane zaɓe a sassa daban-daban na ƙasar nan a lokacin zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC".
Tun farko gabanin fara zaɓen a wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, ya bayyana zaɓen fitar da ɗan takarar a matsayin wani muhimmin mataki na dimokuraɗiyya ba kawai ga jam'iyyar ADC ba, har ma ga 'yan Najeriya da ke neman sahihin shugabanci.
Ya ce manufar jam'iyyar ita ce fito da tsayayyar jam'iyya mai haɗin kai da za ta iya bai wa 'yan Najeriya shugabanci nagari kuma abin dogaro, ba tare da ɗaukar zaɓen a matsayin fafatawar masu nasara da masu faɗuwa ba.
Ƴan takarar da suka fafata:
Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli kamar talauci, rashin tsaro, bashi mai yawa da kuma raunin gwamnati, don haka tana buƙatar shugaba mai kwarewar mulki da fahimtar tattalin arziki.
A wata sanarwa da ya fitar gabanin zaɓen Atiku ya buƙaci wakilan jam'iyyar su zaɓi cancanta fiye da son rai ko tausayi yayin shirin zaɓen 2027.
Ya ƙara da cewa shi yana da gogewa da ilimin gudanarwa da zai taimaka wajen shugabanci, ba kamar wasu 'yan takara da ke dogaro da magana kawai ba.
A tarihin siyasa, Atiku ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007 a zamanin Olusegun Obasanjo, kuma ya sha tsayawa takarar shugaban ƙasa sau da dama ba tare da nasara ba a shekarun 1993, 2007, 2011, 2015, 2019 da 2023.
Ya kuma yi takara a jam'iyyu daban-daban a lokuta daban-daban kafin daga bisani ya koma jam'iyyar ADC a 2025, inda ya nuna sha'awar sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Rotimi Amaechi
Tsohon gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ɗaya ne daga cikin ƴan siyasa masu tasiri a siyasar Najeriya saboda gogewarsa a harkar siyasa.
Amaechi ya taɓa riƙe mukamai da dama, ciki har da kakakin majalisar dokokin Jihar Rivers, sannan kuma ya yi gwamna na jihar. Daga baya ya zama ministan sufuri, inda ya yi fice musamman wajen ayyukan layin dogo da wasu manyan ayyukan sufuri.
Shi ma yana daga cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar APC, kuma ya taka muhimmiyar rawa a gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
A shekarar 2022, Amaechi ya tsaya takarar shugaban ƙasa a APC, amma ya sha kaye a hannun Bola Tinubu.
Bayan tantance 'yan takara, Amaechi ya ce wakilan jam'iyyar su zabi mutumin da zai iya kayar da shugaban da ke kan mulki, mai gogewa da kuma iya yin aiki mai kyau.
Ya ce: "Ku yi mana hukunci da abin da muka yi. Idan mun yi aiki mai kyau, ku zabi wanda ya fi kowa."
Mohammed Hayatu-Deen
Hayatu-Deen ƙwararren masanin tattalin arziki ne, kuma ya taɓa zama babban ma'aikacin banki kuma mai zuba jari, kuma gogagge ne a harkokin kamfanoni. Ya fito daga Jihar Borno, kuma ya shafe fiye da shekara 40 yana aiki a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu.
A 2015, ya jagoranci kwamitin miƙa mulki kan tattalin arziki ga sabuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
A 2023, Mohammed Hayatu-Deen ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, amma ya janye 'yan kwanaki kafin zaɓen fitar da gwani.