Mourinho ya sake karɓar aikin kociyan Real Madrid kan yarjejeniyar kaka uku, Real Madrid
Jose Mourinho ya sanya hannu kan kwantiragin shekara uku, domin sake zama sabon kocin Real Madrid.
Sai dai ba za a gabatar da shi a hukumance ba sai bayan zaben shugaban ƙungiyar da za a gudanar ranar 7 ga watan Yuni.
Duk da haka, kwantiragin Mourinho zai fara aiki ne kawai idan shugaba, Florentino Perez ya ci gaba da rike mukaminsa.
Perez ya sanar da za a gudanar da sabon zaben ne a wani taron manema labarai na musamman da aka yi a farkon wannan watan, inda ya soki ƴan jarida da kuma La Liga, yana mai cewa akwai “tsarin yaki” da ake yi a kansa.
Perez mai shekaru 79 yana shugabantar Real Madrid tun 2009, bayan nan kuma ya taba rike mukamin tsakanin 2000 zuwa 2006. Sai dai ƙungiyar ta kammala kakar wasa biyu a jere ba tare da lashe kofi ba.
Attajiri, Enrique Riquelme ne ke kalubalantar Perez a zaben shugaban Real Madrid na farko cikin shekaru 20 da aka samu hamayya, ko da yake ana sa ran Perez zai sake yin nasara.
Mourinho ya bar aikinsa na kocin Benfica, inda ya karbi ragamar ƙungiyar a watan Satumba kuma ya kai ta matsayi na uku a Primeira Liga ta Portugal a wannan kakar.
A wa’adinsa na farko a Real Madrid tsakanin 2010 zuwa 2013, Mourinho ya lashe La Liga, Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup.
Zai maye gurbin Alvaro Arbeloa, wanda aka naɗa a watan Janairu bayan tafiyar Xabi Alonso.
Real Madrid ta kammala kakar 2025-26 ba tare da lashe kofi ba, yayin da abokiyar hamayyarta FC Barcelona ta ɗauki La Liga bayan nasarar 2-0 a El Clasico.
Haka kuma tafiyar Real Madrid a Champions League ta kare bayan da Bayern Munich ta doke ta da jimillar 6-4 a zagayen quarter-final.
Bayan da ya bar Real Madrid a 2013, Mourinho ya koma Chelsea karo na biyu, inda ya lashe kofin Premier League na uku a rayuwarsa da kuma EFL Cup a kakar 2014-15.
Daga baya ya koma Manchester United a 2016, inda ya lashe Europa League, EFL Cup da Community Shield a kakarsa ta farko kafin a kore shi a 2018, saboda rashin sakamako mai kyau.
Mourinho ya kuma horar da Tottenham da Roma — inda ya lashe Europa Conference League a 2022 — da kuma Fenerbahce kafin ya koma Benfica ta Portugal.